Bugagge ya mutu bayan ya sha maganin kwari da kuskure
Wani abin mamaki da takaici ya faru a wani dakin cin abinci a Titin Adeniran Ogunsanya da ke Surulere a Jihar Legas, inda wani da ya yi dim da giya ya mutu bayan ya sha maganin kwari cikin kuskure. Mamacin wanda ya je dakin abincin tare da abokansa bayan sun dawo daga daurin auren abokinsu […]
Wani abin mamaki da takaici ya faru a wani dakin cin abinci a Titin Adeniran Ogunsanya da ke Surulere a Jihar Legas, inda wani da ya yi dim da giya ya mutu bayan ya sha maganin kwari cikin kuskure.
Mamacin wanda ya je dakin abincin tare da abokansa bayan sun dawo daga daurin auren abokinsu a inda ya sha ya bugu, ya sha maganin kwarin ne da wani ma’aikacin dakin abinci ya ajiye a cikin kwalba.
Mamacin ya sha maganin kwarin ne a matsayin ruwa, kuma ya mutu ne bayan an kai shi asibiti bayan ya shaida wa abokasa cewa ya sha wani ba dai gane ba.
Tuni dai ’yan sanda suka kama manajan dakin abincin bayan sun samu labarin mutuwar mashayin.