Buhari da Muslim
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi Babi na Tamanin da daya: Bayanin garkuwa (a fagen yaki): 591. An karbo daga Isma’il ya ce: “dan Wahab ya ba ni labari ya ce, Amru ya ce, Abul Aswad ya ba ni labari daga Urwatu daga A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya […]
Tare da Sheikh Yunus Is’hak
Almashgool, Bauchi
Babi na Tamanin da daya:
Bayanin garkuwa (a fagen yaki):
591. An karbo daga Isma’il ya ce: “dan Wahab ya ba ni labari ya ce, Amru ya ce, Abul Aswad ya ba ni labari daga Urwatu daga A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya shigo gare ni lokacin tare da ni da wadansu ’yan mata biyu suna rera waka game wakan Ba’us (labarin yakin kabilar Khazraj da Awsu), sai (Annabi SAW) ya kwanta bisa shimfida ya juya fuskarsa. Ana cikin haka sai Abubakar (RA) ya shigo ya tsawace ni ya ce: “Gurmin shaidan a gidan Manzon Allah (SAW)? Sai Manzon Allah (SAW) ya juyo ya fuskance shi ya ce: “kyale su, lokacin da na faki shagalarsa (mantuwarsa game da su) sai na tunkuda su (na yi musu ban-kwana) suka fita. Kuma ya kasance wunin Idi, mutanen Sudan (bakaken fata) suna wasa da garkuwa da makamai, na kan rika rokon Manzon Allah (SAW) yakan ce shin kina sha’awar ki yi kallon? Ta ce, “Na’am, sai ya tsayar da ni a bayansa, kumatuna bisa kumatunsa. Har yana cewa: “Ku ci gaba ya kabilar Arfida! Har sai da na kosa (gaji) ya ce: “Ya ishe ki? Ta ce, “Na’am, ya ce, “To ki tafi.”
Babi na Tamanin da Biyu:
Bayanin rataya makami da hukuncin ratayar takuba bisa wuya:
592. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Hammad dan Zaid ya ba mu labari daga Sabit daga Anas (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya kasance ya fi mutane kyawun hali. Kuma ya fi kowa jaruntaka. Kuma an taba samun wani abin firgici a garin Madina cikin wani dare, sai suka fito da kamar wani kuwwa mai karfi. Annabi (SAW) ya fuskance su alhali har ya tafi neman (binciken) labari ya komo yana bisa wata godiya (doki) mara sirdi na Abu dalha yana rataye da takobi bisa wuyansa. Yana cewa: “Kada ku firgita! Kada ku firgita! Sa’an nan ya ce: “Lallai na samu wannan doki da sauri kamar kogi.”
Babi na Tamanin da Uku:
Yadda ake kawa ga takubba:
593. An karbo daga Ahmad dan Muhammad ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Auza’iyyu ya ba mu labari ya ce, Na ji Saulaiman dan Habib ya ce: “Na ji Abu Umamah yana cewa: “Lallai wadansu jama’a sun yi yake-yake suka ci nasara a kan wadansu jama’a har ya kasance kawar takubbansu ba zinare ba ne ko azurfa amma kawar ta kasance na fatu ne da dalma da bakin karfe.”
Babi na Tamanin da Hudu:
Wanda ya rataya takobinsa bisa itaciya lokacin barcin rana:
594. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce: “Sinan dan Abu Sinan Du’ali da Abu Salmah dan Abdurrahman ya ba mu labari cewa: “Lallai Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), ya ba shi labari cewa: Lallai shi ya fita yaki tare da Manzon Allah (SAW) ta wajen Najad lokacin da Manzon Allah (SAW) ya fita sahabbai suka fita tare da shi, barcin rana ya kama su lokacin da suka kai kwarin Idadat (mai yawan kaya). Sai Manzon Allah (SAW) ya sauka mutane suka rarraba suna neman inuwar itatuwa. Manzon Allah (SAW) ya sauka karkashin wata itaciya ya rataya takobinsa a kanta. Muka yi barci mai nauyi, ana haka sai Manzon Allah (SAW) ya rika kiranmu tare da shi da wani Balaraben kauye ya ce: “Lallai wannan ya dauki takobina lokacin ina barci, sai na farka na same shi da takobi tube (ba shi cikin kube) ya ce: “Wa zai tsare ni daga gare shi? Na ce, “Allah ne, har sau uku.” Annabi (SAW) bai hukunta shi ba, sai ya koma ya zauna. (Abin da ya faru Mala’ika Jibril ya fisge takobin daga hannun Balaraben kauye ya kayar da shi kasa, Annabi (SAW) ya dauki takobin amma ya kyale shi bai kashe shi ba).