Buhari da Muslim 01

Babi na Saba’in da Uku: Iyakar hani game da taryar kaya: 614. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Juwairiyya ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Mun kasance muna taryar mahaya (ayari) sai mu sayi abinci daga gare su. Sai Annabi (SAW) ya hana mu […]

Buhari da Muslim 01
Buhari da Muslim 01

Babi na Saba’in da Uku: Iyakar hani game da taryar kaya:

614. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Juwairiyya ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Mun kasance muna taryar mahaya (ayari) sai mu sayi abinci daga gare su. Sai Annabi (SAW) ya hana mu game da saye har sai an isar da shi kasuwa.” Abu Abdullahi (Buhari) ya ce, “Wannan yana nufin a madaukakiyar kasuwa kamar yadda Hadisin Ubaidullahi zai bayyana shi.”
615. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya ya ba mu labari daga Ubaidullahi ya ce: “Nafi’u ya ba ni labari daga Abdullahi (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Sun kasance suna sayen kayan abinci a madaukakiyar kasuwa sai su sayar da shi a wurinsu. Sai Manzon Allah (SAW) ya hana su sayar da shi a wurinsa har sai sun kai shi masaukinsu.”

Babi na Saba’in da Hudu: Idan mutum ya yi sharadi a cikin ciniki da abin da bai halatta ba:

616. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Hisham dan Urwat daga Babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “Barirah ta zo mini ta ce, iyalaina sun rubuta mini kudin fansa bisa Ukiyya tara, cikin kowace shekara zan biya ukiyya daya, saboda haka ki taimake ni. Sai na ce, “Idan iyalanki (shugabanninki) sun yarda in biya su amma waliccinki na hannuna, zan aikata haka, sai Barirat ta tafi zuwa ga shugabanninta, ta fadi musu sai suka ki yarda. Sai ta komo daga wurinsu lokacin Manzon Allah (SAW) yana zaune. Sai ta ce, hakika ni, na bayyana wannan sharadi amma sun ki yarda face waliccin ya kasance gare su. Da Annabi (SAW) ya ji, A’isha ta ba da labari ga Annabi sai ya ce: “Ki karbe ta ki yi musu sharadin walicci domin walicci na ga wanda ya ’yanta ne. Sai A’isha ta aikata haka, sa’an nan Manzon Allah ya tsayu cikin mutane domin ya yi musu huduba. Ya gode wa Allah ya kuma yi maSa yabo, sa’anan ya ce: “Bayan haka, me ya samu wasu jama’a da suke yin sharadin da babu shi cikin Littafin Allah? Babu wani sharadin da za a yi wanda babu shi cikin Littafin Allah face batacce ne, koda kuwa sharuda dari aka yi. Hukuncin Allah ya fi cancanta, kuma sharadin Allah ya fi aminci, domin walicci yana ga wanda ya ’yanta.”

617. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai A’isha Uwar Muminai ta yi nufin ta sayi wata baiwa (kuyanga) don ta ’yanta ta, sai mutanenta (masu ita baiwar) suka ce, “Za mu sayar miki da ita, bisa waliccinta yana hannunmu.” Sai (A’isha) ta ambaci haka ga Annabi (SAW). Sai ya ce: “Wannan ba zai hana miki sayenta ba, domin hakika walicci yana ga wanda ya ’yanta.”

Babi na Saba’in da Biyar: Cinikin dabino da dabino:
618. An karbo daga Abul Walid ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga dan Shihab daga Malik dan Ausu ya ji dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce, daga Annabi (SAW) ya ce: “Cinikin alkama da alkama akwai riba cikinsu face hannu da hannu, haka sha’iri da sha’iri, akwai riba a cikinsu face hannu da hannu, haka cinikin dabino da dabino akwai riba cikinsu face hannu da hannu.”