Buhari da Muslim
Babi na Tamanin da Tara: Abin da aka ambata game da sulken yakin da Annabi (SAW) ke sanyawa da bayanin taguwar fita yaki. Da fadar Annabi (SAW) cewa: “Amma Khalid ya yi tattalin sulkensa ne domin daukaka kalmar Allah.” 600. An karbo daga Muhammad dan Musanna ya ce: “Abdulwahab ya ba mu labari ya ce, […]
Babi na Tamanin da Tara:
Abin da aka ambata game da sulken yakin da Annabi (SAW) ke sanyawa da bayanin taguwar fita yaki. Da fadar Annabi (SAW) cewa: “Amma Khalid ya yi tattalin sulkensa ne domin daukaka kalmar Allah.”
600. An karbo daga Muhammad dan Musanna ya ce: “Abdulwahab ya ba mu labari ya ce, Khalid ya ba mu labari daga Ikramatu daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce, lokacin da ke kubah: “Ya Allah! Ina shaidawa da Kai bisa cikawa da alkawarinKa da wa’adinKa. Ya Allah! Idan Ka so (halaka wadanda suka yi imani) ba a sake bauta maKa a bayan yau.” Sai Abubakar ya yi riko da hannunsa yana mai cewa: “Ya Manzon Allah! Haka ya isar maka dalili bisa ga abin da kake rokon Allah.” Lokacin Annabi (SAW) yana sanye da rigar sulken yaki. Sai ya fita yana cewa bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Da sannu za a karya taron jama’ar (mayakan abokan gaba) kuma lallai za su juya baya domin gudu. A’a Sa’a ita ce lokacin wa’adinsu. Kuma Sa’ar ta fi tsananin masifa, kuma tafi daci. (k:54:45-56).” Khalid ya ba mu labari cewa wannan ya faru ne a Badar.
601. An karbo daga Muhammad dan Kasir ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga A’amash daga Ibrahim daga Aswad daga A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya bar duniya, alhali sulken yakinsa yana wurin wani Bayahude jingina Sa’i talatin na sha’ir.” Ya’ala ya ce: “A’amash ya ba mu labari cewa: “Sulken na bakin karfe ne.”
602. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Wuhaibu ya ba mu labari ya ce, dawus ya ba mu labari daga Babansa daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Misalin marowaci da mai sadaka. Kamar misalin mutum biyu ne da suke sanye da alkyabba (sulke) na bakin karfe. Na daure da hannayensu da kafadarsu zuwa kasa duk lokacin da mai sadaka ya yi nufin sadaka sai taguwarsa ta buda masa don gabatar da sadaka. Haka kuma duk lokacin da marowaci yayi nufin rowa da sadakarsa sai ta kara matse shi bisa dukan jikinsa ta hada hannunsa da kafadarsa ta zamo masa kukumi.” Kuma ya ji Annabi (SAW) yana cewa: “Duk lokacin da ya yi kokarin ya buda ba za ta budu ba.”
Babi na Casa’in: Sanya (daura) alkyabba cikin tafiya ko yaki:
603. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Abdulwalid ya ba mu labari ya ce, A’mashi ya ba mu labari daga Abu Duhah daga Masruk ya ce: “Mughira dan Shu’aba ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya fita zuwa ga bukatarsa na bayan gida, sa’an nan ya komo na fuskance shi da ruwa ya yi alwala. Lokacin yana sanye da wata alkyabba ta Siriya, ya kurkure baki ya sheka ruwa ya wanke fuskarsa. Sai ya yi kokarin fitar da hannunsa daga hannun alkyabbarsa, kuma sun kasance masu kunci. Sai ya fitar da su ta karkashi ya wanke su ya yi shafa a kansa ya yi shafa bisa huffinsa.”
Babi na Casa’in da daya: Sanya tufafin hariri cikin tafiyar yaki:
604. An karbo daga Ahmad dan Mikdam ya ce: “Khalid dan Haris ya ba mu labari ya ce Sa’id ya ba mu labari daga kattada cewa: “Lallai Anas ya ba su labari cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya yi rangwame ga Abdurrahman dan Auf da Zubair game da sanya tufafi na hariri saboda ciwon da ke fatar jikinsu.”
605. An karbo daga Abulwalid ya ce: “Hammam ya ba mu labari daga kattada daga Anas.
606. An karbo daga Muhammad dan Sinan ya ce: “Hammam ya ba mu labari daga kattada daga Anas (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Abdurrahman dan Auf da Zubair sun kai kukan citar da ke damunsu ga Annabi (SAW) saboda cizon kwarkwata. Sai Annabi (SAW) ya yi musu rangwame ga sanya tufafin hariri. Sai na gan shi a jikinsu a wani yaki.”