Buhari Da Muslim

Tare da Sheikh Yunus Is’haq Almashgool, Bauchi 45. An karbo daga Is’hak dan Muhammad Alfarawiyyu ya ce: “Malik dan Anas ya ba mu labari daga Dan Shihab daga Malik dan Ausu dan Hadasan cewa: “Muhammad dan Jubair ya kasance ya ambata mini wani labari daga hadisinsa. Sai na tafi har na shiga ga Malik dan […]

Buhari Da Muslim
Buhari Da Muslim

Tare da Sheikh Yunus Is’haq Almashgool, Bauchi

45. An karbo daga Is’hak dan Muhammad Alfarawiyyu ya ce: “Malik dan Anas ya ba mu labari daga Dan Shihab daga Malik dan Ausu dan Hadasan cewa: “Muhammad dan Jubair ya kasance ya ambata mini wani labari daga hadisinsa. Sai na tafi har na shiga ga Malik dan Awsu na tambaye shi game da wannan Hadisi sai Malik ya ce: “Wata rana ina zaune a cikin iyalina a lokacin da rana ta raba. Sai ga dan aikar Umar dan Khaddab (RA) ya zo mini ya ce mini ka je Sarkin Muminai na kira. Sai tafi tare da shi har na shiga ga Umar sai ga shi a zaune a gado marar shimfida babu shimfida a kusa da shi, ya jingina bisa ga wani matashi na fata (wanda aka cika audugar rimi). Na yi masa sallama, sa’an nan na zauna. Sai ya ce: “Ya Malik, lallai wadansu jama’a daga mutanenka masu yawan iyali sun zo mini da bukata. Kuma na umarta da wannan kyauta, karba ka raba ta a tsakaninsu. Sai na ce, “Ya Sarkin Muminai da dai ka umarci wanina? Sai ya ce: “Kai wannan mutum ka karba! Lokacin ina zaune a gare shi sai ga mai tsaron kofarsa mai suna Yarfa’u ya zo masa ya ce: “Ga Usman da Abdurrahman dan Aufu da Zubair da Sa’ad dan Abu Wakkas sun zo ko za ka yi musu izini? Ya ce: “Na’am, ya yi musu izini, suka shigo suka yi sallama, suka zauna. Sai Yarfa’u ya zauna na dan lokaci, sai ya zo ya ce: “Ga Aliyu da Abbas ko za ka yi musu izini? Ya ce, “Na’am, ya yi musu izini suka shigo suka yi sallama suka zauna. Sai Abbas ya ce: “Ya Sarkin Muminai! Ka yi hukunci a tsakanina da wannan, saboda su suna husuma bisa ga abin da Allah Ya ba ManzonSa na ganimar (fai’u) daga dukiyar kabilar Bani Nadir. Sai jama’ar da ke wurin su Usman da abokansa suka ce, “Ya Sarkin Muminai! Ka yi hukunci a tsakaninsu, don ka hutar da sashensu a kan sashe. Sai Umar ya ce: “Ku yi hakuri! Zan hada ku da Allah, wanda da izininSa sama da kasa ke tsayuwa. Shin ko kun san lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mu (Annabawa) ba a gadonmu, duk abin da  muka bari sadaka ne,” yana nufin Manzon Allah (SAW) da kansa? Sai wadansu jama’a suka ce: “Lallai ya fadi haka.” Sai Umar ya fuskanci Aliyu da Abbas, ya ce: ‘Ina hada ku da Allah, shin ko kun san cewa: Lallai Manzon Allah (SAW) ya fadi haka?  Sai suka ce, “Lallai ya fadi haka.” Sai Umar ya ce, “Lallai ni zan ba ku labari game da wannan al’amari. Lallai Allah ne Ya kebance ManzonSa da wani abu daga wannan dukiyar fai’u. Bai halatta ta ga kowa ba face shi.” Sa’an nan ya karanto fadar Allah Madaukaki cewa: “Bisa ga abin da Allah Ya bai wa ManzonSa na fai’u daga gare su….(K:59:6). Saboda haka wannan ta kasance kebantacciya gare shi, kuma (Annabi) bai karbe ta duka ba, kuma bai fifita kansa ya bar ku ba. Lallai ya mika ta gare ku ya watsa ta cikinku, har ya rage wannan dukiyar ce tasa. Don haka Manzon Allah (SAW) yake ciyar da iyalansa a shekara daga wannan dukiya. Sa’an nan yakan dauki abin da  ya saura ya sanya shi a wurin da ake ajiye dukiyar Allah. Haka Manzon Allah (SAW) ya rika aikatawa cikin rayuwarsa. Ina hada ku da Allah shin kun san haka yake aikatawa? Suka ce, “Na’am.’ Sai ya fada wa Aliyu da Abbas: Ina hada ku da Allah shin kun san haka? Umar ya ce: “Sa’an nan Manzon Allah (SAW) ya rasu, Abubakar ya ce: “Shi ne waliyin Manzon Allah (SAW) ya karbe ta, ya yi aiki cikinta da abin da  Manzon Allah (SAW) ya yi aiki da shi. Kuma Allah Shi ne Masani lallai shi mai gaskiya ne mai da’a, mai shiryarwa kuma mai bin gaskiya. Sa’an nan Abubakar ya rasu. Ni na kasance waliyyin (mai bi wa) Abubakar na karbe ta shekara biyu, a cikin shugabancina zan yi aiki da irin yadda Manzon Allah (SAW) da kuma irin yadda Abubakar ya yi aiki cikinta. Allah Shi ne Mafi sani lallai ni mai gaskiya ne a cikinta. Kuma ni mai da’a ne, mai shiryarwa, kuma mai bin gaskiya. Sa’an nan ku (Aliyu da Abbas) kun zo kuna yi mini magana, kuma maganarku daya ce, kuma al’amrinku daya ne, kai Abbas ka zo mini kana neman rabonka daga dan dan uwanka. Wannan kuma ya zo yana nufin Aliyu, yana neman rabon matarsa daga mahaifinta (AS) na ce, muku: Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ba a gadonmu, abin da  muka bari sadaka ce.” Lokacin da ya bayyana mini in mika ta gare ku, bisa alkawarin Allah da amanarsa tana kanku lallai za ku yi aiki cikinta da irin abin da  Manzon Allah (SAW) yake aiki cikinta, da kuma irin yadda Abubakar ya yi aiki cikinta, kuma da irin abin da nake aiki cikinta tunda na fara shugabanci, kuka ce in ba ku, to ga ta nan na ba ku. Ina hada ku da Allah shin yanzu na mika ta gare ku. Jama’a suka ce, “Na’am,” sai ya fuskanci Aliyu da Abbas ya ce: “Ina hada ku da Allah shin na mika ta gare ku? Suka ce, ‘Na’am,” sai ya ce: “Sai dai ku nemi hakkin waninku gare ni, ba wannan ba? Ina rantsuwa da Wanda da izininSa sama da kasa ke tsayuwa ba zan yi hukunci da wanin haka ba. Idan kun gajiya game da ita to ku miko mini ita, lallai ni zan isar muku.”

 

 

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara