Buhari da Muslim 2
290. An karbo daga Muhammad dan Bashar ya ce: “Ghundar ya ba mu labari ya ce, Shu’abah ya ba mu labari daga kattada daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “An zo wa Annabi (SAW) da wani nama, sai aka ce, an ba wa Barira sadakarsa ne. Sai ya ce, “Shi […]
290. An karbo daga Muhammad dan Bashar ya ce: “Ghundar ya ba mu labari ya ce, Shu’abah ya ba mu labari daga kattada daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “An zo wa Annabi (SAW) da wani nama, sai aka ce, an ba wa Barira sadakarsa ne. Sai ya ce, “Shi sadaka ne gare ta, amma kyauta yake gare mu (daga wurinta).”
291. An karbo daga Muhammad dan Bashar ya ce: “Ghundar ya ba mu labari ya ce, Shu’abah ya ba mu labari daga Abdurrahman dan kasim ya ce, “ Na ji shi daga Alkasim daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai ita ta yi nufin ta sayi Barira amma iyalanta lallai sun gitta sharadin walicci gare su. Sai aka ambaci haka ga Annabi (SAW), sai Annabi (SAW) ya ce: “Ki saye ta, ki ’yanta ta amma walicci yana ga wanda ya ’yanta.” Ana nan haka wata rana sai aka ba ta (sadakar) wani nama. Sai Annabi (SAW) ya ce, “Mene ne wannan? Na ce, “An ba Barira sadaka ce,” sai ya ce, “gare ta sadaka ce, amma a gare mu kyauta ce.” Sai aka ba wa Barira zabin (zama da mijinta ko rabuwa da shi). Abdurrahman mijinta da ne ko bawa? Shu’abah ya ce, “Na tambayi Abdurrahman game da mijinta ban sani ba da ne ko bawa?”
292. An karbo daga Muhammad dan Mudatil Abul Husain ya ce: “Khalid dan Abdullahi ya ba mu labari daga Khalid Hazza’u daga Hafsa ’yar Sirin daga Ummu Adiyyah ta ce: “Annabi (SAW) ya ce da A’isha (Allah Ya yarda da ita): “Shin ko kuna da wani abin ci? Ta ce, “A’a, face wannan abin da Ummu Adiyyah ta aiko da shi daga namar akuyar da ka taba aika mata da shi na sadaka,” wannan kan ai ba komai tunda dai hakika sakon ya isa muhallinta. (Wato gare ta sadaka, a gare mu kuma kyauta).”
Babi na Takwas: Hukuncin wanda ya yi kyauta zuwa ga abokinsa har yana kirdadon (jirar ranar kwana) wadansu daga cikin matansa ban da wadansu:
293. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Hammad dan Zaid ya ba mu labari daga Hisham daga Babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Mutane sun kasance suna kirdadon ranar kwanan dakinta da kyautarsu (don neman karbawa wajen Allah). Ummu Salmah ta ce, “Lallai abokaina (sauran mata) sun taru suka tattauna