Buhari a Sakwwato ga mai hankali

Mujaddadi Shehu Usmanu Dan Fodiyo ya umarci dukan Sakkwatawa da al’ummar Musulmin Daular Usmaniyya cewa su hankalta da  dabi’u da cikar mutumin kirki wanda yake rayuwa ba tare da fariya ko izgilanci ko domin yabon jama’a kawai ba. Shehu ya yi kira ga mutanen kirki su zamanto masu rikon amana da rashin butulci da kamun […]

Buhari a Sakwwato ga mai hankali
Buhari a Sakwwato ga mai hankali

Mujaddadi Shehu Usmanu Dan Fodiyo ya umarci dukan Sakkwatawa da al’ummar Musulmin Daular Usmaniyya cewa su hankalta da  dabi’u da cikar mutumin kirki wanda yake rayuwa ba tare da fariya ko izgilanci ko domin yabon jama’a kawai ba.

Shehu ya yi kira ga mutanen kirki su zamanto masu rikon amana da rashin butulci da kamun kai.

Tun bayan Shehu Usmanu, al’ummar Sakkwato da dukan ’yan Najeriya masu kyakkyawar manufa, mun yi imani cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya zamanto fitaccen bawan Allah da yake kan gaba wajen jaddada karantarwar Shehu Dan Fodiyo a aikace ba domin jama’a su yaba ba.

Aiki da koyarwar Shehu da Shugaba Muhammadu Buhari ya runguma sun kasance daga cikin ginshikan adawar makiya ci gaban al’ummar Najeriya.

Duk wani mai kaunar ci gaban wannan babbar kasa zai so ya ga cewa an samu shugabanni masu rikon amana da adalci, wanda a kan haka Daular Usmaniyya ta kafu.

Hakika Jihar Sakkwato tana da muhimmaci a siysasar Najeriya; haka kuma muhimmancin siyasar Birnin Shehu a kan ci gaban Arewacin kasar nan ba zai misaltu ba.

To sai dai kash, akwai wadansu mutane wadanda saboda son zuciya da kuma karancin burin ci gaban jama’arsu, ba sa ganin alfanun mulkin Shugaba Buhari na tabbatar da rikon amana da dogaro da kai.

Abin takaicin ma shi ne adawarsu da Shugaba Buhari kara zafafa take yi a kullum, maimakon ta yi sauki; kuma wannan kiyayya ta samo asali ne tun lokacin da yake kokarin neman shugabancin kasar nan.

Amma abin alfahari shi ne talakawan Jihar Sakkwato, kamar sauran talakawan jihohin Arewa da Kudu, suna tare da Shugaban Kasa a kan turbarsa ta yaki da cin hanci da rashawa da farfado da tattalin arziki da samar da zaman lafiya da kuma fadada harkokin tattalin arziki da samar da abubuwan inganta rayuwa kamar ilimi da tituna da asibitoci da hanyoyin jirgin kasa domin inganta sufuri da sauransu. Amma ina! Akwai mutanen da wadannan abubuwa ba su dame su ba, saboda zunzurutun adawar siyasa da rashin kishin kasa.

Ko a shekarar 2003, a garin Sakkwato ne makiya gaskiya suka gwada fasaharsu ta gurbata duk wata manufa ko yanayi ko kalamai da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a lokacin, (kamar yadda har yanzu suke yi). Sun yi amfani da kalaman da Shugaba Buhari ya yi na kira a kan mu daidaita sahu a kan karantarwar Shehu Usmanu Dan Fodiyo suka ce wai ya ce kada a zabi wanda ba Musulmi ba.

Ko Sakwkwatawa suna lura da cewa duk Jihar Sakkwato idan aka ga ana aikin ci gaban kasa “na zahiri,” aikin da Shugaba Muhammadu Buhari ya umarta a yi wa jama’ar jihar ne?

Ko kun san rundunar ma’abota bijirewa da butulce wa koyarwar Shehu Usmanu suna bakin cikin bayyana wa duniya kyawawan ayyukan alheri da shugaba Buhari yake gudanarwa a Jihar Sakkwato kamar ba jihar Naira biliyan 18.3 na kulob din Paris da Shugaba Buhari ya ba Gwamna Aminu Tambuwal domin ya biya hakkin ma’aikatan jihar? Tuni ’yan adawa sun manta da tallafin Naira biliyan 8 da miliyan 700 da gwamnatin Buhari ta ba da don bunkasa aikin gona a Jihar Sakkwato.

Haka kuma sun yi biris sun manta da aikin sake shimfida titin Runjin Sambo zuwa mazaunin dindindin na Jami’ar Usmanu Danfodiyo; ga kuma gina hanyar Sakkwato zuwa Tambuwal zuwa Jega. Bayan haka sun nuna kamar ba su ga kokarin da Shugaba Buhari ya yi na gina sabuwar Rundunar Soji ta 8 a Kalambaina domin bunkasa tsaro da harkokin zamantakewa a Jihar Sakkwato da makwabtanta ba.

Don haka mu jama’ar Jihar Sakkwato mu tsaya tsayin-daka a kan gaskiya, domin ita siyasa ba hauka ba ce, kuma ba gaba bace. Idan mafadin magana wawa ne, majiyinta bai kamata ya zama wawa ba.

Amma saboda an jima ana cin kasuwa da wasa da hankalin Sakwkwatawa sai a ce duk da wadannan abubuwan alherin, wai Shugaba Buhari ba ya son jama’ar Sakkwato? Tabbas ya dace jama’ar Sakkwato su yi hangen nesa, su lura, sa’annan su yabi gwani a lokacin da ya dace.

Tasi’u Mohammed, imel:[email protected]