‘Buhari bai tsayar da ranar sanya hannu a kasafin kudi ba’
Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta tsayar da ranar sanya hannu a kasafin kudin bana ba tukuna. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Sanata Udoma Udo Udoma jiya (Laraba), bayan kammala zaman majalisar zartarwa wadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta. Takaddama ta barke ne tsakanin ‘yan majalisa da […]

Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta tsayar da ranar sanya hannu a kasafin kudin bana ba tukuna.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Sanata Udoma Udo Udoma jiya (Laraba), bayan kammala zaman majalisar zartarwa wadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Takaddama ta barke ne tsakanin ‘yan majalisa da kuma bangaren zartarwa, inda aka kasa samun maslaha.
‘Yan majalisa sun shigar da wasu sauye-sauye a kudin kasafin kudin, abin da wasu suke ganin ya sanya shugaban kasar kin amincewa da shi, bayan Majalisar Dokokin ta aika masa don ya sanya hannu saboda a fara aiki da shi.