Buhari da APC ne matsalar Najeriya – Yanleman
Aminiya: Me ka ke ganin ya haddasa matsalar yunwa da fatara a Najeriya? Yanleman: Matsalar Najeriya Shugaba Buhari da APC ne, domin sun shigowa ‘yan Najeriya da baragurbi cikin tafiyar ta gwamnatin kasar nan, shi ne yasa jama a suka dawo daga rakiyar gwamnatin, ba don komai ba saboda wadancan bata gari sun lalata tafiyar […]
Aminiya: Me ka ke ganin ya haddasa matsalar yunwa da fatara a Najeriya?
Yanleman: Matsalar Najeriya Shugaba Buhari da APC ne, domin sun shigowa ‘yan Najeriya da baragurbi cikin tafiyar ta gwamnatin kasar nan, shi ne yasa jama a suka dawo daga rakiyar gwamnatin, ba don komai ba saboda wadancan bata gari sun lalata tafiyar gwamnatin APC baki daya. Zuwan canjin gwamnatin a Najeriya da talakawa suke bukata ya zo da matsala, domin ba canjin da suke zato suka samu ba. Maimakon ma a samu sauki, matsalolin karuwa suka yi, babu harkokin ilimi, ba ruwan sha, ba tsaro, ba hanyoyin mota masu kyau, kusan kashi 90 na manyan hanyoyin kasar nan a lalace suke, sannan uwa uba matsalolin rayuwa sun ta’azzara ga talakawa, lamarin da yasa jama’a da dama suka dawo daga rakiyar APC da Buharin shi kansa, domin ba ta fitar da su daga kuncin rayuwa ba, sai ma kara jefa su da ta yi.
Aminiya: Ba ka ganin rashin lafiyar da ya samu Shugaba Buhari ne ke kawo tsaiko ga cigaba?
Yanleman: Gaskiya ne, da yana da lafiya za a iya samun gagarumin canjin da talakawa suke tsammani daga gare shi da kuma gwamnatinsa, amma rashin lafiyar ta haifar da koma baya a cikin tafiyar. Ni dai fatana Allah Ya baiwa Janar Buhari lafiya ya dawo Najeriya ya cigaba da jagorancin kasar nan, Allah Ya ba shi ikon magance matsalolin Najeriya. Domin ni a iya sanina a Najeriya tun da aka fara siyasa ba a taba yin zaben da ya yi kyau irin na 2015 ba, saboda jama’a sun rungumi sauyi a duk fadin Najeriya, talakawa kowa ya kosa a sami zaman lafiya, hakan ce tasa guguwar Buhari ta sa kowa ya bar PDP aka yi mata raga-raga a zaben 2015.
Sai dai kuma yanzu saboda bakar wahala da jama a suke fuskanta musamman talakawa, an fara watsi da jam’iyyar musamman a dadai wannan da ake fuskantar zaben 2019. Domin zai iya zama barazana ba ma ga Buhari kawai ba, ga dukkan dan siyasa dake kwadayin mulkin Najeriya, muddin baka da kyakkyawar alaka da jama’a, to kada ma ya ce zai tsaya takara, saboda kan talakawan Najeriya ya waye, musamman wadanda suka shiga rigar Buhari sun kauracewa talakawan da suka zabe su, sun kauracewa kauyukansu.
Aminiya: Me zaka ce kan dokar da majalissar tarayya ke son yi na baiwa dan siyasa damar takarar kai-da-halinka?
Yanleman: Wannan abu ne mai kyau, wanda zai baiwa dan takara damar ya sami ikon tsayawa takara ba tare da wata jam’iyya ba. Yin hakan zai magance matsalar siyasar uban gida, jama’a su na da damar tsayar da wadda suke so koda ba shi da jam’iyya, domin yanzu talakawa sun gane mutum ake zaba ba jam’iyya ba.