Buhari da Muslim 02
200. An karbo daga Abdullahi dan Yazid ya ce: “Sa’id dan Abu Ayyub ya ba mu labari ya ce, Abu Aswad ya ba ni labari daga Ikramat daga Abdullahi dan Amri (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Na ji Annabi (SAW) yana cewa: “Wanda aka kashe saboda dukiyarsa ya yi shahada.” Babi na Talatin […]
200. An karbo daga Abdullahi dan Yazid ya ce: “Sa’id dan Abu Ayyub ya ba mu labari ya ce, Abu Aswad ya ba ni labari daga Ikramat daga Abdullahi dan Amri (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Na ji Annabi (SAW) yana cewa: “Wanda aka kashe saboda dukiyarsa ya yi shahada.”
Babi na Talatin da Biyar: Wanda ya karya akushi ko wani abu ga waninsa:
201. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya dan Sa’id ya ba mu labari daga Humaid daga Anas (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Annabi (SAW) wata rana ya kasance tare da wasu matansa, sai wata mace daga uwayen muminai ta aika mai yi mata hidima da wani akushi a cikinsa da abinci, sai daya daga cikin matan (ko baiwar) ta fadar da (akushin) daga hannunta akushin ya fashe sai (Annabi) ya karba ya hada shi, ya sanya abincin a cikinsa. Ya ce, “Ku ci, Annabi ya karbe wannan akushi har sai da suka kare ci. Ya musanya da wani akushi mai kyau, ya rike fasasshen.”
Babi na Talatin da Shida: Idan mutum ya rusa (ture) katanga to lallai ya gina misalinsa.
202. An karbo daga Muslim dan Ibrahim ya ce: “Jarir dan Hazim ya ba mu labari daga Muhammad dan Sirin daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Wani mutum daga cikin kabilar Yahudawa wanda ake ce masa Juraij ya kasance yana Sallah sai uwarsa ta zo tana kiransa, sai ya ki amsa mata. Ya ce, “A cikin ransa in amsa mata ko in yi Sallah? Sai ta sake zuwa kashi na biyu ta kira shi, sai ta ce: Ya Allah! Kada ka karbi ransa har sai ka nuna masa fuskokin mazinata (karuwai).” Juraij ya kasance a kan haka wata rana yana cikin bukkarsa (Tsangaya). Sai wata mazinaciya ta ce, ‘Sai na jarrabi (fitini) Juraij, sai ta gitta gare shi, ta yi masa magana ya ki amsa mata. Sai ta tafi ga wani makiyayi sai ta ci nasara a kansa ya sadu da ita, ta yi ciki da ta haifi wani yaro sai ta ce: “Cikin Juraiju ne.” Sai jama’a suka ta tafi gare shi, suka karya bukkarsa suka sauko da shi suka zazzage shi, sai ya yi alwala ya yi Sallah sa’an nan ya je ga yaron nan ya ce: “Wane ne babanka? Ya ce, “Makiyayi.” Sai jama’a suka ce, “Tunda haka ne to lallai za mu sake gina maka bukkarka da zinari (gidanka). Ya ce, “A’a, face dai da yumbu (kasa).”