Buhari da Muslim

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi Babi na Dari da Tamanin da Biyu: Lallai Allah zai karfafa wannan addini ko da ta karkashin fajiri ne: 15. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri, Hawwala Sanad. 16. An karbo daga Mahmud ya ce: “Abdurrazak ya ba mu labari […]

Buhari da Muslim
Buhari da Muslim

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Dari da Tamanin da Biyu: Lallai Allah zai karfafa wannan addini ko da ta karkashin fajiri ne:

15. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri, Hawwala Sanad.

16. An karbo daga Mahmud ya ce: “Abdurrazak ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Zuhuri daga Dan Musayyab daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Mun halarci wani yaki tare da Manzon Allah (SAW) sai ya ambaci wata magana ga wani mutum da ke da’awar Musulunci (Annabi SAW) ya ce: “Wannan yana daga cikin mutanen wuta. Lokacin da ya halarcin yakin nan, mutumin nan ya yi yaki mai tsanani sai aka yi masa rauni. Sai aka ce ya Manzon Allah, wanda ka fadi wata magana game da shi dazu cewa yana daga cikin mutanen wuta, ya mutu.” Sai Annabi (SAW) ya ce: “Wuta zai tafi,” har sai da wadansu mutane suka kusan su yi kokwanto (bisa ga abin da Annabi SAW ya fada). Ana cikin haka sai aka ce, bai mutu ba amma dai yana da rauni mai tsanani. Lokacin da dare ya yi sai ya gaza hakuri bisa raunin sai ya kashe kansa. Da aka ba Annabi (SAW) labarin haka sai ya ce: “Allahu Akbar, na shaida lallai ni bawan Allah ne kuma ManzonSa ne.” Sa’an nan ya umarci Bilal ya yi shela ga mutane cewa: “Babu wata rai da za ta shiga Aljanna face rai Musulma. Kuma lallai Allah zai daukaka wannan addini ko da ta karkashin mutum fajiri.”

Babi na Dari da Tamanin da Uku:

Wanda ya shugabanci mutane wajen yakin daukaka kalmar Allah, ba tare da an shugabantar da shi ba, idan ya ji tsoron abokan gaba:

17. An karbo daga Yakub dan Ibrahim ya ce: “Dan Ulayyatu ya ba mu labari daga Ayyub daga Humaid dan Hilal daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya yi muna huduba (a lokacin Yakin Mu’atata). Ya ce: “Zaid dan Haris ya dauki tutar yaki amma an kashe shi. Sa’an nan Abdullah dan Rawah ya karba shi ma an kashe shi. Sa’an nan Khalid dan Walid ya karba ba tare da an nada shi ba, Allah Ya bayar da cin nasara ta wurinsa. Kuma lallai su da aka kashe ba zan so a ce suna raye tare da mu ba, ko ya ce: “Ba za su so a ce suna raye tare da mu ba (Saboda abin da suka iske na alheri.) Lokacin idanuwarsa na zubar da hawaye.”

Babi na Dari da Tamanin da Hudu: Neman taimakon karin mayaka a lokacin yaki:

18. An karbo daga Muhammad dan Basshar ya ce: “Dan Abu Addiyu da Sahlu dan Yusuf sun ba mu labari daga Sa’id daga Kattada daga Anas (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Annabi (SAW) kabilar Ri’ilu da Zakawan sun je masa tare da kabilar Usayyatu da kabilar Lahyan. Sai suka riya cewa lallai su, sun musulunta (amma karya suke yi). Kuma wai mutanen suna auka (fada) musu da yaki don haka suke neman taimakon (Annabi SAW) da wadansu mayaka. Sai Annabi (SAW) ya taimaka musu da mutum saba’in daga mutanen Madina. Anas ya ce: “Mun kasance muna kiransu da sunan: Makaranta Alkur’ani. Sun kasance suna dauko itace da rana da dare suna ta Sallah. Sai suka tafi da su har sai da suka isa rijiyar Ma’unatu sai suka yaudare su, suka kashe su (Makaranta Alkur’anin). (Annabi SAW) Ya rika musu kanuti kusan wata guda yana addu’a a kan Ri’il da Zakawan da Lihyan. Kattada ya ce, Anas ya ba mu labari ya  ce: “Lallai su, sun karanta musu Alkur’ani da cewa: “Ya Allah! Ka isar da wannan abin da ya faru da mu ga jama’armu. Lallai mun hadu da Ubangijinmu Ya yarda da mu, kuma mun yarda da abin da Ya yi mana.” Sa’an nan wannan aya aka dauke (shafe) ta.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara