Buhari ba zai ceci gwamnonin APC ba a zaben 2019-PDP

Jam’iyyar PDP ta ce shugaba Muhammadu Buhari ba zai ceci gwamnonin APC daga shan mummunan kaye a zaben shekarar 2019 ba.   Babbar jam’iyyar adawar ta ce gwamnonin APC suna ta rigegeniyar zuwa Abuja don su samu goyon bayan Buhari a zaben shekarar 2019 saboda rashin tabuka abin-a-zo-a-gani a jihohinsu.   A sanarwar da ya […]

Buhari ba zai ceci gwamnonin APC ba a zaben 2019-PDP

Jam’iyyar PDP ta ce shugaba Muhammadu Buhari ba zai ceci gwamnonin APC daga shan mummunan kaye a zaben shekarar 2019 ba.
 
Babbar jam’iyyar adawar ta ce gwamnonin APC suna ta rigegeniyar zuwa Abuja don su samu goyon bayan Buhari a zaben shekarar 2019 saboda rashin tabuka abin-a-zo-a-gani a jihohinsu.
 
A sanarwar da ya fitar a Abuja, Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar na Kasa, Kola Ologbondiyan ya kalubalanci jam’iyyar APC da ta gwada farin jininta ga ’yan Najeriya ta hanyar gudanar da zabubbukan kananan hukumomin jihar da ke jihohinsu.