Buhari ba ya cikin mawuyacin hali — Bashir Ahmad

Tsohon hadimin ya ce rahotannin da wasu kafafe suka wallafa ba gaskiya ba ne.

Buhari ba ya cikin mawuyacin hali — Bashir Ahmad

Bashir Ahmad tare da Shugaba Buhari

Bashir Ahmad, hadimin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce shugaban yana cikin ƙoshin lafiya a birnin Landan.

A cewarsa, labarin da ke yawo cewa Buhari na fama da mummunar rashin lafiya har yana kwance a ɗakin kulawa na musamman (ICU), ba gaskiya ba ne.

Bashir ya tabbatar da cewa Buhari ya yi rashin lafiya a baya, amma yanzu yana samun kulawar likitoci kamar yadda ya kamata.

“Lamarin ba kamar yadda wasu kafafen labarai ke yaɗa labari suka ruwaito ba, Buhari yana cikin yanayi mai kyau kuma magunguna na aiki a jikinsa,” in ji Bashir.

Ya ƙara da cewa suna fatan zai samu cikakkiyar lafiya nan ba da jimawa ba.

Idan ba manta ba, Garba Shehu, mai magana da yawun Buhari ne, ya bayyana cewar yana cikin mawuyacin hali a birnin Landan.