Buhari da Muslim..1

BABI NA ASHIRIN dA HUdU:  Sumbantar mace ga mai azumi: 389. An karbo daga Muhammad dan Musanna ya ce: “Yahya ya ba ni labari daga Hisham ya ce, “Babana ya ba ni labari daga A’isha daga Annabi (SAW) Hawwala Sanad ya ce, “Abdullahi dan Maslamata ya ba mu labari daga Malik daga Hisham daga Babansa […]

Buhari da Muslim..1
Buhari da Muslim..1

BABI NA ASHIRIN dA HUdU: 

Sumbantar mace ga mai azumi:

389. An karbo daga Muhammad dan Musanna ya ce: “Yahya ya ba ni labari daga Hisham ya ce, “Babana ya ba ni labari daga A’isha daga Annabi (SAW) Hawwala Sanad ya ce, “Abdullahi dan Maslamata ya ba mu labari daga Malik daga Hisham daga Babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya kasance yana sumbantar wasu daga cikin matansa, alhali yana azumi, sa’an nan ta yi dariya.”

390. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya ya ba mu labari daga Hisham dan Abu Abdullahi ya ce, Yahya dan Abu Kasir ya ba mu labari daga Abu Salmata daga Zainab ’yar Ummi Salmata daga mahaifiyarta (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Wata rana ina tare da Manzon Allah (SAW) a cikin mayafi (wanda aka saka da ulu) sai na yi haila na sulale (fita) na dauki tufafin hailata, sai ya ce, “Me ya same ki? Shin kin yi haila ne? Na ce, “Na’am, sai na shiga cikin mayafi tare da shi. Kuma ita ta kasance tana wanka tare da Manzon Allah (SAW) na janaba a cikin kwarya guda. Kuma ya kasance yana sumbantarta yana azumi.”

BABI NA ASHIRIN dA BIYAR:
Wankan mai azumi saboda zafi.

dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya taba jika tufafi ya yafa a jikinsa yana azumi. Sha’abi ya shiga ruwan dumi a dakin wanka yana azumi. dan Abbas ya ce, “Babu laifi a dandana abincin tukunya, ko wani abinci.” Alhasan ya ce, “Babu laifi da kurkurar baki da sanyaya jiki saboda azumi.” dan Mas’ud ya ce, “Idan yinin azumin dayanku ya kasance yana iya wayargari na mai shafar mai da gyaran gashi.” Anas ya ce: “Ina da wani bututu (daro) da nake zama cikinsa ina azumi.” An karbo daga Annabi (SAW) cewa, lallai shi yana asiwaki (goge baki) yana azumi.” dan Umar ya ce: “Ya kasance yana goge bakinsa a farkon yini da karshensa kuma bai hadiye abin asiwakinsa.” Adda’u ya ce, “Idan mutum ya hadiye abin asiwaki ba ya karya azumi.” dan Sirin ya ce, “Babu laifi yin asiwaki (goge baki) da danyen itace.” Sai aka ce, masa: “Na da dandano,” sai ya ce, “Ruwa ma na da dandano amma kana kukurar baki da shi.” Anas da Alhasan da Ibrahim ba su ganin lafin sanya tozali ga mai azumi.”
391. An karbo daga Ahmad dan Salih ya ce: “dan Wahab ya ba mu labari ya ce, Yunus ya ba mu labari daga dan Shihab daga Urwata da Abubakar cewa A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Annabi (SAW) fajiri na riskarsa a cikin Ramadan da janaba ba na mafarki ba, sai ya yi wanka ya yi azumi.”
392. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba ni labari daga Summiyyu bawan Abubakar dan Abdurrahman dan Haris dan Hisham dan Mughirata cewa: Lallai shi ya ji Abubakar dan Abdurrahman ya ce: “Na kasance ni da Babana sai na tafi tare da shi har sai da muka shiga ga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Ina shaidawa ga Manzon Allah (SAW) yakan wayigari da janabar jima’i ba na mafarki ba. Sa’an nan yana azuminsa.” Sa’an nan muka shiga ga Ummu Salmata sai ta fadi misalin haka.