Buhari bai yarda da bokanci ba – Garba Shehu
Fadar Shugaban kasa ta musanta rade-radin da wasu kafafen labarai na intanet suka bayar cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki komawa Fadar Shugaban kasar ne saboda shawarar da wasni boka daga Senegal ya ba shi. Wata sanarwa da ta fito daga Kakakin Shugaban kasar Malam Garba Shehu ta ce Fadar Shugaban kasa “ba ta […]
Fadar Shugaban kasa ta musanta rade-radin da wasu kafafen labarai na intanet suka bayar cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki komawa Fadar Shugaban kasar ne saboda shawarar da wasni boka daga Senegal ya ba shi.
Wata sanarwa da ta fito daga Kakakin Shugaban kasar Malam Garba Shehu ta ce Fadar Shugaban kasa “ba ta ji dadin wannan labari ba,” inda ta ce Shugaba Buhari cikakken Musulmi ne da ya yi imani da tare da mika al’amuransa ga Allah.
Sanarwar ta ce, babu Musulmin kirki da ya yi imani da Allah da zai rika dogaro da wani karfi na dan Adam mai mutuwa da ba zai iya kare kansa ba balle ya kare wasu mutane daban daga abin da aka kaddara musu.
Malam Garba Shehu ya ce batun “Wani boka ko malami yana tsarkake Fadar Shugaban kasa kafin Shugaba Buhari ya tare a ciki,” zace-zace ne na masu yada jita-jita.
Sanarwar ta kara da cewa, abin takaici ne a jingina rashin tarewar Shugaba Buhari cikin fadar kan wata shawara daga wani boka.
A cewa Shehu aikin gyara fadar ce babban dalilin rashin komawar Shugaba Buhari cikin fadar Shugaban kasar.