Buhari: Canjin dole ne? (3)

Ba wai nufina ba ne in zakalkale da cewa Buhari bai da laifi a cikin irin wannan tarmahaha da muke ciki a halin yanzu ba, amma a kullum tambayar da har yau an ki ko ba a son ba ni amsa ita ce, wai me Buhari zai samu na daga tagomashin rayuwa in har ya […]

Buhari: Canjin dole ne? (3)
Buhari: Canjin dole ne? (3)

Ba wai nufina ba ne in zakalkale da cewa Buhari bai da laifi a cikin irin wannan tarmahaha da muke ciki a halin yanzu ba, amma a kullum tambayar da har yau an ki ko ba a son ba ni amsa ita ce, wai me Buhari zai samu na daga tagomashin rayuwa in har ya fitar da kasar nan daga cikin halin kaka-ni-ka-yi? Lambar yabo ta kasa za a ba shi wadda ta fi wadda yake da ita a halin yanzu? Ko kuwa za a tallata shi a duniya ne domin ya kasance Shugaban Majalisar dinkin Duniya? Ko kuwa dai za a tara masa dukiyar da har Mahadi ba zai taba talauci ba, shi da iyalansa da jikoki da tattaba-kunne? Ko kuwa wani matsayi na musamman za a sama masa a ranar Lahira idan ya kasance mai ceton al’ummar Najeriya? Me zai samu?
Ina sane kamar sauran al’umma cewa Buhari mutum ne kamar kowa, yana da nasa matsalolin, idan kuma ya ga lallai shugabancin kasar nan da yake yi ba zai haifar wa kasar nan abin a-zo-a-gani ba, ina da yakinin cewa zai iya ajiye shugabanci wani ya hau domin gyarawa. Na san da haka! Ke nan akwai abin da ke hana ruwa gudu, wanda kuma gano shi da magance shi, shi kansa aiki ne, kuma na tabbata abin nan da ke hana ruwa gudu ba daga sararin samaniya aka turo shi ba, yana nan tattare mu da ’yan Najeriya, mu ne matsalar kanmu da kanmu, ina kuma jin wannan shi ne sirrin gane matsalolinmu da magance su.
kila wasu su tambaya to shin Buhari bai san da wadannan matsalolin ba ne koko dai ya hau mulkin ido rufe ne? Ga duk wanda ya karancin tsare-tsaren Jam’iyyar APC kafin zaben shekarar da ta wuce ya san an san da matsalolin Najeriya, kila yadda za a shawo kan wasu daga ciki ne ba a yi tanadin kwarai ba, ba kuma wani abu ya jawo haka ba sai domin an shiga an iske dankalin shugabancin kasar ashe tuni ya yi sankara, gyaran irin wannan dankali kuwa, barna yakan zamo a wasu lokuta. Cire sankarar dankalin shugabanci irin wannan zai iya kaiwa a ga ana neman rasa ran (kasar) baki daya, kamar yadda muke fama a yau. Amma wannan na nufin cewa ba mafita? Akwai mafita!
Sai dai kamar kullum ni ba mafitar da Buhari zai samar ta fi damuna ba, domin kuwa na san cewa ko ba-dade-ko-ba-jima za a kai karshen wannan darga, sai dai lokacin da za a dauka ba mai iya cewa ga shi. Ma’ana ba mai iya cewa ga ranar da karancin man fetur zai kau. Mu dubi alkawurran da aka yi ta yi game da wannan matsalar zuwa yau, ina aka ga hasken? Ko da karamin Minista Kachikwu ya ce za a kawo karshen matsalar man fetur nan da watan Mayu na wannan shekara, murmushi na yi da murna, amma a cikin zuciyata na san akwai jan aiki kafin a kai ga tudun mun tsira. Me ya sa? Ba wani abu ya sa haka sai ganin akwai tarkuna da dama da mu ’yan Najeriya muka dana da ke hana wulgawa. Akwai cikinmu ’yan Najeriyar da ke sa kullum ake tufka da warwara, domin su inganta harkar lamurran man fetur, ba zai musu alfanu ba, za su kuma yi duk iya yin su da su da iyayen gijinsu su ga ba a kawo karshen wannan matsala ba. Suna nan jibge, su ne kuma matsalarmu, ba Buhari ba. A sani ko da wani muka sake zaba da su zai dinga darga, in ba a yi sa’a ba, in bai da karfin hali irin na Buhari, sai sun ga bayansa da gwamnatinsa da ma kasa baki daya. Ba su da imani ko tausayi.
