Buhari da Muslim
Babi na Takwai: Tarayyya cikin kasa (filaye) da waninsu:215. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Hisham ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Zuhuri daga Abu Salmata daga Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su) ya ce: “Abin sani dai Annabi (SAW) ya sanya kamun shufu’a (shiga […]
Babi na Takwai: Tarayyya cikin kasa (filaye) da waninsu:
215. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Hisham ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Zuhuri daga Abu Salmata daga Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su) ya ce: “Abin sani dai Annabi (SAW) ya sanya kamun shufu’a (shiga cinikin filin makwabci da makamancinsa) cikin dukkan abin da ba a raba ba. Idan iyakoki suka auka ko hanyoyi suka rarraba, to babu kamun shufu’a.” (Shufu’a, shi ne idan makwabci ya sayar da wani bangaren gidansa ga wani kafin ya sanar da makwabcinsa, to shi makwabcin yana iya warware cinikin domin ya biya saboda na da hakkin saye).
Babi na Takwas: Idan aka raba gidajen gamayya ko waninsu babu komai cikinsu ko kamun shufu’a:
216. An karbo daga Musaddad ya ce: “Abdulwahid ya ba mu labari daga Ma’amar daga Zuhuri daga Abu Salmata daga Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su) ya ce: “Annabi (SAW) ya yi hukunci da kamun shufu’a cikin dukkan abin da ba a raba ba. Idan iyakoki suka auku ciki ko hanyoyi suka rarraba to babu shufu’a.”
Babi na Tara: Tarayya cikin Zinari da Azurfa da abin da musanya ke shiga cikinsa:
217. An karbo daga Amru dan Aliyu ya ce: “Abu Asim ya ba mu labari daga Usman yana nufin dan Aswad ya ce, “Sulaiman dan Muslim ya ba mu labari ya ce, “Na tambayi Abu Minhal game da cinikin musanya hannu da hannu. Sai ya ce, “Ni ina da wani abokin tarayya (gamayya) mun sayi wani abu muka yi (musanya) hannu da hannu da kuma jinkiri. Sai Barra’u dan Azib ya zo mana muka tambaye shi sai ya ce: “Na aikata haka ni da abokinna Zaid dan Arkam muka tambayi Annabi (SAW) game da haka ya ce, “Duk abin da ya kasance hannu da hannu ku karbe shi, abin da yake bisa jinkiri (bashi) ku kyale shi.”
Babi Na Goma: Gamayya tare da kafirin amana da mushiriki ga aikin gona (noma):
218. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Juwairiyyatu dan Asma’u ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya bar wa Yahudawan Khaibara aikinta da nome gonakinta bisa sakamakon rabin abin da aka samu na amfani.”
Babi na Goma Sha daya: Rabon dukiyar ganima bisa adalci a cikinta:
219. An karbo daga kutaiba dan Sa’id ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Yazid dan Abu Habib daga Abul Khair daga Ukuba dan Amir (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya ba shi wasu tumaki yana raba su ga sahabbansa abin layya sai wata utud (karamar tunkiya) ta saura. Sai ya ambace ta ga Manzon Allah (SAW) sai ya ce: “Yi layya da shi kai.”