Buhari da Muslim

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi 61. An karbo daga Sa’id dan Muhammad Aljarmiyyu ya ce: “Yakub dan Ibrahim ya ba mu labari ya ce, Babana ya ba mu labari cewa: Lallai Walid dan Kasir ya ba shi labari daga Muhammad dan Amru dan Halhalatu Addailiyyu ya ba shi labari cewa: Lallai dan Shihab […]

Buhari da Muslim
Buhari da Muslim

Tare da Sheikh Yunus Is’hak

Almashgool, Bauchi

61. An karbo daga Sa’id dan Muhammad Aljarmiyyu ya ce: “Yakub dan Ibrahim ya ba mu labari ya ce, Babana ya ba mu labari cewa: Lallai Walid dan Kasir ya ba shi labari daga Muhammad dan Amru dan Halhalatu Addailiyyu ya ba shi labari cewa: Lallai dan Shihab ya ba shi labari cewa: Lallai Aliyu dan Husain ya ba shi labari cewa: Lallai su lokacin da suka iso Madina daga wajen Yazid dan Mu’awiyya inda aka kashe Husain dan Aliyu (Allah Ya yi masa rahama), sai Miswar dan Makhramat ya iske shi  ya ce masa: Shin ko kana da wata bukata da za ka umarce ni da ita? Na ce masa, “A’a, sai ya ce: “Shin ko za ka ba ni takwabin Manzon Allah (SAW) ina jin tsoron kada mutane su rinjaye ka a kansa yau? Ina rantsuwa da Allah idan ka ba ni ba za su samu ikon karbarsa face in sun kashe ni.” Kuma ya ce: “Lallai Aliyu dan Abu Dalib (RA) ya taba neman ’yar Abu Jahil bisa ga nemansa ga Fadima (AS) (wato suna tare). Sai na ji Manzon Allah (SAW) yana huduba ga mutane a mumbarinsa wannan. Lokacin na balaga sai ya ce: “Lallai Fadima tawa ce, kuma lallai ni ina tsoron a fitine ta cikin addininta (bisa ga ’yar Abu Jahil). Sa’an nan ya ambaci surukuntarsa da kabilar Abdu Shams ya yabe shi bisa ga surukuntarsa da shi. Ya ce: Ya yi mini magana ya yi mini gaskiya, ya yi mini alkawari ya cika. Kuma lallai ni, ban zamo mai haramta halal, ko kuma mai halatta haram ba. Amma wallahi ’yar Manzon Allah (SAW) ba ta haduwa da ’yar makiyin Allah har abada.”

 

62. An karbo daga Kutaiba dan Sa’id ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Muhammad dan Surakatu daga Munzir daga Abu Hanifiyyatu ya ce: “Da dai Aliyu (Allah Ya yarda da shi), ya kasance yana son ya zame wa Usman (Allah Ya yarda da shi) tunatarwa bisa munantawa da ya yi masa a ranar da mutane suka zo suna kai kukan tawagar masu karbar Zakkar Usman. Sai (Aliyu) ya ce: “Ka tafi ga Usman ka ba shi labari cewa: Lallai wannan sako takardar karbar sadaka ce ta Manzon Allah (SAW) don haka ka umarci ma’aikatanka su yi aiki da ita, sai na je da ita, ya ce: “Ka wadatar da ni game da wannan.” Sai na tafi da ita ga Aliyu na ba shi labari.” Abu Hannafiyyatu ya ce: “Babana ya aike ni cewa: Ka karbi wannan takarda ka tafi da shi zuwa ga Usman (RA), abin da ke cikinta umarnin Manzon Allah (SAW) ne game da yadda za a rika karbar sadaka.”

 

Babi na Shida:

Dalilin da ke tabbatar da daya cikin biyar na ganimar yaki. Saboda rage wasu bukatun Manzon Allah (SAW) ne da miskinai. Da bayanin baiwar da Annabi (SAW) ya yi wa mutane Suffah (talakawa) da gwagware kuma da bayanin lokacin da Fadima (RA) ta tambaye shi tana kukan rashin mai yi mata hidima saboda wahalar nika da kwaba alkama. Saboda ya ba ta kuyangi sai ya mayar da ita zuwa ga yarda da al’amarin Allah.

63. An karbo daga Badal dan Muhabbar ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Hakam ya ba ni labari ya ce, na ji Dan Abu Wa’il ya ce, Aliyu ya ba mu labari cewa: Lallai Fadima (AS) ta taba kaiwa kukan abin da  ke faruwa da ita na wahalar nika da kwaba alkama. Saboda haka da ta ji an zo wa Manzon Allah (SAW) da kuyangi na fursunonin yaki, sai ta tafi ta roke shi (Annabi) ya ba ta mai yi mata hidima, sai ba ta iske shi gida ba. Sai ta fada wa A’isha (RA) da Annabi (SAW) ya komo A’isha ta ambata masa. (Fadima) ta ce: “Sai (Annabi) ya zo muna gida lokacin har mu shiga kwanci, sai muka yi kokarin tashi domin taryarsa sai ya ce: “Ku zauna inda kuke, har ina jin sanyin kafarsa bisa kijina (inji Fadima). Sai ya ce: “Shin in nuna muku abin da ya fi Abin da kuka nema gare ni alheri, idan kuka yi riko da su lokacin barcinku? Ya ce: Ku yi kabbara sau talatin da hudu (34). Ku yi tahmidi talatin daidai (30). Ku yi tasbihi sau talatin (30). Wannan ya fi muku alheri daga abin da kuka roke ni game da shi.”

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano