Buhari da Muslim 10
Babi na Ashirin da Uku:Zama a cikin farfajiyar gidaje da bayanin hukuncin zama cikin hanyoyi. A’isha ta ce, “Abubakar ya gina wani masallaci a cikin farfajiyar gidansa wanda yake Sallah cikinsa yana kuma karatun Alkur’ani sai matan mushirikan Makka suka rika tsayuwa tare da ’ya’yansu suna mamaki lokacin da Annabi (SAW) ya ke Makka. 185. […]
Babi na Ashirin da Uku:
Zama a cikin farfajiyar gidaje da bayanin hukuncin zama cikin hanyoyi. A’isha ta ce, “Abubakar ya gina wani masallaci a cikin farfajiyar gidansa wanda yake Sallah cikinsa yana kuma karatun Alkur’ani sai matan mushirikan Makka suka rika tsayuwa tare da ’ya’yansu suna mamaki lokacin da Annabi (SAW) ya ke Makka.
185. An karbo daga Mu’azu dan Fadalatu ya ce: “Abu Umar Hafsu dan Maisarata ya ba mu labari daga Zaid dan Aslam daga Adda’u dan Yassar daga Abu Sa’idul Khudri (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce, “Kashedinku da zama a gefen hanyoyi.” Sai (wasu sahabai) suka ce, “Ai kuwa ba mu da makawa ga haka, saboda gefen hanya ce wurin zamanmu domin hira.” Sai (Annabi) ya ce, “To idan kuka zo ga wurin zaman naku, ku bai wa hanya hakkokinta.” Suka ce, “Mene ne hakkokinta? Ya ce, “Rintse gani (ido ga mata masu wucewa) da kamewa daga cutar da mutane bisa zundensu idan sun zo wucewa da amsa sallama da umarni da kyawawan ayyuka da hani game da miygun ayyuka.”
Babi na Ashirin da Hudu: Hukuncin rijiyoyin da suke bakin hanya idan ba a cutuwa da su:
186. An karbo daga Abdullahi dan Maslamata ya ce: “Daga Malik daga Summiyya bawan Abubakar daga Abu Salih Samman daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Wata rana wani mutum na tafiya cikin hanya sai kishirwa mai tsanani ya kama shi, sai ya iske wata rijiya ya sauka ya sha sa’an nan ya fita zai tafi sai ga wani kare yana lallaga har yana cin tabo mai sanyi saboda kishirwa. Sai mutumin ya ce, “Hakika kishirwa ya kama wannan kare kamar yadda wahalar kishi ta same ni. Sai ya sauka ga rijiyar ya ciko takalmansa na fata da ruwa, ya shayar da karen. Sai Allah Ya gode masa Ya gafarta masa. Sai (Sahabai) suka ce, “Ya Manzon Allah! Shin muna samun lada cikin taimakon dabbobi? Ya ce, “Cikin dukkan dabba mai hanta mai rai akwai sakamako (lada).”
Babi na Ashirin da Biyar: Gusar da kazanta (abin cutarwa) daga kan hanya. Hammam ya ce, daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) cewa: “Kawar da (dauke) abin cuta daga hanya sadaka ce.”
Babi na Ashirin da Shida: Halaccin gina gidaje da benaye madaukaka da mai su zai rika hangen wasu gidaje, ko ku kuwa ba ya hangen gidan kowa idan gidajen akwai rufi ko babu:
187. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “dan Ulayyatu ya ba mu labari daga Zuhuri daga Urwatu daga Usama dan Zaid (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Wata rana Annabi (SAW) ya yi dubi ga wasu benayen mutanen Madina, sa’an nan ya ce, “Shin ko kuna ganin abin da nake gani? Lallai ni ina ganin wuraren fitinu a tsakanin gidajenku kamar wurin saukar ruwan sama.”