Buhari a matsayin tatsuniya? (3)
Tambayi kanka don Allah, nawa litar man fetur take yau? Za a ce ta kai Naira 145, alhali a zamanin gwamnatin Jonathan tana Naira 87. Wadansu za su ce da ko an kara farashin albarkatun man fetur ne don a samar da shi a cikin kasa a kuma daina biyan tallafi da rara ga ’yan […]
Tambayi kanka don Allah, nawa litar man fetur take yau? Za a ce ta kai Naira 145, alhali a zamanin gwamnatin Jonathan tana Naira 87. Wadansu za su ce da ko an kara farashin albarkatun man fetur ne don a samar da shi a cikin kasa a kuma daina biyan tallafi da rara ga ’yan kasuwar da ke ci da gumin mutane. Amma hakan gaskiya ne? Ba gaskiya ba ne, domin har jiya har yau gwamnatin Buhari na biyan tallafi ga masu ci da gumin talaka, to ina amfanin badi ba rai!
Wannan tsarin da manufofin tattalin arziki shi ya sa farashin kayayyakin masarufi ke kara yin tashin gwauron zabo, domin kuwa duk abin ya ci Doma, ba zai bar Awai ba. Abubuwan more rayuwa irin su itacen girki ko gawayi da man fetur da kananzir da gas da abincin ci da na sayarwa da kudin makarantar yara da na shiga motocin haya da na dauko amfanin gona ko tufafin sawa da takalma da huluna da zannunwa da wutar lantarki da fiya-wata da kayan miya da man gyada da manja da magi da daddawa, kai da ita kanta rayuwar baki daya ba abin da bai daga ba, amma kuma ba abin da ake ji a cikin kasa sai ‘canji’ ya samu! Idan kuma wadansu suka rika fadar ai ba wani canji da ya samu, in kuma an ga inda ya samu a kai mu mu gani, sai a ce da kai, ai an kusa kai gaci, a sake zaben gwamnatin APC, za a ga ci gaban da ba a taba gani ba, somin tabi ne aka gani a shekaru kusan 4 da suka wuce. Abubuwan more rayuwa na zuwa nan gaba. Nakan dade ina mamakin irin wannan alkawari da ake yi wa talaka, to amma da na tuna da duniyar mafarki ko kuma tatsuniya, sai in ce ai ban ga laifin shugabannin namu ba!
Abu na uku da aka rika yi wa al’umma wala-wala da shi domin samun wurin zaman da kuma ci gaba da mulki shi ne yaki da cin hanci da rashawa da almundahana. Shi ma in ka natsu da kyau sai ka ga nan ne ma tatsuniyar Hausawa ta fi bayyana a fili. Tunda aka kawar da gwamnatin Shugaba Jonathan ba abin da aka fi yawan buga misali da shi irin sata da babakere da almundahanar da aka tafka a zamanin mulkin PDP, musamman abin da ya shafi kudin makamai, wanda ya jawo har zuwa yau ake tsare da Kanar Sambo Dasuki. Shi ma wannan kamar sauran matakan da aka bi domin yakin neman zabe da kuri’u, ba komi ba ne sai almara da tatsuniya. Da shi ne kuma aka bi ake ta mamunga da talakawa, ana ta yi musu wuji-wuji, ina gabas, suna nuna sama.
A yau ba abin da talakan Najeriya, musamman na Arewacin Najeriya ke son ji irin an kame wancan ‘kasurgumin barawon’ ko wancan ‘hamshakin dan kasuwar’ ko wani ‘gawurtaccen mai tarin dukiya’ ko ’ya’yan shafaffu da mai ko wani dan siyasar da bai da uwa a gindin murhu, amma ya taka, ya tsare daga ajiyar Karuna ko a cikin kauyensu ko garinsu ko birninsu ko jiharsu ko kuma a kasa baki daya. Ba abin da ke yi wa ‘talakan’ Arewa dadi da sa su cikin sowa irin su ga an kame ‘mugaye’ da ‘barayin gwamnati’ da suka hana su jin dadin rayuwa, a kai su gidan maza a kulle. Yin haka ko ba a tabbatar da laifin ba, ya ishe su. Shi ya sa a kullum ake ta yayatawa, Buhari ba barawo ba ne, amma shi ne ‘azara’ilun barayi’, tamkar dai yadda talakawa ke yi a cikin tatsuniya ga masu kudi da sarakai da mugayen cikinsu. Yaya abin yake a zahiri?
A duk lokacin da masu tatsuniya ke kitsa adabinsu, suna yi ne da biyu, su nishadantar da su kuma rama azabar da suke sha a hannun masu gari ko masu tarin dukiya. Shi ya sa za a ga a cikin tatsuniya Sarki ko wani mai mulki na cikin tasku daga bakin talaka, wannan kuma na faruwa ne domin bai da hanyar da zai iya zagi ko cin mutunci ko wahalar ko kuntata wa sarakin sai ta tatsuniyar, za a ga ya zayyana saraki cikin damuwa ko da kuwa Sarkin na gaskiya zai ci gaba da tursasa masa, bai damu ba, ai ya dai more ta fuskar tatsuniya! Ka ga ke nan tunda talakawa ba su iya zagin Sarkinsu ko Hakimi ko Dagaci ko Mai unguwa, ko wani mugun attajiri za su fake da tatsuniya ce su ci karensu ba babbaka.
Abin da ke faruwa yanzu a Najeriya ke nan. Duk wani dan siyasar da ya tara, ko ya tada kai da kayan adon gidan Karuna, musamman dan adawa, barawo ne. Kama shi ko tona masa asiri ko daure shi, ko ba a yi musu shari’a ba, daidai ne, domin ba wani mai gaskiya in ba Buharin ba! A nan Buhari ya zama tatsuniyar a zahiri, tunda ba mu iya rama ‘muguntar’ shugabanni ko hamshakanmu da suke tare da mu a tsawon lokaci, bari mu yi ta sowa in Buhari ya taba su, ko ba komai ai mun ji sa’ida!
Amma wannan shi ne daidai? Shin ba wadansu barayi sai a cikin Jam’iyyar PDP? Ba almundahana sai a zamanin mulkin PDP na shekara 16 da ta yi tana mulki? Ba mugaye sai a Jam’iyyar PDP? Saboda haka a zabi Jam’iyyar APC, saboda nan ne ‘waliyyai’ suke ciki? Shin hakan gaskiya ne? Ba gaskiya ba ne!
Za mu ci gaba.