Buhari da Muslim
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi Babi na Goma Sha Tara: Abin da Annabi (SAW) ya kasance yana bayarwa saboda lallashin wadanda suke wajen Musulunci daga daya cikin biyar na ganimar yaki. Abdullahi dan Zaid ya ruwaito shi daga Annabi (SAW): 90. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Auza’iyyu ya ba mu […]
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi
Babi na Goma Sha Tara: Abin da Annabi (SAW) ya kasance yana bayarwa saboda lallashin wadanda suke wajen Musulunci daga daya cikin biyar na ganimar yaki. Abdullahi dan Zaid ya ruwaito shi daga Annabi (SAW):
90. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Auza’iyyu ya ba mu labari daga Zuhuri daga Sa’id dan Musayyib da Urwatu dan Zaubair cewa: “Lallai Hakim dan Hizam (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Na taba rokon Manzon Allah (SAW) ya ba ni. Sa’an nan na sake rokonsa ya ba ni. Sa’an nan ya ce mini: “ Ya Hakim! Lallai wannan dukiya kamar ’ya’yan itace ne mai zaki (koriya ce mai saukin ci), wanda duk ya karbe ta da neman wadutawa daga roko Allah zai sanya masa albarka. Wanda ke karba don tarawa da neman daukaka ba a sanya masa albarka. Sai ya kasance kamar wanda ke cin abinci bai koshi. Kuma hannu madaukaki (mai mikawa) ya fi alheri a kan hannu makaskanci (mai karba).” Sai Hakim ya ce, “Sai na ce, “Ya Manzon Allah! Ina rantsuwa da Wanda Ya aiko ka da gaskiya ba zan sake rokon wani ba a kan komai a bayanka har in bar duniya. Daga nan Abubakar (RA) ya kasance yakan kira Hakim don ya ba shi kyauta sai ya ki karbar komai. Sa’an nan lokacin Umar (RA) ya kira shi domin ya ba shi kyauta sai ya ki karba sai ya ce: “Ya jama’ar Musulmi! Ku shaida na gitta (ba shi) hakkinsa wanda Allah Ya raba daga wannan ganimar yaki sai ya ki karbarsa. Hakim ya bar rokon komai daga wajen mutane bayan Annabi (SAW) har ya rasu.”
91. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce: “Hammad dan Zaid ya ba mu labari daga Ayyub daga Nafi’u cewa: “Lallai Umar dan KhaDDab (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Ya Manzon Allah! Lallai na taba alwashi a lokacin Jahiliyya cewa zan yi I’itikafi yini daya, sai ya umarce shi da ya cika alwashinsa. Ya ce, “Umar ya samu ’yan mata biyu daga fursunan Yakin Hunain sai ya sanya su daga cikin gidajen Makka. Ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya yi baiwa (’yanta) wadansu fursunonin Yakin Hunain sai suka rika tafiya cikin hanya (babu wanda ya ce musu komai). Sai Umar ya ce da Abdullahi duba mene ne wannan? Ya ce, “Manzon Allah ne ya saki fursunonin yaki.” Sai ya ce, “Tafi ka ’yanta (sake) yaran matan nan biyu.” Nafi’u ya ce, “Manzon Allah (SAW) bai yi Umara daga Ji’iranata ba, da kuwa ya yi da haka bai buya ga Abdullahi dan Umar ba.”
92. An karbo daga musa dan Isma’il ya ce: “Jarir dan Hazim ya ba mu labari ya ce, Alhassan ya ba mu labari ya ce, “Amru dan Taglib (Allah Ya yarda da shi), ya ba ni labari cewa: “Manzon Allah (SAW) ya taba bayar da wata kyauta ga wadansu jama’a ya hana, bai bayar ga wadansu ba. Kamar ka ce, sai suka aibata shi. Sai ya ce: “Lallai ni, ina bayar da kyauta ga wadansu mutane saboda ina tsoron zamiyarsu da rashin hakurinsu. Kuma na bar wadansu mutane saboda abin da Allah Ya sanya a cikin zuciyarsu na alheri da wadatar zuci. Daga cikinsu akwai Amru DanTaglib, (Amru ya ce) babu abin da ya fi mini dadi kamar kalmar da Manzon Allah (SAW) ya fada game da ni ko da kuwa za a ba ni garken rakuma jajaye.” Alhassan ya ce: “Amru dan Taglib ya ce, “An taba zuwa ga Manzon Allah (SAW) da dukiya ko ya ce fursunan yaki (kuyangi) ya raba shi kamar yanda aka ambata a sama.”
93. An karbo daga Abul Walid ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Kattada daga Anas (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Lallai ni, ina bayar da kyauta ga Kuraishawa saboda neman jan hankalinsu (lallashinsu) ne, saboda ba su dade da shiga Musulunci ba.”