Haka abin yake a fagen gyara tattalin arziki da noma da saye da sayarwa da makamantan haka. Ke nan aiki ne ja, ba wai kawai na Buhari shi da gwamnatinsa ba, mu duka ’yan Najeriya. Kamar yadda na sha fada Buhari ba shi ne ya kashe zomon ba, rataya aka ba shi.
Wa ke nan ya kashe zomon, kuma yaya wanda aka ba rataya zai dawo masa da ransa? Mu sani mu ’yan Najeriya mu ne muka kashe zomon muka rataya wa Buhari, sannan kuma muke ta kwarmato!
Yaya hakan ya faru? Shin su wa ke fashi da makami? Su wa ke tsare hanya suna fizge da kwace da sane ko kuma masu tukin ganganci a bisa hanyoyin kasar nan? Ina masu yin karuwanci da daudanci da masu yin ludu da madigo, su kuma su wane ne? Cewa nake ’yan Najeriya ne! Wa muke jira ya zo ya gyara wadannan mugayen dabi’u da halaye? Ba dai Buhari ba! Idan ba Buhari muke jira ba ke nan mun san inda ya dace mu gyara, mun kuma san cewa abin da muke yi ba daidai ba ne, muna dai jiran Buhari ya gama da manyan matsalolin Najeriya, sai ya dawo ya gyara wadannan su ma! Ni kuwa sai na ga cewa mun sa riga baibai idan wannan shi ne tunaninmu. Me ya sa haka? Idan har Buhari na ta fama dodannin man fetur da tattalin arziki kasa, sa’annan  mu muna nan yin abin da muke yi na lalaci da barna da almundahana da sauran ayyukan assha, to da alama mun shiga motar canjin da matacciyar taya. Kamar yadda na sha fada ne, ba laifi  in muka nemi a kawo canji a cikin kasar nan saboda canji muka zaba. Ba laifi ba ne in mun saka a zukatanmu cewa nan da ’yan watanni za a yi ruwan saman canji a cikin kasar nan, saboda haka mu za mu ci gaba da halin batunci da barna har sai canjin da muke hankoro ya zo! Idan har muna son canji na hakika ya tabbata, to mu yi namu kokarin a lokacin da Buhari ke nasa, ba wai mu tsaya muna ta kwakwa da kwakwazo ba, alhali kashi 7 cikin 10 na canjin mu ne za mu kawo shi ba Buhari ba. Me ya kamata mu yi ke nan? Mu fara dabbaka canji daga yau, mu zama mu ne sinadaran canjin; mu kasance canjin da Buhari zai zo da shi, ya iske mu bisa torokon da tsunamin canza al’amurran namu rayuwar ko yaya.
Me za mu iya yi domin ganin haka ya tabbata? Akwai abubuwa da dama. Maimakon mu tsaya muna ta faman bata miyan baki da cewa ‘Buhari canji ko-da-gora’ kamata ya yi mu bar sana’ar fashi da makami ko sata ko sane ko fizge ko wani abu makamancin haka. Idan muna son canji, to mu bar tukin ganganci a bisa titi, shi ma direban bas ko tasi ko mai motar kashin kansa da ke ajiye mota ba bisa ka’ida ba a kan titi, kamata ya canza wannan rayuwa tasa, sai mu ga canji. Mu daina karuwanci da daudanci da ludu da madigo za mu ga canji. Su kuwa ma’aikatan gwamnati abin da muke so mu ji daga wurinsu shi ne daga yau sun bar jan kaya, sun bar cin hanci da almundahana da latti zuwa wurin aiki da hada baki da ’yan kwangila domin zurmuke.
Haka malamanmu na addini su wa’azantar bisa turbar canji, su daina ci-da-ceto da neman tara abin duniya ba ji ba gani, mu ga in canji bai samu ba. Haka su ma talakawa da ke can karkara, canji zai samu ne kurum in sun bar magudi da lalata da lalaci da duk wani abu da Buhari ke yaki da shi.
Idan mun yi haka, ni da kai da ke da shi da ku, to, ba wata burga da canjin Buhari zai yi mana balle a ce ya yi mana barazana. A daidai wannan lokacin nan canjin Buhari zai zama dole. Amma wai shin za mu iya?
Mun kammala