Buhari da kansa ya ce ba zai yi takara ba a zaben 2019-Jummai Alhassan
Ministan Harkokin Mata, Hajiya Jummai Alhassan, ta ce Shugaba Buhari da kansa ya ce ba zai yi takara karo na biyu ba a zaben 2019. Hajiya Jummai ta yi furucin ne a wata tattaunawa da ta yi da gidan rediyon BBC a yau. “Daga shekarar 2015 a lokacin da aka matsa masa ya tsaya takara, […]

Ministan Harkokin Mata, Hajiya Jummai Alhassan, ta ce Shugaba Buhari da kansa ya ce ba zai yi takara karo na biyu ba a zaben 2019.
Hajiya Jummai ta yi furucin ne a wata tattaunawa da ta yi da gidan rediyon BBC a yau.
“Daga shekarar 2015 a lokacin da aka matsa masa ya tsaya takara, a lokacin ya ce sau daya zai yi mulki, shekara hudu kawai zai yi kuma har yanzu babu wanda zai ce Baba ya gaya masa zai sake tsayawa takara”. Inji shi.
Ta bayyana cewa akwai Ministoci da dama da ba za su mara wa Buhari baya ba idan ya ce zai sake tsayawa takara a zaben 2019.
Ta dage a kan cewa ta fito fili ta bayyana goyon bayanta ga Atiku saboda ita ba butulu ba ce.
Ta bayyana cewa akwai Ministocin da ke goyon bayan ’yan takarar shugaban kasa daban-daban.
Ta dage a kan cewa akwai Ministocin da ke ikirarin cewa har yanzu PDP suke goyon baya.