BUHARI DA MUSLIM

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi 72. An karbo daga Muhammad dan Ala’u ya ce: “Dan Mubarak ya ba mu labari daga Ma’amar daga Hammam dan Munabbih daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce, “Wani Annabi ya taba nufin fita yakin daukaka kalmar Allah tare da jama’arsa, […]

BUHARI DA MUSLIM
BUHARI DA MUSLIM

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

72. An karbo daga Muhammad dan Ala’u ya ce: “Dan Mubarak ya ba mu labari daga Ma’amar daga Hammam dan Munabbih daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce, “Wani Annabi ya taba nufin fita yakin daukaka kalmar Allah tare da jama’arsa, sai ya ce: “Duk wanda ya yi sabon aure bai sadu da ita ba kuma yana son saduwa da ita, to kada ya bi ni zuwa wannan yaki. Haka kuma duk wanda ya gina wani gida da bai masa rufi ba, kuma yana son ya yi masa rufi kada ya biyo ni. Haka wanda ya sayi tumaki ko wasu dabbobin da ke dakon haihuwarsu. Daga nan ya fita zuwa yakin da ya kusanci wata alkarya kuma sai ga lokacin Sallar La’asar ya yi. Ko ya ce rana ta yi kusan buya kuma bai yi Sallar La’asar ba kuma ga yaki. Sai ya ce ga rana: “Ke ma wadda ake umarta ce, kuma ni ma an umarce ni. Ya Allah! Ka tsare ta gare mu. Sai aka tsare ta har sai da Allah Ya ba su cin nasarar yaki. Ya tara ganima mai yawa wuta ta zo don ta cinye ta, ta gaza cin ta. Sai (Annabin) ya ce: “Lallai daga cikinku akwai wanda ya boye wani abu (gululu). Saboda haka kowace kabila ta zo ta yi mini mubaya’a dai-daya. Sai hannun mutum biyu ko ya ce, mutum uku suka makale da hannunsa (Annabi). Ya ce: “Cikinku akwai gululu, sai suka zo da wani dunkulen zinari kamar kan saniya suka sanya ta. Sai wuta ta zo ta cinye ganimar. (Annabi)  (SAW) ya ce: “Sa’an nan Allah Ya halatta mana ganimomi, kuma Ya ga rauninmu da gazawarmu Ya halatta mana ita.”

 

Babi na Tara: Ganima ana raba ta ce ga wanda ya halarci fagen yaki:

73. An karbo daga Sadakatu ya ce: “Abdurrahman ya ba mu labari daga Malik daga Zaid dan Aslam daga Babansa ya ce: “Umar (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Ba domin Musulmi da suke gaba gare mu ba, da ban taba cin wata kasa da yaki ba. Face na raba ta a tsakanin jama’arta kamar yanda Annabi (SAW) ya raba dukiyar Khaibara.”

 

Babi na Goma: Hukuncin wanda ya fita yakin Musulunci domin samun ganima shin ko ladarsa ya tauye?:

74. An karbo daga Muhammad dan Bashar ya ce: “Ghundar ya ba mu labari ya ce, Shu’abah ya ba mu labari daga Amru ya ce: “Na ji Abu Wa’il ya ce, Abu Musal Ash’ariyuu (Allah Ya yarda da shi),  ya ba mu labari ya ce: “Wani Balaraben kauye ya zo ga Annabi (SAW), ya ce: “Daga cikin mutane akwai mai yaki don ganima. Kuma akwai mutumin da ke yakin nan saboda a yabe shi. Kuma domin a ga matsayinsa. To, wane ne domin daukaka kalmar Allah? Sai (Annabi) ya ce: “Wanda ya yi yakin nan domin kalmar Allah ta kasance madaukakiya shi ne domin Allah.”

 

Babi na Goma Sha Daya: Shugaba yana iya rabon ganima ga wadanda suke nan kuma yana iya ajiye wani abu ga wadanda ba su nan halarce:

75. An karbo daga Abdullahi dan Abdulwahab ya ce: “Hammad dan Zaid ya ba mu labari, daga Ayyub daga Abdullahi dan Abu Mulaikatu cewa: “Lallai Annabi (SAW) an taba yi masa kyautar wasu taguwoyin siliki masu maballan zinari. Sai ya raba su ga wadansu daga sahabbansa ya janye daya daga ciki ya ajiye saboda Makhramatu dan Naufal. Sai ya zo tare da shi da Miswar dan Makhramatu ya tsaya a kofa. Ya ce, “Kira mini shi, sai Annabi (SAW) ya ji muryarsa ya riko wata taguwar yana rataye da ita, sai ya fuskance shi da wannan taguwar siliki ya ce: “Ya Abu Miswar na ajiye maka wannan ce, ya fadi haka har sau biyu, saboda cikin halayensa (Makhrama) akwai wani abu.”

 

Babi na Goma Sha Biyu: Yadda Annabi (SAW) ya raba ganimar Bani Kuraizat da Bani Nadir da bayanin abin da  ya ajiye saboda wasu bukatunsa.

 

76. An karbo daga Abdullahi dan Aswad ya ce: “Mu’atamir ya ba mu labari daga babansa ya ce, na ji Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), yana cewa: “Mutum yakan kasance yana sanya gonar dabinai kyauta ga Annabi (SAW) har sai da Allah Ya ba shi budi a kan Bani Kuraiza da Nadir. Daga nan ya kasance bayan haka yana mayar wa jama’a kyautarsu.”

 

 

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano