Buhari @81: Abubuwa 10 da ba za a manta ba

A yau tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya cika shekara 81. Ga Abubuwa 10 a rayuwarsa da ba za a manta da su ba.

Buhari @81: Abubuwa 10 da ba za a manta ba

A yau 17 ga Disamba, 2023 ne tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya cika shekara 81, kimanin wata shida da saukarsa daga mulki a matsayin shugaban kasa na 15 a Najeriya, bayan ya shekara 8 a kan karaga.

Tsohon kakain shugaban kasa Garba Shehu, ya ce Buhari ya hana gudanar da shagalin bikin a yayin da yake ci gaba da rayuwarsa a mahaifarsa Daura, Jihar Katsina.

Shugaba Tinubu ya bayyana Buhari a matsayin mai gaskiya da adalci da kuma kishin kasa wanda samun nagartaccen shugaba kamarsa sai an yi tsananin sa’a.

A cewarsa, ayyukan Buhari ba su da kama a bangaren gina filayen jirage sama, jiragen kasa, jiragen ruwa, madatsan ruwa, tashoshin lantarki, gabodi da hanyoyi da kuma bangaren mai da sauransu.

Ga muhimman abu 10 game da Buhari:

1- An haife shi ranar 17 ga Disamba, 1942 a Daura, a gidan wani bafulani mai suna Mallam Hardo Adamu, daga Dumurkol da ke Karamar Hukumar Mai’Adua, mahaifiarsa kuma sunanta Zulaihat, wadda ta hada jinin Hausawa da Kanuri.

2- Bayan kammala sakanadare ya shiga aikin soja har ya yi ritaya a matsayin Janar. ya halarci yakin basasan Najeriya gaba dayan, amma bai samu rauni ba. Da shi aka gudanar da wasu juyin mulki mulki da kuma murkushe wasu masu juyin mulkin  a lokacin soja. Duk manyan runudononin sujin Najeriv hudu ya jagorance su, banda guda daya, sannan ya kasance sakaaren soji a masayin babban mai adana bayanan sojoji.

3- A 2015 ya fara lashe zaben shugaban kasa bayan an kayar da shi sau uku a jere, inda jam’iyyarsa, APC da shi suka kafa tarihin kayar da jam’iyya mai mulki. APC ta samu rinjaye a majalisar dokokin kasa da gwamnonin jihohi.

4- 14 ga Oktoba, 2019, Buhari ya rufe iyakokin Najeriya da kasashen Nijar, Chadid, Benin, da Kamaru da nufin murkushe masu fasa-kwari da bunkasa harkoin noman cikin gida, inda ya kaddamar da shirin noman wasu abubuwa 16 da tallafin manoma daga Bankin CBN. Sai dai ana zargin matakin da haifar da tsadar kaya da kuma durkusar da harkokin kasunwanci a yankunan da ke iyaka da kasashen.

5 – A Oktoba 2022, CBN ya sauya fasalin takardun kudi da nufin rage yawon tsabar kudi da ayyukan almundahana, lamarin da ya jefa al’ummar Najeriya cikin kuncin rayuwa kafin Kotun Koli ta yi watsi da batun.

6- Buhari ya sanya hannu kan Dokar Man Fetur (PIA) wadda aka shekara 20 ana kai-komo wajen ganin tabbatuwarta da nufin bunkasa bangaren mai da samuwarsa a Najeriya. Ya kuma yi nasara a kotun Birtaniya, wadda ta soke tarar Dala biliyan 11 kan kwangilar man fetur na P&ID .

7 – Ya sauya ranar Dimokuradiyya ga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga Yuni domin karrama zaben ranar a 1993, wanda aka ayyana a matsayin mafi sahihanci, amma gwamnatin soji ta soke shi. Domin lallashi, Buhari ya ba da hakuri ga al’ummar kasa game da soke zaben MKO Abiola, ya karrama shi da lamba mafi girma a kasa (GCFR), wadda ake ba wa shugabannin kasa.

8- Ya cire tallafin mai da gwamnati ta yi zargin na cinye tiriliyoyin Naira da NNPP ba zai iya dorewa da biya ba. Sai dai hakan da Gwamnatin Tinubu ta sanar ya bar baya a kura, inda ake zargin sa da haddasa tsadar rayuwar da ke ci gaba da karuwa da ma karancin man a kasar.

9- A zaminsa ne sojoji suka kashe Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau da na ISWAP, Albanawi, suka kwato kaso mai yawa na daliban Chibok da Dapchi da kungiyoyin suka yi garkwua da su. Matsalar ta’addancin kungiyoyin a Arewa maso Gabas ta ragu sosai har masu gudun hijira sun koma gidajensu; Amma an samu karuwarta a Arewa maso Yamma da Arewa ta tsakiya, inda ’yan bindiga ke kashe mutame su yi garkuwa da su domin karbar kudin fansa. An sha yin garkuwa da dalibai a makarantun Islamiya, firamare, sakandare da na gaba da su; an kashe wasu, wasu an sako su bayan karbar kudin fansa, da sauransu.

Tags