Buhari babban barazana ne ga PDP – Halifa Hassan Yusuf

Galadiman Damaturu Halifa Hassan Yusuf ya bayyana zaben Janar Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar Jam’iyyar APC da cewa babban kalubale ne ga Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan.Halifa Hassan Yusuf ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya a garin Damaturudangane da zabar Janar Buhari a matsayin dan takarar Jam’iyyar APC a zaben Shugaban […]

Buhari babban barazana ne ga PDP – Halifa Hassan Yusuf
Buhari babban barazana ne ga PDP – Halifa Hassan Yusuf

Galadiman Damaturu Halifa Hassan Yusuf ya bayyana zaben Janar Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar Jam’iyyar APC da cewa babban kalubale ne ga Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan.
Halifa Hassan Yusuf ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya a garin Damaturu
dangane da zabar Janar Buhari a matsayin dan takarar Jam’iyyar APC a zaben Shugaban kasa da ke tafe a bana.
Ya ce “Ga dukkan alamu zaben Janar Buhari a matsayin dan takarar Jam’iyyar APC kalubale ne ga PDP, kuma hakan zai tilasta ta shiga taitayinta domin ba ta yi tsammani zai lashe zaben share fagen ba, wanda hakan na iya jawo mulki ya kubuce mata a wannan karo.”
Galadiman na Damaturu ya ce, alamomi sun nuna cewa jam’iyyarsu ta APC ce ke da nasara a zaben da ke tafe domin al’ummar Yarbawa ne kan gaba wajen ba da goyon baya ga takarar Buhari kuma an dauki dansu a matsayin wadda zai mara wa Buhari baya.
Sai ya kirayi al’ummar Arewa su hada kai don zabar Buhari a zaben da ke tafe ko sa samu kansu
musamman game da halin tabarbarewar tsaro da aka jefa yankin ciki saboda siyasa.
Halifa Hassan Yusuf ya bukaci Janar Buhari ya yi kokarin ganin an gudanar da adalci ga duk wani dan takarar da zai tsaya a Jam’iyyar APC, musamman a harkokin cikin gidan jam’iyyar don
kauce wa farraka ’ya’yanta ganin a halin yanzu ta cika ta batse da jama’a saboda kyawawan manufofinta.

Zaben 2015: ’Yan siyasa sun fara zarya zuwa gidan Janar Babangida

Daga Muhammad danladi Ibrahim, Minna

’Yan siyasa daga sassa daban-daban na kasar nan na ci gaba da ziyartar tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida domin neman tubarraki ganin cewa zabubbukan kasa da za a gudanar a bana suna kawo jiki.
A ranar Litinin ne Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ziyarci Janar Babangida a gidansa da ke Minna inda suka yi ganarwar sirri na wani lokaci, ziyarar da daga baya ake cewa ba ta rasa nasaba da dawowar Babangida daga kasar Jamus inda ya shafe wani lokaci yana jinya.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa wakilinmu cewa halin da Najeriya ta samu kanta musamman Arewa na tabarbarewar tsaro da tattalin arzikin da ya yi sanadiyyar watsewar miliyoyin jama’ar da suka rasa dukiyoyi da rayuka wasu suka zama ’yan gudun hijira na daga cikin batutuwan da shugabannin biyu suka tattauna a kai.
A ranar Asabar da ta gabata ne Shugaban Goodluck Ebele Jonathan ya ziyarci Janar Babangida inda ya shaida masa halin da kasar take ciki, tare da neman shawarwari kan yadda zai shawo kan kalubalen da suka hada da rashin tsaro ga kuma zabe mai zuwa.
Janar Babangida, ya yi kira ga ’yan Najeriya su mara wa Shugaban baya domin ya samu nasarar ciyar da kasar nan a gaba na dora ta a jerin manyan kasashe 20 da suka fi karfin tattalin arziki a duniya.

Ni dan PDP ne daga sama har kasa – Gwamna Yuguda

Daga Hamza Aliyu, Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya sake nanata aniyarsa ta cigaba da zama a jam’iyyarsa ta PDP ba tare da sauya sheka zuwa wata jam’iyyar ba.
Gwamna Yuguda ya bayyana haka a ranar Talata lokacin da ya je gidan rediyon Ray-Power domin amsa tambayoyi al’ummar jihar kai-tsaye a wani shiri mai sunaTumbin Giwa da ake gabatarwa a gidan rediyon.
Gwamna Isa Yuguda ya kara da cewa “Ni dan Jam’iyyar PDP ne tun daga sama har kasa kuma zan ci gaba da zama a PDP domin da yawa daga cikin ’yan Najeriya sun samu romon mulkin dimokuradiyya albarkacin wannan jam’iyya ta PDP.”
Da yake tofa albarkacin bakinsa game da abin da ya faru a makon jiya a babbar kasuwar Santaral Gwamna Yuguda ya bayyana cewa sakamakon binciken da hukumomin tsaro suka gabatar masa a matsayina na Gwamnan Jihar ya nuna ba bom ba ne ya fashe a cikin kasuwar, gwangwanayen maganin sauro ne suka fashe daga bisani wasu daga cikin shagunan kasuwar suka kama da wuta.