Buhari ba zai samu tarbar kirki daga talakawan Zamfara ba!

Jihar Zamfara, jiha ce da tun tarihin takarar Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2003 yake samun gagaruwamar tarba daga talakawan jihar duk lokacin da ya shigo ta, saboda kauna da fata nagari da talakawan suke yi masa ne, kuma hakan ya sa bai taba faduwa zabe a jihar ba. Hatta lokacin da jihar ba hannun […]

Buhari ba zai samu tarbar kirki daga talakawan Zamfara ba!
Buhari ba zai samu tarbar kirki daga talakawan Zamfara ba!

Jihar Zamfara, jiha ce da tun tarihin takarar Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2003 yake samun gagaruwamar tarba daga talakawan jihar duk lokacin da ya shigo ta, saboda kauna da fata nagari da talakawan suke yi masa ne, kuma hakan ya sa bai taba faduwa zabe a jihar ba. Hatta lokacin da jihar ba hannun jam’iyyar da ya yi takara take ba, kamar a 2011 lokacin da Gwamna yake Jam’iyyar PDP shi kuma Shugaba Buhari ya yi takara a rusashshiyar Jam’iyyar CPC.

Kuri’un da Shugaban ya samu a 2015 lokacin da ya lashe zaben da ya kafa tarihin doke Jam’iyyar PDP tare da kayar da Shugaban lokacin Goodluck Jonathan, al’ummar Jihar Zamfara sun zuba masa kuri’a mai yawa. Haka ya tabbatar da Zamfarawa cikakkun masoya Shugaba Buhari ne.

Sai dai kash! Bayan mun yi nasara zama daga wadanda suka zabi gwamnatinsa, da kyakkyawan fatan zai taka muhimmiyar rawa wajen kawar da matsalar tsaron da ke addabar Arewa musamman al’ummar Arewa maso Gabas da burbushin wanda ke shafar Jihar Zamfara da lungu da sakon kasarmu.

Alhamdulillahi Shugaban ya taka rawar gani, kwarai da gaske a yankin Arewa maso Gabas, inda ta’adin kungiyar Boko Haram ya illata, har ana iya bugun gaban an yi nasara ko karya lagon kungiyar ta’addanci ta Boko Haram. Yayin da yanzu suka koma harin sari-ka-noke wanda ke nuna raunin kungiyar karara.

Sai dai kash! A Jihar Zamfara ba haka abin yake ba. Domin ba a taba lokacin da aka dauki rayukan al’ummar jihar aka salwantar aka mayar da dama daga cikin ’ya’yan jihar  marayu ba, aka mayar da  mata gwaggwaren  dole, masu arziki suka zama matsiyata, garuruwa suka zama kufai, kamar lokacin jagorancin Shugaba Buhari ba.

Duk da cewa mafiya yawanmu talakawan jihar muna dora laifin kashi 80 cikin 100 na matsalar ga gwamnanmu na yanzu, wanda shi ne ya yi sakaci da matsalar tun tana karama, har ta gawurta zuwa inda take yanzu, sai dai akwai wadansu da dama a talakawan jihar da ke ganin akwai sakaci sosai daga bangaen Shugaba Buhari, wanda shi ne mafi yawan nauyin kare rayuka da dukiyoyin al’umma ya rataya a wuyansa, ko ba komai shi ne dukan rundunonin tsaron kasa ke karkashinsa. Hakan ya sa  jama’a da dama suka dawo daga rakiyar Shugaban.

Abu na biyu shi ne; halin da Jam’iyyar APC ta samu kanta a Jihar Zamfara inda kowane bangaren na ’yan siyasar jihar ba APC kurrum ba, ke cikin zaman zullumi da rashin sanin abin da zai faru, kuma hakan ya sa harkokin siyasa suka yi tsit, duk da kasa da wata daya a yi babban zaben  bana. Ko shi Gwamnan Jihar a cikin halin tsaka mai wuya yake, duk yana kammala zango na biyu da tsarin mulkin kasa ya ba shi damar yi ne.

Idan muka dubi mafiya yawan mukarraban Shugaba Buhari a Zamfara da ake tunanin za su iya nema masa jama’a, ba su da wani amfani ga al’umma, da har za su iya tara masa jama’a.

Misali Ministan Tsaro Janar Mansur Dan Ali dan asalin Birnin Magaji ne, ba wani tagomashi ke gare shi ga al’umma ba. Hasali ma ba na tunanin zai iya tara wa shugaba mutun dubu 3.

Ba maganar jakadu biyu da muke da su ake yi ba, Ambasada Mairiga da takwaransa Barista Garba Gajam. Domin jama’a na korafin an nada su kan mukaman ne, don su tallafi iyalansu. Kamar yadda zahirin hakan ya nuna la’akkari da halin suman da suka yi ba wani labarinsu da talakan jihar ke ji, ballantana ya yi tunanin samun sa’ida daga gare su, balle talakawan suna kaunar Shugaba Muhammadu Buhari dominsu. Don haka ba mu tunanin za su taka wata rawa wajen shigowar Buhari a Zamfara.

Akwai tsantsan son Buhari a zukatan mafiya yawan talakawan jihar, sai dai ya kamata a yi sara tare da duban bakin gatari.

Allah Ya tallafi kasarmu da jiharmu ta Zamfara Ya dora mu a kan tafarki nagari, tare da yi mana mafita a kan kangin rashin tsaron da muke ciki. Allah Ka bai wa jagororinmu ikon yi mana adalci, mu kuma Allah Ka ba mu ikon yi musu biyayya da ba ta kauce wa addininKa ba.

Daga Abdulmalik Sa’idu Mai Burodi Tashar Bagu Gusau.

08069807496.