Budurwa ta yi tiyatar sauya kamannu sau 30 don burge saurayi

Wata budurwa mai shekara 22, mai suna Berry Ng, a 22 a kasar Hong Kong ta yi tiyatar kwaskwarimar sauy kamannu sau 30 a shekara biyar don ta burge saurayinta. Matar dai ta shahara a akfar sadarwa ta youtube, har ta kai ga bayan sun rabu da saurayin ta yi nadmar abin da ta aikata. […]

Budurwa ta yi tiyatar sauya kamannu sau 30 don burge saurayi

Wata budurwa mai shekara 22, mai suna Berry Ng, a 22 a kasar Hong Kong ta yi tiyatar kwaskwarimar sauy kamannu sau 30 a shekara biyar don ta burge saurayinta. Matar dai ta shahara a akfar sadarwa ta youtube, har ta kai ga bayan sun rabu da saurayin ta yi nadmar abin da ta aikata.

Ta ce ta fara zuwa ana yi mata tiyatar sauya kamannu ne lokacin da tsohon saurayinta ya soki lamarin fuskarta, har ta kai ga yana kwatanta da wata mashahuriyar ’yar kwalisa mai tallata haja, kamr yadda kafar sadarwa ta Nedt Shark ta ruwaito.

Budurwa Ng ta ce ta kashe Dala dubu uku don a daidaita mata goshinta da idanu da kumatu da hanci da mamunanta. Duk da irin kokarin da ta yi tsohon saurayin ya ce ba ta burge shi ba.

Da a ce ya hana ni, kuma ya nuna mini ni kyakkyawa ce da na daina, amma bai yi hakan ba,” inji ta.

Ta ce duk da yawan tiyatar da aka yi mata, har zuwa lokacin da suka rabu kirjinta ba ya burge shi, don haka ta sa aka dan gyara mata shi ya yiwo gaba.

Lokacin da mahaifiyar Ng ta ganta bayan da aka yi mata tiyatar jirkita kamannu ta karshe, sai ta fashe da kuka. Domin a lokacin ne Ng ta farga cewa ta yi mugun damfaruwa da son a sauya mata kamannu.

Tuni dai ta yi watsi da tsohon saurayin nata, ta kuma sanar da kafafen yada labarai irin nadamar da ta yi kan yawan tiyatar sauya kamannu da ta biya aka yi mata har sau 30 cikin shekara biyar.