Buhari da Muslim 003
Babi na Biyar: Hadin gwiwa wajen kasuwanci ko kaya bisa daidaita farashi:211. An karbo daga Imran dan Maisarata ya ce: “Abdulwaris ya ba mu labari ya ce, Ayyub ya ba mu labari ya ce daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya yafe rabonsa […]
Babi na Biyar: Hadin gwiwa wajen kasuwanci ko kaya bisa daidaita farashi:
211. An karbo daga Imran dan Maisarata ya ce: “Abdulwaris ya ba mu labari ya ce, Ayyub ya ba mu labari ya ce daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya yafe rabonsa daga bawan da suka yi tarayya da wani kuma yana iya biyan sauran abin da ya rage daga bawan bisa daidaito shi ne mai ’yanci. Idan ba haka ba to ya dai ’yanta abin da ya ’yanta.” Ayyuba mai ruwaya ya ce: “Ban sani ba game da maganar cewa: “Ya ’yanta abin da ’yanta,” ko magana ce daga Nafi’u ko kuwa daga Annabi (SAW).”
212. An karbo daga Bishiru dan Muhammad ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Sa’id dan Abu Arubatu daga kattada daga Nadar dan Anas daga Bashir dan Nahik daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya ’yanta wani kaso daga bawan da suke tarayya da wani, to lallai shi ke da hakkin biyan sauran kudin don cikar ’yancin bawa. Idan ba zai iya ba, to sai a kayyade kudin da ke kan bawa domin ya yi kokarin biya da kansa ba tare da tsananta masa (bawan) ba.”
Babi na Shida: Shin ana iya yin kuri’a domin rabo?:
213. An karbo daga Abu Nu’aim ya ce: “Zakariya ya ba mu labari ya ce, na ji Amir yana cewa: “Na ji Nu’aman dan Bashir (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Daga Annabi (SAW) ya ce, “Misalin wanda yake tsayuwa bisa dokokin Allah da mai aukawa cikinsu, kamar misalin mutane ne da suka yi kuri’a wajen hawa jirgin ruwa, wasu suka zabi zama bisansa wasu kuma karakashinsa. Sai wadanda ke karkashinsa idan za su nemi (bukaci) ruwan sha, sai su tafi zuwa ga wadanda suke bisansu (samansu, sai haka ya zama musu husuma). Sai suka ce, “Bari mu yi wani huji daga karkashin jirgin don kada mu rika cutar da wadanda ke bisanmu. Idan wadanda ke bisa suka kyale (bari) wadanda ke karkashi bisa ga abin da suka yi nufi (na yin huji ga jirgin) sai su halaka gaba daya. Idan kuwa suka yi riko da hannayensu nan da can kowane bangare zai tsira (kubuta) daga hallaka.”
Babi na Bakwai: Tarayyar marayu da masu gado cikin dukiyan gado:
214. An karbo daga Uwais ya ce: “Ibrahim dan Sa’ad ya ba mu labari daga Salih daga dan Shihab ya ce, “Urwatu ya ba ni labari cewa, lallai shi ya tambayi A’isha (Allah Ya yarda da ita). Laisu ya ce, Yunus ya ba ni labari daga dan Shihab ya ce, “Urwatu dan Zubair ya ba ni labari cewa: Lallai shi ya tambayi A’isha (Allah Ya yarda da ita), game da fadar Allah Madaukaki cewa: “Idan kun ji tsoron ba za ku iya yin adalci ba game da ’yan mata marayu, ba, to! Ku auri abin da ya yi muku dadi daga (wadansu) mata, bibbiyu ko uku-uku ko hurhudu…har zuwa karshen aya.” (k:4:3). Sai (A’isha) ta ce, ya dan yar uwata! Wannan hukuncin marainiya ce, wadda take karkashin tsaro (kulawar) waliyinta tana tarayya da shi cikin dukiyarsa sai dukiyarta ya ba shi sha’awa da kyawonta. Sai shi waliyinta ya yi nufin aurenta ba tare da ya yi adalci cikin biyanta sadakinta ba, wato ba zai ba ta kamar yadda waninsa zai bayar gare ta ba. Sai aka hane su (waliyyai) su aure su face in har za su yi musu adalci kuma za su kai matukar iyakar biyan sadakin. Don haka sai aka umarce su da auren abin da ya yi musu dadi daga wadansu matan da (da ba marayu ba).” Urwatu ya ce, “A’isha (RA) ta ce, “Sa’an nan sai mutane suka rika neman fatawar Manzon Allah (SAW), bayan wannan aya sai Allah Ya saukar da cewa: “Suna tambayarka game da mata (marayu) har zuwa fadarSa cewa: “Kuna kwadayin aurensu….” abin da Allah Ya ambata cewa: “Ana karanta muku cikin littafi ita ce ayar farko wadda Ya ce a cikinta: “Idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba cikin yara mata marayu, to! Ku auri abin da ya yi muku dadI daga mata….” A’isha (RA) ta ce, bisa fadarSa a cikin wata aya. Allah Ya ce: “Kuna kwadayin aurensu…” shi ne kaunar dayanku ga marainiyarsa wadda take cikin gidansa lokacin da ta kasance mai kankanen (karancin) dukiya da kyawo (ba za su yi ba). Sai aka hane su ga auren wadda suke kwadayin dukiyarta da kyawonta daga mata marayu face da adalci saboda kwadayinsu game da su (marayu).”