Buhari a matsayin tatsuniya? (4)
Abin da ke faruwa yanzu a Najeriya ke nan. Duk wani dan siyasa da ya tara, ko ya ta da kai da kayan adon gidan Karuna, musamman dan adawa, barawo ne. Kama shi ko tona masa asiri ko daure shi, ko ba a yi musu shari’a ba, daidai ne, domin ba wani mai gaskiya in […]
Abin da ke faruwa yanzu a Najeriya ke nan. Duk wani dan siyasa da ya tara, ko ya ta da kai da kayan adon gidan Karuna, musamman dan adawa, barawo ne. Kama shi ko tona masa asiri ko daure shi, ko ba a yi musu shari’a ba, daidai ne, domin ba wani mai gaskiya in ba Buharin ba! A nan Buhari ya zama tatsuniyar a zahiri, tunda ba mu iya rama ‘muguntar’ shugabanni ko hamshakanmu da suke tare da mu a tsawon lokaci, bari mu yi ta sowa in Buhari ya taba su, ko ba komai ai mun ji sa’ida!
Amma wannan shi ne daidai? Shin ba wadansu barayi sai a cikin Jam’iyyar PDP? Ba almundahana sai a zamanin mulkin PDP na kusan shekara 16 da suka wuce? Ba mugaye sai a Jam’iyyar PDP? Saboda haka yanzu za a zabi Jam’iyyar APC, saboda nan ne ‘waliyyai’ suke ciki? Shin hakan gaskiya ne? Ba gaskiya ba ce!
Idan jam’iyya ce mafita a Najeriya a halin yanzu, to ba kuwa Jam’iyyar APC ta Buhari ba, sai dai wata. Mu natsu mu gane bakin zaren. Bai dace ba a ciji ‘mumini’ har sau biyu ba, yana ji, yana gani. Idan har Jam’iyyar APC ita ce mafita a yau domin tana kunshe da mutanen ‘kwarai,’ karkashin Shugaba Buhari, to da alama dodoridon ya ci mu, ba mu za mu taba bambancen barcin makaho ba.
Me ya sa na ce haka? Ga misali. A lokacin da Jam’iyyar PDP ta kafu, ta kuma zama jam’iyyar mulki tun daga 1998 zuwa 1999, an yi shugabannin da suka rike jam’iyyar a Najeriya su 13, daga cikinsu, guda biyu 2, wato Aled Ekwueme da Solomon Lar, sun mutu, yanzu sauran 11. Daga cikin 10 da suka rage, wato ban da mai ci yanzu, 7 duk suna cikin Jam’iyyar APC yanzu, da su ake damawa. Da su ne Jam’iyyar APC ke godo a wasu sassan kasar nan. Idan kuwa kashi 70 cikin 100 na shugabannin kasa na Jam’iyyar PDP da magoya bayansu yanzu suna cikin Jam’iyyar APC, me ya kamata mu fahimta ke nan? Har yanzu Jam’iyyar PDP ce ke mulkin ba Jam’iyyar APC ba! Wadansu daga cikin wadannan shugabanni na PDP ma yanzu ministoci ne ko ’yan Majalisar Tarayya; wadansu daga cikinsu na cikin dakarun Shugaba Buhari da tsarin gwamnatinsa; in haka ne, wanda hakan ne, ina ruwan jam’iyya a wannan kwamacala? Wane laifi Jam’iyyar PDP ta yi cikin tsawon shekara 20 na wannan dimokuradiyya da muke ciki, tunda komai ya zama wake da shinkafa?
Saboda haka muna iya cewa har yanzu muna nan tare da ‘macuta’ da ‘mahandama’ da mutanen da suka durkusar da Najeriya a tsawon mulkin PDP na shekara 16 da kuma a cikin mulkin APC na shekara 4! Wato dai wayon a ci ne an kori kare daga gindin kanya! Kuri’armu ake nema da zarar aka shanye zakin amarya, nan za mu gane ba mu da wayo!
Idan har cikin tsawon shekara 20 da sake dawo da tsarin mulkin dimokuradiyya ba mu hankalta ba, ba mu gane cewa dokin sukuwa aka mayar da talaka ba, ba mu fahimci duk kanwar ja ce ba, to mun shiga uku, mun lalace. Mu sani ba mai fitar da mu daga kangin bauta, sai da kanmu. Dadin baki ba zai fitar da mu ba. Ya dace yanzu mu wage idanunmu da kyau mu gane dawan garin, mu kuma san cewa, ‘yan siyasa, ’yan tsiya ne, kansu kadai suka sani. Ba ruwansu da halin da muke ciki ko kuma yadda kasar za ta kasance, in dai burinsu zai biya. Za su iya shirga kowace irin karya, za su iya yin kowane irin alkawari, za su iya yin duk wani rufa-ido in dai za su kai ga gaci na hayewa bisa karagar mulki, domin yin sukuwa. Shi ya sa yanzu ba abin da ke yin tashe irin yadda ake yin kaura daga jam’iyyar ‘shaidanu’ zuwa jam’iyyar ‘waliyai’, alhali ba abin da ya canja. A lura da kyau, a lokacin da Shugaba Buhari ke maraba da ’yan Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC, za a ga cewa masu damukakken kashi a duwawu ne ake ta murnar an yi babban kamu. Ina gaskiya a cikin irin wannan badakala?
Abin da ya dace mutane su fahimta shi ne, a lokacin da irin wadancan ‘batattun’ ’yan PDP suke yin hijira zuwa APC, suna yin haka ne don neman na abinci da samun mafaka. Ba ruwansu da talaka ko gyaran kasa, mu ne suka raina wa hankali, su bar mu da gaba da juna da cin mutunci da kashe-kashen kawunanmu, wato mu rike kan saniyar, suna tatsarta! Za a iya ganin haka daga gungun ’yan Buharin, har masu neman su gaje shi! Ba kuma za su taba canjawa ba sai mun sa musu gorar saita hankali!
Saboda haka idan sun zo neman kuri’ummu wannan karo, kada mu yarda da dadin baki! Ba wata jam’iyya ta ceton talakawa a tsakanin manyan jam’iyyun nan guda biyu, wato PDP da APC, duk kanwar ja ce, domin kuwa buzayen da ke tallar kanwar duk daga sharar hamada suka tusgo. Kada mu yarda mu ba da kai bori ya hau, komai ya kasance a faifai, mu gani a kasa tukuna ko kuma su fada mana ayyukan da za su yi mana, karara da yadda za su yi ayyukan da inda za su samo kudaden yin ayyukan da lokacin da za a gama ayyukan, ba alkawari ba. Mu fada musu, mun gaji da gafara sa, ba mu ga kaho ba!
Mun kammala.