Budurwar Robot za ta shiga manyan jami’o’in Sin a badi

Budurwar Robot za ta shiga dayaga daga cikin manyan jami’o’in kasar Sin a shekarar 2017, wannan kuwa ya auku ne saboda Mutum-mutumin budurwar Robot din ta nuna kwazon karatu fiye da ’yan kwaleji matakin aji na 12. Don haka ake sa ran za ta kasance a jami’o’in Peking ko Tsinghua nan da shekarar 2020.Budurwar Robot […]

Budurwar Robot za ta shiga manyan jami’o’in Sin a badi
Budurwar Robot za ta shiga manyan jami’o’in Sin a badi

 Budurwar robotBudurwar Robot za ta shiga dayaga daga cikin manyan jami’o’in kasar Sin a shekarar 2017, wannan kuwa ya auku ne saboda Mutum-mutumin budurwar Robot din ta nuna kwazon karatu fiye da ’yan kwaleji matakin aji na 12. Don haka ake sa ran za ta kasance a jami’o’in Peking ko Tsinghua nan da shekarar 2020.
Budurwar Robot za ta zauna jarrabawar fannonin karatu da suka hada da lissafi da harshen China (Mandarin) da sauran fannonin zayyana da fasaha, da suka hada da tarihi da siyasa da tasawirar kasa, a cewar Lin Hui, shugaban kamfanin kera mutum-mutumi mai kwakwalwa da ke birnin Chengdu. Wannan kamfani ya samu nasarar samar da mutum-mutumin robot mai kaifin basira da zai iya warware matsalolin lissafi, kamar yadda Ma’aikatar Kimiyya da kere-kere ta tsara  cikin shekarar 2015.
Tamkar yadda kowane mai rubuta jarrabawa, robot din za ta kammala jarrabawarta a kan lokacin da aka kayyade. Sai dai sabanin yadda aka san cewa mutane da dama ke zama a dakin jarrabawa, robot din za ta zauna ta jarrrabawar ita kadai, amma ban da al’amuran da suka shafi fannin koyon gabatar da kara ko dokoki a gaban kotun shari’a.
A cewar Lin, za a hada robot din da na’urar dab’i ta ‘printer’ kafin kowace jarrabawa, inda aka tsdara yadda za ta rika fito da sakamako ko amsoshin tambayoyin jarrabawarta. Sannan ba za a hadata da intanet ba, sannan za a tabbatar da cewa, ta warware daukacin matsalolin da aka gabatar mata, inda za a ga amsoshin tambayoyinta a takardar da aka fito da ita daga cikin na’urar dab’i.
Lin ya ce an samu ci gaba wajen sarrafa rubutun robot, inda ake amfani da fasaha da basirar da aka cusa wa mutum-mutin, har ya rika fahimta sarrafa harshe. Domin a cewar Fu Hongguang, wani jami’in bincike da bunkasa massarafar basirar robot akwai bukatar a yi mutum-mutumin gwajin auna fahimtar lissafi.
A daidai lokacin da Robot ke kokarin shiga jami’o’in Peking da Tsinghua a kasar Sin nan da shekara ta 2020, can kuwa a kasr Japan irin wannan mutum-mutumi na hankoron shiga jami’ar Tokyo.

Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD

NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024

Kano: Abba ya rusa ciyamomin riko

An haramta wa ma’aikatan Asibitin Tarayya yin ‘kirifto’ a wurin aiki