Buhari da majalisa ku ja hankulan gwamnonin Benuwai da Taraba kan dokar kiwo – Sheikh Jingir
Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah na kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga shugaban kasa da majalisun tarayya da manyan kasa da shugabannin addini, su jawo hankulan gwamnonin jihohin Benuwai da Taraba kan illolin dokar hana kiwo da suka kafa a jihohinsu. Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir […]
Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah na kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga shugaban kasa da majalisun tarayya da manyan kasa da shugabannin addini, su jawo hankulan gwamnonin jihohin Benuwai da Taraba kan illolin dokar hana kiwo da suka kafa a jihohinsu.
Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron bude sabuwar sakatariyar kungiyar Izala ta kasa, da aka gudanar a garin Jos a karshen makon da ya gabata.
Ya ce da manomi da makiyayi dan juma’a ne da dan jummai, don haka ya ce rikici-rikicen da ke faruwa tsakanin fulani makiyaya da manoma a jihohin Benuwai da Taraba da sauran wasu jihohin Nijeriya abin bakin ciki ne. Kuma barazana ce ga Nijeriya baki daya.
Ya ce kafa dokar hana kiwo da gwamnonin jihohin Benuwai da Taraba suka yi a jihohinsu ne ya dada yaduwar wadannan rikice-rikice. “Tun a lokacin da na ji labarin cewa za a kafa wannan doka ta hana kiwo a jihohin Benuwai da Taraba. Na fito na yi kira ga gwamnatin tarayya da majalisun tarayya da gwamnatocin jihohin kasar nan, kan su shiga tsakani don a dakatar da kafa wannan doka, domin kafa wannan doka za ta iya kawo matsala ga tsaron kasar nan. Don haka ina kara kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari da ‘yan majalisar tarayya da gwamnoni da shugabannin addini da sauran manyan kasar nan, su jawo hankulan gwamnonin jihohin Benuwai da Taraba su janye dokar hana kiwo da suka kafa a jihohinsu, domin a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali”.
Da ya juya ga sabuwar sakatariyar kungiyar da aka bude, Sheikh Jingir ya yi bayanin cewa ganin irin yadda ayyukan kungiyar na yada harkokin addinin musulunci ya kankama a Najeriya da kasashen waje, ya sanya suka gina sabuwar sakatariyar da ta kunshi ofisoshi daban-daban da zasu rika amfani da su wajen gudanar da ayyukan kungiyar.
A nasa jawabin gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya mika godiyarsa ga al’ummar Jos kan goyan bayan da suka ba shi, a lokacin zaben da ya gabata da kuma zaman lafiyar da aka samu a garin Jos da jihar Filato baki daya. Ya ce ya sani wannan zaman lafiya an same shi ne sakamakon goyan baya da irin addu’o’in da al’ummar musulmi suke yi.
Gwamnan wanda kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Ahmad Muhammad Nazifi ya wakilta, ya roki a cigaba da addu’a domin zaman lafiyar da aka samu a jihar ya dore.
Shima a nasa jawabin gwamnan jihar Bauchi, Barista MA Abubakar ya taya Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir murna kan gina wannan sabuwar sakatariya da kungiyar ta yi. Ya ce wannan aiki da kungiyar ta yi, ya zo daidai lokacin da ake bukatar a gyara tunanin matasan Najeriya.
Gwamnan wanda sakataren dindindin a ma’aikatar harkokin addinin musulunci ta jihar, Ustaz Muhammad Auwal Ibrahim ya wakilta ya yi fatan Sheikh Sani Yahya Jingir, zai kara zage damtse kan abubuwan da yake yi, na taimakawa wannan kasa wajen tsayar da matasa kan hanya.