Buhari: Alkawari kaya ne (2)

Ga wadanda ke biye da mu zuwa yau, mun tsaya ne inda nake cewa ya dace mu yi amanna da cewa zaben BUHARI Shugaban kasa, zaben nagari ne, ina kuma da yakinin bisa ga dukkan alamu, zaben BUHARI turba ce ta ci gaba da sake fasalta tsarin shugabancin kasar nan da yardar Allah.  Me ya […]

Buhari: Alkawari kaya ne (2)
Buhari: Alkawari kaya ne (2)

Ga wadanda ke biye da mu zuwa yau, mun tsaya ne inda nake cewa ya dace mu yi amanna da cewa zaben BUHARI Shugaban kasa, zaben nagari ne, ina kuma da yakinin bisa ga dukkan alamu, zaben BUHARI turba ce ta ci gaba da sake fasalta tsarin shugabancin kasar nan da yardar Allah. 

Me ya sa na fadi haka? Bari mu soma da bin diddigin alkawurra da abubuwan da BUHARI zai yi da zarar ya haye karaga da kuma yadda zai bi matakin aiwatar da su.
Me BUHARI zai iya yi game da almundahana da lalacewar shugabanci a Najeriya? Wannan ita ce tambayar da ke dauke da ruhin gudanar da mulki cikin adalci da ci gaba. Almundahana da lalacewar shugabanci su ne sankarar da ke cinye rayuwar al’umma tunda dadewa a kasar nan, musamman kuma a cikin shekara 15 da suka wuce na rayuwar wannan kasa. Ke nan alkawarin da Buhari ya yi na zai bayyana kadarorinsa da duk wata dukiya da ya mallaka a bainar jama’a cikin wata UKU na hawansa mulki ya fara tabbatar mana cewa gaskiya aka shirya yi.
Kiran da zan yi shi ne, mu dauki biro da takarda, mu rubuta duk abin da zai bayyana, (wanda yawanci mun san abin da ya mallaka,) mu ajiye, idan mun ga dukiyarsa ta karu ta wata barauniyar hanya bayan ya hau mulki, to mu tabbata ba BUHARIN da muka zaba ba ne. BUHARIN da za mu zaba ba zai taba zama bera ba, domin tun can asali bai da halin beran, balle a ce.
Saboda haka ba sai mun nanata ba, idan har BUHARI ba zai saci dukiyar al’umma ba, to ba kuma zai bari wasu su sata ba daga cikin mukarrabansa, ko kuma wadanda ya zabo domin su taya shi shugabancin kasar nan. Ta haka ne kuma za a tabbatar da ana amfani da dukiyar al’umma bisa amana da kuma ci gaban al’umma.
Wani zai iya cewa lallai ilai mun yarda da gaskiyar BUHARI, amma ta yaya za mu amince da gaskiyar mukarrabansa? Wannan tambaya ce mai ma’ana, amma ita ma BUHARI ya yi nazarinta, shi ya sa ya yi alkawarin cewa ba zai yi aiki da duk wanda ya ki bayyana wa al’umma irin dukiyar da ya mallaka ba kafin a nada shi bisa mukami. Ya sha alwashin ganin duk wanda za a nada Minista ko wani mukami irin wannan a gwamnatinsa, dole ya bayyana abin da ya mallaka kafin ma a nada shi. Idan tafiya ta yi nisa aka lura ya kauce hanya, mun san abin da BUHARI zai yi, wannan ba sai an nanata ba! Domin a kara tamke bakin aljihun gwamnati, BUHARI ya sha alwashin ganin cewa duk ’yan siyasar da zai nada a mukamai, to albashin da doka ta tanada ne kurum za su karba. Wanda ya kasance mai dogon hannu, albashin da za a ba su, yana ga bai isarsa, dangane da haka ya sa hannun cikin baitulmali domin sata, to za a hukunta shi ko ita, nan take.
Saboda haka domin ya tabbatar da kowa ya bi, BUHARI ya sha alwashin ganin ya yi mulki mai tsabta, duk wani ko wata da yake kazami ko kazama, to, ba ya cikin tsarin tafiyar da mulkinsa. Buhari ba zai ci ba, ba kuma zai bari a ci ba!
