Buhari da Jonathan: Kar-ta-san-kar ce

Hausawa kan ce karshen tika-tika-tik idan har wani al’amari ko zarafi ya kawo karshe. Zabbukan firfitar da gwanaye don mukaman jam’iyyun siyasa daban-daban wadanda aka faro su gadan-gadan sun kawo karshe, wasu sun samu nasara, wasu kuma an yi galba bisansu. Jama’a sun fi zakuwa kan don ganin yadda babban zaben tantance gwanayen da za […]

Buhari da Jonathan: Kar-ta-san-kar ce
Buhari da Jonathan: Kar-ta-san-kar ce

Hausawa kan ce karshen tika-tika-tik idan har wani al’amari ko zarafi ya kawo karshe. Zabbukan firfitar da gwanaye don mukaman jam’iyyun siyasa daban-daban wadanda aka faro su gadan-gadan sun kawo karshe, wasu sun samu nasara, wasu kuma an yi galba bisansu. Jama’a sun fi zakuwa kan don ganin yadda babban zaben tantance gwanayen da za su riki tutocin jam’iyyunsu a zaben shugaban kasa da za a yi a watan Fabrairu zai kaya, ganin cewa mutane sun kosa a samu canji mai ma’ana a dukkan harkokin mulki da na siyasa a kasar nan. Dangane da haka ne hankalin jama’a ya fi raja’a akan manyan jam’iyyu guda: ta PDP mai jan ragamar gwamnati da kuma ta jam’iyyar APC, babbar ‘yar adawa. 

Tun kafin akai ga babban zaben fitar da gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP shugabanninta sun rigaya sun tsayar da Shugaban kasa mai ci a yanzu dangane da haka, suka kuma bi suka kakkare, suka kan-kange dukkan hanyoyin da wasu za su bi don ja da shi, kuma ko da aka zo yin taron shi kakai, kwallin-kwal kinsa ne ya tsaya takarar fitar da gwanin. A waccan jam’iyyar adawar kuwa an samu wasu guda biyar da suka jajirce sai sun fafata da tsohon shugaban kasa, Janar Muhammadu Buhari, wanda zai nemi a tsayar da shi takarar a karo na huku duk kuwa da godon da aka sha yi da su don hakure masa amma suka kekasa kasa, suka ki.
To da ma an ce akan yi karo tsakanin kwai da dutse ko da sau guda ne kuwa, an kuma yi karon, kowa ya san matsayinsa. Dangane da haka ne Janar Muhammadu Buhari ya samu kuri’u masu rinjayen gaske, wadanda suka ba shi damar fafatawa da Shugaba Goodluck Jonathan a zaben watan Fabrairu mai zuwa. Jama’a da yawa sun yi murna da haka ganin cewa sabuwar jam’iyyar APC wacce wasu jam’iyyu uku suna narke, sa’annan kuma suka dunkule don samar da ita, ta kasance kashin-bugun-kashi, ko kuma a ce dutsen-fashin-tama, domin kuwa ita ce ake ganin za ta iya karya wa PDP tsinken tsire a idanu.
Saboda haka nan ana iya cewa za a yi gaba-da gaba ne tsakanin madambata guda biyu, kuma kar ta san kar ce, domin sun taba karawa, kowa ya san laggon kisan kowa. An ce Jonathan ya samu nasara akan Janar Buhari, wanda ya garzaya kotu don a share masa hawayen kukansa game da zargin cewa an yi munakisa da zamba wajen bayyana sakamakon zaben. Duk da cewa an kayar da Buhari a kotun koli, ya amince da hukuncin kotun, amma sai dai bai hakura ba, ya ci gaba da dagewa don daukar fansa. Bisa ga dukkan alamu kuma da gaske Janar Buhari ke yi, domin da karfinsa ya fito a wannan karon don ramuwar gayya idan ya yi kayen da zai sa a ji zafin gayyar da ya zo da ita.
Babu shakka jama’a sun gaji da lusarancin Shugaba Jonathan, wanda gwamnatinsa ta kasa tabuka wani aikin alheri illa sakacin da ya wanzar da matsanancin yanayin rashin tsaro da zubar da jinin da kowa da kowa ke Allah-wadai da shi. Rashawa da cin hanci sun tsananta, kuma hakan ya gurgunta dukkan ayyukan gwamnati, ya kuma zaizaye mutuncinta. Hukumomin gwamnati wadanda jama’a suka dogara akai, don habaka harkokin kasuwancinsu da kuma zamantakewarsu sun sukurkuce, sun kuma kaikaice, sun kasa biyan wata kwakkwarar bukata. A cikin shekaru shida na mulkin Jonathan jama’a sai kuka suke ta shirgawa saboda halin matsin da suke ciki, a kullum suna cewa gara bara da bana saboda rashin wadata da fitintinun da ke hana su more girkin rayuwa.
Wannan ne ya sa aka mayar da alkiblar siyasar kasar nan ga jam’iyyar APC da kuma kan takararta na shugaban kasa, Janar Muhamadu Buhari wanda talakawa suka yi amma shi ne kan-kwarai wanda zai kai kasar nan gaci, ya magance mata kimbin matsalolin da jam’iyyar PDP ta haddasa mata. A yanzu an rigaya an fahimci kowane ne Janar Buhari, an kuma gane irin kazafi da bakin fentin da aka yi ta shafa masa don a bakanta shi da sunan addini. An ce shi ne ubangidan ‘yan ta’adda dake yankin Arewa-maso-gabas don haka ya ki ya hana su kisan jama’a, ya kuma fito fili ya karyata haka, ya muzanta ‘yan ta’addan sa’annan kuma ya nisanta kansa da su amma duk da haka nan bai tsira ba, ana ta yi masa b-ta-da-kulli wai idan ya zama shugaban kasa zai mayar da kowa Musulmi. Anya kuwa, haka na iya faruwa?
To yanzu ba abin da ya rage sai a ba Janar Buhari cikakken goyo baya, kudu da arewa, yamma da gabas don ya samu gagarumar nasarar da za ta kora shi bisa mulki, ya kuma samu ‘yan majalisun tarayya masu yawan gaske ta yadda zai ji dakin aiwatar da kyawawan manufofin da ya tsara don inganta rayuwar talakawa da raya kasa. Hakan zai sa ya samu sukunin cika alkawarinsa na magance rashin tsaron da ya tayar da zaune tsaye. Wajibi ne kuma a mayar da hankali ga dukkan abubuwan da za su iya kawo cikas dangane da haka, musamman kokarin da ake yi don amfani da jami’an tsaro birjik a ranakun zabe da kuma halayyar jami’an zabe yayin tattara takardun zabe da aka jejjefa da kuma yadda za a sarrafa su don a kawar da dukkan munakisar da makiya zaman lafiya za su iya hadasawa.
Baicin haka nan kuma sai a yi taka-tsantsan da mutanen yankin Kudu-maso-Yamma, wadanda za su iya cin amana, su sayar da mutuncin jam’iyya da kuma nasu don biyar bukatar bakar aniyarsu. A halin yanzu an yi yunwa, halin wasu ya fara fiyowa fili, bai kamata ba kuma a yi kasake, a bari su yi wa jam’iyya da kan takararta sakiyar da ba ruwa. Ga dai alheri nan ya danno, to sai a yi niyyar taryensa da hannu bibbiyu don a ci gajiyar fa’idojin da za su biyo bayansa.