Buhari da Muslim
712. An karbo daga Amru dan Khalid ya ce: “Zuhair ya ba mu labari ya ce, Abu Is’hak ya ba mu labari ya ce, “Na ji Barra’u dan Azib (Allah Ya yarda da su), yana bayar da labari ya ce: “Annabi (SAW) ya nada Abdullahi dan Jubair shugaban maharba (gwanayen harbi) a Ranar Yakin Uhudu, […]
712. An karbo daga Amru dan Khalid ya ce: “Zuhair ya ba mu labari ya ce, Abu Is’hak ya ba mu labari ya ce, “Na ji Barra’u dan Azib (Allah Ya yarda da su), yana bayar da labari ya ce: “Annabi (SAW) ya nada Abdullahi dan Jubair shugaban maharba (gwanayen harbi) a Ranar Yakin Uhudu, sun kasance kamar mutum hamsin. Sai (Annabi) ya ce: “Lallai ku tsaya a matsayinku ko da kun ga an yi mana tsinke (an mamaye mu) kamar tsuntsaye na takarmu (cakkwadarmu). Har sai na aika zuwa gare ku, kuma ko kun ga mun karya (ci nasara) a kan abokan gaba da masaukansu. Kada ku bar wannan wuri har sai na aiko zuwa gare ku. Ana nan haka sai (Musulmi) suka karya su (abokan gaba). Ya ce: “Wallahi sai da na ga mata suna gudu har zobban kafafunsu suna bayyana da kwaurinsu saboda sun tattara tufafinsu wajen gudu.” Sai mutanen Abdullahi dan Jubair suka ce: “Ga ganima ta bayyana ga abokanku ku me kuke jira? Sai Abdullahi dan Jubair ya ce: “Shin kun manta ne da abin da Manzon Allah (SAW) ya fada muku? Sai suka ce, “Wallahi za mu tafi ga mutane mu samo rabonmu daga ganima. Lokacin da suka tafi gare su (don neman ganima) sai aka juyar da fuskokinsu aka karya Musulmi. A wannan lokacin ne Manzon Allah (SAW) yake kiransu a cikin karshensu babu wanda ya saura tare da Annabi (SAW) face mutum goma sha biyu, sai suka kashe mana mutum saba’in.” Kuma Annabi (SAW) ya kasance shi da sahabbansa sun sanya mushirikai sun rasa mutum dari da arba’in, su kuma sun kama fursunonin yakin kamar saba’in suka kashe mutum saba’in.” A nan haka sai Abu Sufiyan (da ya ga kamar sun ci Musulmi da yaki) sai ya ce: “Acikinku da kuka saura da rai ko akwai Muhammadu? Ya rika fadin haka har sau uku, Sai Annabi (SAW) ya hana su amsa masa. Sa’an nan ya ce: “Akwai dan Abu kuhafa (Abubakar) a cikinku? Har sau uku, sa’an nan ya ce: “Akwai Umar dan Khaddab a cikinku? Har sau uku.” Sai ya juya shi da mutanensa ya ce: “Amma wadannan dai duk an kashe su. Sai Umar ya kasa hakura ya ce: “Makiyin Allah! Wallahi ka yi karya, lallai wadannan da ka lissafa dukansu suna raye, abin da ke bata maka rai zai tabbata maka.” Sai (Abu Sufiyan) ya ce: “Yau namu ne kamar yadda Badar take taku, yakin kuma jan masaki ne (kun yi nasara, mu ma mun yi nasara), kuma lallai za ku iske jama’arku matattatu kuma haka bai bata mini rai.” Sa’an nan ya ci gaba da rera waka yana cewa: “Gunkil Hubal ya daukaka! Hubal ya daukaka! Sai Annabi (SAW) ya ce: “Ba za ku amsa musu ba? Suka ce, “Ya Manzon Allah (SAW) me za mu ce? Ya ce: “Ku ce, Allah ne Madaukaki.” Sai ya ce: “Lallai mu, muna da Uzza ba ku da Uzza.” Sai Annabi (SAW) ya ce: “Shin ba za ku amsa masa ba? Ya ce, “Sai suka ce, me za mu amsa masa, ya Manzon Allah! Ya ce: “Allah Shi ne Maulanmu (Majibincinmu), ku kuwa ba ku da maula.”
Babi na dari da Sittin da Biyar: Idan mutane suka firgita da dare:
713. An karbo daga kutaiba dan Sa’id ya ce: “Hammad ya ba mu labari daga Sabit daga Anas (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance ya fi mutane kyau, kuma ya fi mutane alheri, kuma ya fi mutane jarumtaka. Kuma mutanen Madina sun taba firgita cikin dare saboda sun ji wata kara mai karfi. Ana nan haka sai Annabi (SAW) ya hadu da su lokacin da ke komowa daga wajen binciken abin da ya faru bisa wata godiyar Abu dalhat marar sirdi, alhali yana rataye da takobinsa. Sai ya ce: “Kada ku firgita! Kada ku firgita! Sa’an nan ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya na same shi kamar kogi saboda saurinsa.” Abin da ake nufi dokin nan ya da sauri.