Buhari da El-Rufai ba su halarci babban taron APC ba
Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa tsohon shugaban bai samu katin gayyata a kan lokaci ba.

Jam’iyyar APC mai mulki, ta gudanar da babban taronta na ƙasa a Abuja, wanda ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar daban-daban.
Duk da kasancewar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima a waje taron, wasu manyan shugabannin jam’iyyar ba su halarci taron ba.
- Ƙungiya ta raba wa marayu da mabuƙata kayan makaranta a Kano
- Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa
Daga cikin waɗanda ba su halarci taron ba akwai tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, da tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi.
Dalilin Rashin Halartar Buhari
Dangane da dalilin da ya sa Buhari bai samu halartar taron ba, tsohon mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa tsohon shugaban bai samu katin gayyata a kan lokaci ba.
“Taron masu ruwa da tsaki ne, wanda ya kamata Buhari ya halarta. Amma an aike masa da gayyatar taron ne a ranar Litinin, sai dai bai samu wasiƙar ba sai ranar Talata da rana.
“A wannan lokacin, ba zai iya barin Daura ya tafi Abuja don halarta ba, ko da kuwa yana da jirginsa na musamman.”
Duk da hakan, Garba Shehu ya jaddada cewa Buhari har yanzu cikakken ɗan jam’iyyar APC ne kuma zuciyarsa tana tare da ita.
Dalilin Rashin Halartar El-Rufai da Amaechi
Babu cikakken bayani game da dalilin da ya sa Malam Nasir El-Rufai bai halarci taron ba.
Sai dai a baya, tsohon gwamnan na Kaduna ya sha bayyana rashin jin daɗinsa game da jagorancin jam’iyyar, inda zargi cewa ta sauka daga aƙidar da aka kafa ta.
Duk da haka, ya nanata cewar har yanzu shi cikakken ɗan jam’iyyar.
Shi ma Rotimi Amaechi bai bayyana dalilin rashin halartarsa ba.
A kwanakin baya dai, tsohon gwamnan na Ribas ya daina yawan magana a fili.
A wata hira da ya yi da BBC, ya ce: “Idan akwai abu guda ɗaya da na koya daga Shugaba Buhari, shi ne rage yawan surutu.
“Domin ya taba fada min cewa ‘Amaechi, ba don abinci kawai aka yi ciki ba.’“
Manyan Jiga-Jigan da Suka Halarci Taron
Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai na jihohin Edo, Benuwe, Ondo, Ekiti, Kaduna, Jigawa, Nasarawa, Yobe, Nejs, Legas, Kogi, Ogun, da Imo.
Mataimakin gwamnan Ebonyi da wasu tsofaffin gwamnoni daga Kogi, Kebbi, Neja, Zamfara, da Filato su ma sun halarci taron.
Duk da rashin halartar wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar, babban taron ya gudana kamar yadda aka tsara.