Wata tambayar da kila wani zai iya yi ita ce, ai shi BUHARIN ai ba Allan Musuru ba ne, ba ya iya kasancewa a fadar Shugaban kasa, sa’annan yana sa ido kan abin da ministoci ko sauran mukarrabansa ke yi a ma’aikatu da hukumomin gwamnati ba? Lallai kam haka ne! Amma nan ma BUHARI ya samar da amsa. Ya sha alwashin da zarar ya hau karagar mulki zai samar da kuma kaddamar da Hukumar Kula Da Yadda Ake Ba Da Kwangila Da Aiwatar Da Ita, kamar yadda yake a cikin doka da aka ki aiki da ita. Ke nan Majalisar Ministoci da zai shugabanta ba za ta koma ta bayar da kwangila ba ce kurum, domin ba aikinta ba ne, irin yadda ake ta fama yanzu duk mako, an mai da zama irin na majalisar tamkar Kasuwar Kwangila, a maimakon zama don tattauna matsaloli da yadda za a shawo kansu.
Yin haka zai sa kowane minista da sauran shugabanni su shiga taitayinsu, domin za su fahimci wannan gwamnatin ba ta kwangila ba ce, ta yi wa al’umma aiki ce!
Haka kuma BUHARI ya sha alwashin ganin duk wani mai halin bera ko ma beran da ya taushe daddawar mutane bai kai labari ba. Ta yaya? Gwamnatin BUHARI za ta sake bitar dukkan rahotannin da hukumomi suka bayar dangane da albarkatu da arzikin kasa don a tabbatar ba a yin cuta ko kuma cutarwa. Ta haka arziki da jin dadin al’umma zai bunkasa, wadata ta samu, a kuma rage radadin talauci a cikin kasa.
BUHARI kuma ya sha alwashin hada kai da Majalisun kasa domin a samar da dokar TSEGUMIN KAR-TA-KWANA da za ta bayar da dama da kuma kariya ba tare da tsangwama ba ga duk wanda ya ga inda ake barna ya fito ya bayyana don a magance aukuwar hakan. Wannan zai bayar da dama ga sauran mutane da ba su kusa da fadar Shugaban kasa su taimaka wajen yaki da rashawa da almundahana a ko’ina a cikin kasa.
Sauran hukumomin da ake da su na yaki da cin hanci da rashawa da almundahana irin su ICPC da EFCC, gwamnatin Buhari ta sha alwashin yin aiki kafada-da-kafada da Majalisun kasa don kara musu karfi da ba su cikakken ikon bincike da hukuntawa da kuma sakar musu mara su sakata su wala ta hanyar samar musu da kudaden gudanar da aikinsu cikin ruwan sanyi. Haka kuma za a tabbatar da cewa shugabannnin wadannan hukumomi ba su zama ’yan-amshin-shatan gwamnati ko na kusa da gwamnati ba. Tunanin gwamnatin BUHARI game da wadannan hukumomin shi ne, ba sani ba sabo!
Haka kuma BUHARI ya sha alwashin ganin ministoci da ma’aikatu suna bayyana abin da suke yi a kai, a kai ga al’umma, kuma ’yan jarida na da damar su tambayi komai suke son sani, don su gudanar da aikinsu, in dai yana bisa doka da oda!
Haka kuma gwamnatin BUHARI ta sha alwashin neman hadin kan Majalisun kasa da bangaren Shari’a domin a rage facaka da dukiyar kasa da kuma al’umma, shi ya sa BUHARI yake cewa ‘da zarar na hau karagar mulki abu na farko-farko da zan fara yi shi ne mika wa Majalisun kasa DAFTARIN GWAMNATI NA KAWAR DA FACAKA DA DUKIYAR AL’UMMA DA YAkI DA RASHAWA DA ALMUNDAHANA.’
Wannan shi ne matakin da BUHARI zai bi domin kawo karshen wandaka da dukiyar kasa da ta zama kwalliya a halin yanzu.