Buhari: Alkawari kaya ne (3)

Yaya Gwamnatin Buhari za ta kawo karshen Boko Haram da rashin tsaro? Ba sai an bata miyan baki ba, daga cikin mutanen biyu (manya) da suke a fage a halin yanzu domin a zabe su su shugabanci Najeriya, ba wanda zai iya kawo karshen rikicin Boko Haram ko rashin tsaro da ya zame mana ruwan […]

Buhari: Alkawari kaya ne (3)
Buhari: Alkawari kaya ne (3)

Yaya Gwamnatin Buhari za ta kawo karshen Boko Haram da rashin tsaro?

Ba sai an bata miyan baki ba, daga cikin mutanen biyu (manya) da suke a fage a halin yanzu domin a zabe su su shugabanci Najeriya, ba wanda zai iya kawo karshen rikicin Boko Haram ko rashin tsaro da ya zame mana ruwan dare kamar BUHARI. Nan ma akwai dalilai masu gamsarwa.
Na farko dai matsalar rashin tsaro da ta addabi kasar nan gwamnati mai ci ta same ta tana ci ko kuma tana ruruwa, me ta yi domin kawo karshenta a cikin shekara 6 bisa karagar mulki? Saboda haka muna iya cewa gwamnatin da ta kasa katabus domin tsare mutuncin Najeriya da al’ummarta cikin shekara 6, me za ta iya yi cikin shekara 4 in an sake zaben ta?
Ba wannan ba ma, ta yaya za a iya kwatanta BUHARI da wani dangane da yadda za a magance matsalar tsaro a Najeriya? Mun dai san cewa BUHARI tsohon Janar ne, kuma kamar yadda ya sha fada, ya bauta wa Najeriya a matakai daban-daban har ya kai Janar, kuma Shugaban Dakarun Najeriya, matsayin da ya yi amfani da shi ya yi yaki domin kare martabar Najeriya.
Saboda haka ne BUHARI ya sha alwashin ganin bayan matsalolin tsaro da suka addabi kasar nan da zarar aka zabe shi Shugabn kasa. BUHARI zai yi yaki ne da matsalolin a matsayin jagora. Zai kasance tare da dakarun kasar nan ko’ina suke, ba wai ya yi zaune a cikin harabar fadar Shuganan kasa da ke Aso Rock ba, kamar yadda aka saba yi yanzu.
BUHARI ya sha alwashin tabbatar da jin dadin dakarun Najeriya da kuma na iyalansu. Zai kuma tabbatar da ganin duk dakaren da ya rasa ransa a fagen daga ya samu yabo da kyautatawar da ta dace, haka iyalansa ba za su koka da gwamnati ba. Su kuma wadanda hargitsin rashin tsaro ya auka wa za su samu kulawa ta musamman daga gwamnati.

Ta yaya gwamnatin BUHARI za ta cimma wadannan manufofi nata idan an zabe ta?
BUHARI ya sha alwashin daga martabar dakarun da ke a filin daga suna bauta wa kasarsu ta hanyar yabawa da kwazonsu a duk lokacin da hakan ya taso. Haka kuma za a dinga yayata irin kwazon nasu don al’umma ta gani ta kuma kara yabawa ita ma ta fuskar sa wadanda suka jajirce ko suka yi abin a zo a gani a cikin abubuwan tunawa da mutanen kwarai na kasa, sa’annan a dinga yi ana canza wa dakaru wuraren aiki da biyan su hakkokinsu kan kari. Sa’annan BUHARI zai tabbatar da ganin ana samun yaukakuwar sadarwa tsakanin dakarun da ke a bakin daga da sauran jami’an kula da tsaro don inganta aikinsu. Za a tabbatar da kiwon lafiyar dakaru da kuma ta iyalansu a kodayaushe, da kuma tabbatar da samar da ingantaccen matsuguni da muhalli ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a fagen fama.
Ba wannan kadai ba, da zarar BUHARI ya hau karagar mulki zai fito da kundin dabashiri da za a yi amfani da shi wajen kawar da matsalolin rashin tsaro da suka hada da na Boko Haram da rikice-rikicen kabilanci da na addini da satar jama’a da kuma fashi da makami da makamantansu. Daga cikin dabashirin da za a aiwatar, gwamnatin BUHARI ta sha alwashin samar da makamai da sauran kayayyakin da dakarun kasar nan ke bukata domin maido da tsaro da kare rayuka da dukiyar al’ummar kasar nan. Wannan ne ya sa BUHARI ya sha alwashin yin aiki kafada-da-kafada da gwamnonin jihohin da wadannan matsaloli suka addaba ba tare da nuna bambancin siyasa ba. Haka kuma BUHARI zai tuntubi shugabannin kasashe makwabta da ma sauran kasashen duniya domin ganin an kawo karshen ta’addanci irin na Boko Haram da satar danyen mai da duk wasu al’amurran rashin tsaro a kasar nan.
Daga cikin tsarin gwamnatin BUHARI idan ta kai gaci akwai tabbatuwar yin taro da ilahirin hukumomin tsaro a kai-a kai don a tabbatar komai na tafiya daidai a cikin kasa.
Ba sai ya fada ba, BUHARI kamar kowane irin mahaifi yana cikin alhini da damuwa irin wadanda iyayen da suka rasa ’ya’ya ko ’yan uwa ko dukiya daga rikice-rikicen rashin tsaro a kasar nan suke ciki. Zawara ne su ko marayu. Na dakaru ne ko na farar hula ku kuma iyaye da ’yan uwan ’yan’yanmu na Chibok. Gwamnatin BUHARI za ta yi iyakar yin ta ta ga an gano wadannan ’yan mata duk inda suke a cikin gaggawa da yardar Allah!
Mun kammala