Buhari da Muslim

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai Littafin bayanin hukuncin farillan daya cikin biyar na ganimar yaki. Bisa fadar Allah Madaukaki: 43. An karbo daga Abdan ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Yunus ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Aliyu dan Husaini ya ba ni labari cewa: Lallai Husain dan […]

Buhari da Muslim
Buhari da Muslim

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

Littafin bayanin hukuncin farillan daya cikin biyar na ganimar yaki. Bisa fadar Allah Madaukaki:

43. An karbo daga Abdan ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Yunus ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Aliyu dan Husaini ya ba ni labari cewa: Lallai Husain dan Aliyu (AS) ya ba shi labari cewa, lallai Aliyu ya ce: “Ya kasance ina da wani rakumi da na samu daga rabon ganimar Badar. Kuma Annabi (SAW) ya ba ni wani rakumi daga daya cikin biyar na ganima. Lokacin da na yi nufin aure da Fadima ’yar Manzon Allah (SAW) sai na yi wa’adi da wani makerin zinari daga kabilar Kainuka’u yakan tafi tare da ni sai mu yiwo kayan tsaure. Ina nufin in rika sayarwa ga makera. Saboda in yi amfani da kudin wajen walimar aurena. Ina cikin wannan halin tanadi da sai na debi wasu kaya da sirdin taguwa na gurfana da su kusa da gidan wani mutumin Madina. Sai na komo lokacin da tara abin da nake son tarawa. Sai kawai taguwoyin nan nawa biyu na iske an yanke musu tozo an soke kwibinsu biyu an debe hantarsu. Sai na kasa (gaza) tsare idona daga kuka, saboda abin da na gani. Na ce, “Wa ya aikata mini wannan? Sai suka ce mini, “Hamza dan Abdul Mudallib ne ya aikata, yana cikin wannan gida na mutanen Madina inda ake shan giya. Sai na tafi har sai da na shiga Annabi (SAW) yana tare da Zaid dan Harisa, Annabi (SAW) ya fahimci abin da ke cikin fuskata na bacin rai. Sai Annabi (SAW) ya ce, me ya faru da kai? Na ce, “Ya Manzon Allah! Ban taba ganin bakin ciki irin wannan yini ba, Hamza ya fada wa taguwoyina biyu ya katse musu tozo, ya huda cikinsu. Ga shi can a wani gida na shan giya. Annabi (SAW) ya kira aka kawo masa alkyabbarsa ya yafa ta. Sa’an nan ya tafi da kafa na bi shi ni da Zaid dan Harisa har sai da ya isa ga gidan da Hamza ke cikinsa, ya nemi izini suka yi masa izini sai ga su cikin maye. Sai Manzon Allah (SAW) ya rika zargin Hamza bisa abin da ya aikata, sai ga Hamza idanuwansa sun yi ja, Hamza ya yi dubi ga Manzon Allah (SAW) sa’an nan ya daga idonsa, ya yi dubi zuwa ga gwiwarsa. Sa’an nan ya dubi zuwa cibiyarsa sa’an nan ya daga ganinsa zuwa fuskarsa. Sa’an nan Hamza ya ce: “Shin ku ba komai ba ne face bayin babana.” Sai Manzon Allah (SAW) ya fahimci cewa lallai shi ya bugu: Sai Manzon Allah (SAW) ya juya bisa duga-duginsa da sauri zuwa baya, muka fita tare da shi.”

44. An karbo daga Abdul’aziz dan Abdullahi ya ce: “Ibrahim dan Sa’ad ya ba mu labari daga Salih daga Dan Shihab ya ce: “Urwatu dan Zubair ya ba ni labari cewa: Lallai Uwar Mumminai A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ba shi labari cewa: Lallai Fadima (AS) ta nemi Ababakar Siddik ya ba ta rabonta na gadon dukiyar fai’u (ganimar da aka same ta ba ta hanyar zubar da jini ba) bayan rasuwar Manzon Allah (SAW), tana neman a ba ta gadon abin da Manzon Allah (SAW) ya bari. Sai Abubakar ya ce: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ba a  gadon mu (Manzanni), abin da  muka rasu muka bari sadaka ce.” Sai Fadima ’yar Manzon Allah (SAW) ta yi fushi har ta kaurace wa Abubakar  ba ta gushe ba tana kaura ce masa har ta rasu. Kuma ta rayu ne a bayan rasuwar Manzon Allah (SAW) da kamar wata shida. (A’isha) ta ce, “Fadima ta kasance tana neman rabonta daga abin da Manzon Allah (SAW) ya rasu ya bari daga dukiyar Khaibara da Fadak da sadakarsa na Madina. Abubakar ya ki karba mata bisa ga haka ya ce: “Ban barin komai daga abin da Manzon Allah (SAW) ya kasance yana aiki da shi face na yi aiki da kamarsa. Kuma lallai ni ina jin tsoron in har na bar wani al’amarinsa da ke aikatawa, zan karkace.” Amma sadakarsa da ke Madina sai Umar ya mika ta ga Abbas, amma Khaibar da Fadak, Umar ya rike su ya ce: “Sukan sadakar Manzon Allah (SAW) ne, hakkokinsu sun kasance abin da ke batarwa a shekara, da wasu bukatunsa da suke faruwa. Al’amarinsu na ga hannun wanda yake rike da shugabancin wannan al’umma.” Zuhuri ya ce: Suna bisa haka har zuwa Ranar Kiyama.”

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara