Buhari bai ba da izinin biyan $6.2m ga masu sa ido kan zaɓe ba — Boss Mustapha
Sa hannun da takardun suke ɗauke da su na Buhari na bogi ne.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya musanta ba da izinin biyan dala miliyan 6.2 ga masu sanya ido kan harkokin zaɓe na ketare.
Boss Mustapha ya bayyana hakan ne a gaban wata babbar kotu da ke Abuja a ranar Talata.
- Tsohuwar da ta shafe shekara 32 tana maganar sa’a guda kacal duk rana
- An kama matasa 3 kan zargin kashe dilan tabar wiwi a Gombe
Boss Mustapha ya shaida wa kotun cewa ba shi da masaniya kan wata takardar ba da izini ga tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele wadda ake zargin ta sahale masa biyan sama da dalar Amurka miliyan 6.2 ga masu sanya ido a zaɓe na ƙasashen waje.
Tsohon Sakataren Gwamnatin wanda yana daga cikin shaidu a ƙarar da ake tuhumar Emefiele, ya ce a tsawon shekaru biyar da watanni bakwai da ya yi yana riƙe da wannan muƙamin ba shi da masaniya kan takardar.
Boss Mustapha ya kuma bayyana wa kotun cewa, ba daga ofishinsa takardar ta fito ba kuma ba daga fadar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari takardar biyan kuɗaɗen ta fito ba.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya ya kuma shaida wa kotun cewa babu ruwan gwamnatin tarayyar da biyan masu sa ido na ƙasashen wajen kuɗaɗe.
A ƙunshin takardun bayanan da jagoran lauyoyin masu kara, Rotimi Oyedepo, suka gabatar masa, tsohon Sakataren Gwamnatin ya ce bai taba ganinsu ba, hasalima sa hannun da suke ɗauke da su na Buhari na bogi ne, sai dai ya bar wa kwararru hakan su tabbatar.
Mista Emefiele dai na fuskantar tuhume-tuhume 20 a shari’ar, waɗanda suka haɗa da cin hanci da rashawa, haɗa baki domin aikata laifi, da cin amana da ungulu da kan zabo da kuɗaɗen da suka kai dalar Amurka $6,230,000.
Ana zargin tsohon gwamnan na CBN da yin amfani da sa hannu na jabu domin karɓar kuɗaɗen ba bisa ƙa’ida ba.
Masu sa ido a babban zaben ƙasar da aka yi a shekarar 2023 na ƙasashen waje ake ikirarin an biyan kuɗaɗen.