Buhari ba zai dauki-dora ga ’yan takara ba – Yariman Bakura

Aminiya ta zanta da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura, inda ya bayyana cewa Shugaba Buhari ba zai yi dauki-dora ba a wajen tsayar da dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC: Shugaban Kasa mai ci dan yankin Arewa maso Gabas ne kamar kai, me ya sa kake neman Shugaban Kasa? Saboda […]

Buhari ba zai dauki-dora ga ’yan takara ba – Yariman Bakura

Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura

Aminiya ta zanta da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura, inda ya bayyana cewa Shugaba Buhari ba zai yi dauki-dora ba a wajen tsayar da dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC:

Shugaban Kasa mai ci dan yankin Arewa maso Gabas ne kamar kai, me ya sa kake neman Shugaban Kasa?

Saboda ni ma dan Najeriya ne. Ban ciki yarda da batun yanki ba. Wai a ce wani dan wajen kaza ne, kawai a samu mutane masu nagarta shi ne. Kowa ya kawo irin aikace-aikacen da zai yi wajen ciyar da kasar gaba. Sai mutanen Najeriya su tantance. Ba wai daga ina mutum yake ba ne abin dubawa. Don haka a tunanina, mutum za a duba ba yankinsa ba. Idan ba haka kuma sai dai mu nemi a gyara a Kundin Tsarin Mulkin Najeriya domin kama-kama. Idan kuma maganar kama-kama za a yi, sai a ce to Arewa maso Gabas ta yi, sai Kudu maso Kudu, ke nan duk dan yankin ko ya cancanta ko bai cancanta ba sai a zabe shi.

Akwai rade-radin cewa Shugaba Buhari ya yi yarjejeniya da Bola Tinubu cewa zai ba shi mulki a shekarar 2023. Yaya za ka yi da wannan?

Ba na tunanin Najeriya ta wani mutum daya ne daga cikinsu, kuma ba na tunanin wani dan Najeriya komai matsayinsa da zai nuna inda mutanen Najeirya za su dosa. Siyasa lamari ne na zabe, mutane su zabi wadanda suke so. Idan ya yi yarjejeniya da Bola Tinubu, wannan yarjejeniyar ba za ta yi amfani ba ko a wajen tsayar da dan takara. Misali Shugaban Kasa ya yi sanarwa, kuma jam’iyyarmu ta APC ta sanar cewa tsarin kai-tsaye za a bi wajen fitar da dan takara kamar yadda muka zabe shi a zaben da ya wuce. Shin zai ce ne kowa ya zabi Bola Tinubu a zaben? Ina da yakinin zabe za a yi mai inganci, don haka maganar yarjejeniya maganar siyasa ce kawai. Kuma ba na ma tunanin hakan domin ba na tsammanin Buhari da na sani zai shiga yarjejeniya irin wannan. Ya san ba shi da wannan karfin iko na bayar da mulki ga wanda yake so kawai. Don haka kawai jita-jita ce.

Amma idan Shugaba Buhari ya tsayar da mutum daya za ka bi shi?

Na fada cewa Buhari ba ya da tsayayyen dan takara guda daya.

Amma kana da mutane da kudin da za ka iya fafatawa da Tinubu?

A bangaren iyawa, ina tunanin ina da lafiya da ilimi da sanin makaman aikin da nake ganin sun isa in yi amfani da su wajen mulkin kasar nan. A bangeren kudi kuma, ba ka tsayawa tunanin kudi idan za ka shiga takara. Idan har ina da dan abin da zan zagaya in yi kamfe shi ke nan. Sauran duk gudunmawa ce daga mutanen kasa wadanda suke cikin jam’iyyar, domin jam’iyya ce take daukar nauyin dan takara ba dan takara ne zai dauki nauyin jam’iyya ba. Ba ni da Naira miliyan 20 lokacin da na nemi takarar Gwamna, haka kuma na zama Gwamna. Allah ne Yake kaddara komai, kawai abin da ake bukata shi ne tsarkake zuciya. Ba ina son zama Shugaban Kasa domin in tara dukiya ba ce ko in samu karfin mulki. Maganar yi wa kasa aiki ne.

Shin kana da-na-sanin rasa Zamfara da kuka yi?

Dukkan mutanen Zamfara nawa ne. Gwamnan yanzu tsohon kwamishinana ne. mun yi APP tare, inda ya nemi shugaban karamar hukumarya fadi. Ni na ba shi kwamishinan  kananan hukomomi, inda yake shugabantar wanda ya kayar da shi a zabe. Sai ya bar mu lokacin da tsohon Gwamna ya koma PDP. Yanzu kuma ya zama Gwamna. A duk inda ya yi magana, yana yawan bayyana ni a matsayin tsohon mai gidansa, don haka ni ma ba zan bar fadin matsayinsa a wurina ba, sannan kuma Allah Ya ba shi matsayi da mulki. Duk wanda ya lashe zaben Gwamnan Zamfara dole in goya masa baya. Bayan zabe ba na damuwa da jam’iyya. Idan zabe ya zo ne kawai bari in goyi bayan wane.

Akwai batun gwamnanku na yanzu zai koma APC daga PDP?

Eh, akwai. Ba abin mamaki ba ne idan ya dawo. Muna aiki da kuma magana a kai. Kowane dan siyasa yana son ya samu mutane a jam’iyyarsa, musamman ma Gwamna. Idan zan samu Gwamna a tare da ni, ai jam’iyyar za ta fi kyau. Kuma maganar nan ta yi nisa.

Ke nan ya kusa dawowa?

