Buhari: Canjin dole ne? (2)
Shin da gaske ne canji muka zaba ko dai son rai da gaggawar dole abubuwa su canza ko da gora? Shin ba mu jin cewa ba mu kyautata wa Buhari da gwamnatinsa in muka tsaya kai da fata cewa sai an yi mana yadda muke so ko da kuwa hakan ba shi ne mafita ba? […]
Shin da gaske ne canji muka zaba ko dai son rai da gaggawar dole abubuwa su canza ko da gora? Shin ba mu jin cewa ba mu kyautata wa Buhari da gwamnatinsa in muka tsaya kai da fata cewa sai an yi mana yadda muke so ko da kuwa hakan ba shi ne mafita ba? Shin ba mu jin idan muka ci gaba da bin irin wannan tafarki za a iya kai wani lokaci da za mu sa shugabannin da muka zaba su watsar da kwallon mangoro domin su huta da kuda? Shin wai ma canjin da muke bukata daga Buhari da gwamnatinsa, shin wai dole ne, mu zauna haka nan mana?
Na san ba kowa ne zai amince da irin wannan tunanin ba, amma a bisa gaskiya abubuwa biyu ke kara bayyana bisa halin da muke ciki. Ko dai Buhari yana neman gazawa a shugabancin da muka zabe shi ko kuma, da ma can shigo-shigo ba zurfi muka yi masa, shi kuma ya burma, domin mun san ba za mu bari ya kawo canjin ba, domin ba shi muke bukata ba! Me ya sa zan fadi haka?
Mu koma kan korafe-korafen da muke ta yi a halin yanzu na rashin sanin makoma game da al’amuran kasar nan, da muke ganin cewa duk matsalar ta Buhari ce. Shin matsalar mai da rashin wutar lantarki, yau ne suka same mu, yau ne suka zama ruwan-dare ko suka auka wa al’umma ko kuwa muna nufin cewa sai da Buhari ya hau ne, suka kunno kai? Shin hauhawar farashin man fetur daga wannan zamani na Buhari aka soma ganin haka, ko kuwa da can ma an yi, ci gaba kurum aka yi? Na san amsar ba za ta taba zama eh ba sai dai a’a, to me ya sa za mu dage cewa an kasa yin komai ko kuma an ki yin komai game da wannan matsala? Shin tsawon wane lokaci ne ya dace a ce an kawar da matsalar man fetur ko kuma hauhawar farashin man fetur? Ana da wani takamaiman lokaci da ake jin cewa ya dace a ce an ga bayan wannan matsala? Idan babu, me ya sa muke yawan kokawa? Muna kokawa ne saboda Buhari kwance yake magashiyyan ba ya komai game da samar da hanyoyin kawar da wadannan matsaloli ko kuwa muna ganin cewa wasa kurum yake da hankalinmu, ya zo ne kurum ya kwashi garabasa, ya yi yawace-yawace a duniya don jin dadi ganin ya kai shekara 70 da dori bai ji dadin rayuwa ba?
Abin na da daure kai in mutum ya tsaya ya yi nazarin abubuwan da mutane ke fada game da halin da shugabancin kasar nan yake ciki a karkashin shugabancin Buhari. Buhari ya yi wa kamfanin NNPC garambawul, domin a samu hanyar yin gyara, amma ba wanda ya ga katabus a nan. An kori na kora, daga cikin hamshakan hana ruwa gudu a kamfanin NNPC, amma an ce ba haka ake so ba, korar ma ai ta son rai ce. An shiga bincike da tumbuko duk inda barna take game da matsalolin harkar hakowa da tace danyen mai da rarraba shi da shigo da shi daga waje, amma ba mai ganin wannan, sai lalakin ake gani na rashinn daidaitar lamura.
Tambayar da mutum kan iya yi ita ce, shin su wa ke hana ruwa gudu a wajen daidaita lamuran harkokin samarwa da rarraba man fetur a kasar nan? Su wane ne ke sayar da dan man da ake samarwa? Su wa ke hada-hadar man fetur a kasar nan, cewa nake ’yan Najeriya ne? Ko kuwa dai Shugaba Buhari ne ke hako danyen man fetur? Shi ke tace shi, shi ke rarraba shi? Shi ke sayar da shi a gidajen man ta hanyar tsawwala masa farashi da ya gallabi al’umma? Cewa nake ’yan Najeriya ne ba aljannu ko mala’iku ba! Shin don Buhari ya ce shi ne Ministan Harkokin Man fetur shi ne ya sa muke dora dukkan wani laifi na wannan ma’aikata a kansa, muke ganin cewa yana neman gazawa ko kuwa dai mu ne ’yan Najeriyar da ke yi masa zagon-kasa ke da laifi? Mu ne da ke neman canjin ke hana canjin samuwa? Ko kuwa mu ne da ke kukan abubuwa sun ki motsawa, amma muke dora laifi inda ba nan ya kamata ba? Mu auna da kyau!
Haka lamarin yake a wajen samar da makamashin wutar lantarki! Kullum kukan shi ne NEPA ta ki gyaruwa! Wuta ta ki zama! Farashin da ake biya ba wutar lantarki sai hauhawa yake yi ba kuma wutar! Wasu har cewa suke gara jiya da yau, domin ba su ga canjin da ake magana ba. Idan ka tambaya me ya sa jiya ta fi yau, abin da za su fada shi ne, ai da ana samun wutar lantarki, kuma ga saukin biya. Amma yau sai hakilon ana gyara amma abubuwa sai kara tabarbaewa suke yi. Amma da yawa irin wadannan mutane ba su fahimci cewa ai ba kowa ne matsalar ba face su kansu. Da can da ake magana abubuwa na da kyau ai tamkar wutar daji ce a cikin dare, ci ta yi, ta yi, har sai da ta gama barna, sa’annan aka farga, shi ya sa muka tashi cikin irin wannan hali da muka samu kanmu. Yanzu kuma da aka samu mai kula, ya ga cewa wutar dajin ba ta tashi ba, ko cikin dare ko rana, yana kuma kira da a mike tsaye a tanadi ruwa don ko-ta-kwata, ake ganin cewa ai shi ne fetur da ke kara hasa wutar. Ina adalci a nan?
Irin wannan ne ke sa wasu ke tunanin ko dai an shirya ta ne tunda farko, ana son gwamnatin Buhari ta gaza sai a samu abin fada ko kuma da wata manufar da ba a san da ita ba. Mu dubi wasu misalai mu gani da kyau. Duk da irin rashin hana ido barci da Buhari ke yi na ganin ya kawo karshem matsalar rashin man fetur da inganta farashi, kullum al’amarin sai kara ta’azzara yake yi, laifin wa? Buhari? Sai dai ’yan Najeriya dai! Rashin isasshen makamashin wutar lantarki fa, laifin ma na Buhari ne? Ko alama, namu ne ’yan Najeriya! Matsalar lalacewar tattalin arzikin kasa da ake fama da shi fa, shi ma laifin na Buhari ne? In har na Buhari ne, ke nan shi ne ya sa wasu ma’aikatan Gwamnatin Tarayya suka yi wa kasafin kudin wannan shekara huji, suka jefa wani abu a ciki, wanda ba shi ne ainihin abin da Buhari ya tanada ba. Nan kuma Buhari ne ya sa su yin haka domin su yi wa gwamnatinsa zagon-kasa? Abin da daure kai wallahi!
Za mu ci gaba