Eh, ya kusa.

Amma abin mamaki shi ne, kana batun Gwamnan zai dawo APC, amma kuma mutanen a kananan hukumomi suna ta koma jam’iyyar gwamna ta PDP?

Wannan duk siyasa ce. Ba za ka gane abin da ke faruwa ba. Ba haka nan zai dawo jam’iyyar ba, ba tare da gane wadanda suke tare da shi ba. Amma ka ga yanzu idan ya taho tare da su, sun zama mutanensa ke nan. Kowane dan siyasa yana son ganin cewa dan siyasa wane da wane mutanena ne.

Shi ma Yari zai shiga cikin tsarin?

Zai shiga mana. Zai ci gaba da kasancewa dan APC sai dai idan ya fice.

Shin Gwamna Matawalle yana yi wa ’yan APC bi-ta-da-kulli?

Ban san abin da ke faruwa ba gaskiya. A siyasa akwai abubuwa da dama da ba za ka iya karantawa ba, kuma ba za ka gane ba har sai ka san makasudin abin. Kuma ban binciki wannan lamarin ba domin ina tunanin abu ne na cikin gida, da bai kamata in da mu kaina ba. Kowa na girmama ni a Zamfara, shi ya sa nake kokarin kare mutuncina wajen kin shiga lamarin da bai fito min fili ba.

Mene ne tunaninka game da soke dokar da tsohon Gwamna ya yi kan fanshon tsofaffin gwamnoni?

Na amince da shi. Kundin tsarin kasar nan ya ba Hukumar Haraji da Albashi ta Kasa ta kawo abin da za a ba gwamnoni idan sun bar ofis. Wannan ne ya sa Gwamna Yari ya mayar da karatun yaranmu ya zama za a biya kudi ne. Kula da lafiya za a biya Naira miliyan 10, da miliyan 5, amma ya mayar 10. Wannan Gwamnan kuma sai ya ce ba daidai ba ne. doka ce ta sanya abin, kuma yanzu doka ce ta cire shi. Don haka duk abin da doka ta yi, ya yi daidai.

Yaya za ka kwatanta mulkin Yari da na Matawalle?

Dukansu sun yi kokari. Yari ya yi nasa kokari, Matawalle yana yin nasa kokarin yanzu.

Akwai rikice-rikice a Jam’iyyar APC, har wadansu suna koke-koke cewa a cire Oshiomhole a shugabanci. Me za ka ce?

Ni na fi yarda da bin tsarin doka. Duk kokarin cire shugaba ba tare da bin doka ba, ba na tare da shi. Duk wanda yake son Oshiomhole ya sauka, ya bi doka. Surutu ba shi ba ne, ba kawai za ka yi tunanin cewa wadansu mutane ba sa son wannan mutumin ba ne kawai shi ke nan. Misali kamar mutane ne su yi zanga-zangar ba sa son Gwamna ko Shugaban Kasa. Zabe aka yi Oshiomhole ya ci, kuma akwai tsari da jam’iyyarmu ta gindaya idan za a cire shugaban jam’iyya.

Ka jagoranci addu’a ga tsohon Shugaban Kasa marigayi Umaru ’Yar’aduwa da Jonathan, me ya sa ba ki yi wa Buhari ba?

Wa ya fada maka ban yi ba. Ka san wadansu ba sa so a bayyana wasu abubuwa. Buhari irin wadannan mutane ne. Amma muna yi masa addu’a. babu ranar da zan yi Sallah ban yi masa addu’a ba. Babu ranar da zan yi magana da malamai ba tare da na bukaci su yi masa addu’a ba. Akwai hanyoyin addu’a ga Allah da yawa. Idan kana yi domin Allah, ba sai ka bayyana ba.

Yaya za ka bayyana mulkin Buhari a bangaren tsaro?

A tunanina yana kokarin gaske. A zamanin Jonathan, Boko Haram sun kawo Abuja, sun kai hari a ofishin Majalisar Dinkin Duniya. Amma yanzu fa? Suna Borno an danne su.

Yaki da ’yan ta’adda ba abu ba ne mai sauki da za ka kammala a rana daya. Su ma manyan hafsoshin kasar suna kokarinsu domin sun dauki yakin kamar nasu ne. Na san abin da ke faruwa, amma wadansu mutanen ba su sani ba.

Yaya batun gonarka fa?

Gona lafiya kalau. Na fara ne da kaji masu kwai 5000 a shekarar 2003 wadanda na sayo a lokacin a gonar Obasanjo domin na fara ne bisa shawarar Obasanjo din da tsohon Gwamnan Jihar Neja, marigayi Kure. Amma a yanzu, ina da kaji guda 450,000 kuma ina fitar  da akalla kwai kwando (crate) 9000 kullum. Ina godiya ga Allah ina da abin yi bayan makaranta da yanzu nake zuwa na Larabci da addinin Musulunci da kuma siyasa.

Yaya kake sayar da kwayayen?

Muna da dillalai. Ina tabbatar maka cewa ba ma iya gamsar da masu nema.

Yaya batun kwantiraginka da Gwamnatin Jihar Zamfara a kan kwai?

Tun kafin Yari ake wannan, kuma har yanzu ana ci gaba. Wadansu mutane suna tunanin ina sayar wa gwamnati da kwan a kan Naira dubu 10 a kowane kwando, amma ba haka ba ne. Naira dubu 1 nake sayar musu. Ana sayar wa dillalai a kan Naira 850 ko 900. Su kuma aka kara Naira 100 saboda kudin motar kai musu zuwa makarantu.