BUHARI DA MUSLIM
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi 98. An karbo daga Mahmud dan Ghailan ya ce: “Abu Usama ya ba mu labari ya ce, Hisham ya ba mu labari ya ce, Babana ya ba ni labari daga Asma’u ’yar Abubakar (Allah Ya yarda da su), ta ce: “Na kasance ina dibar dabino daga kasar Zubair da ke […]
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi
98. An karbo daga Mahmud dan Ghailan ya ce: “Abu Usama ya ba mu labari ya ce, Hisham ya ba mu labari ya ce, Babana ya ba ni labari daga Asma’u ’yar Abubakar (Allah Ya yarda da su), ta ce: “Na kasance ina dibar dabino daga kasar Zubair da ke Khaibara wanda Manzon Allah (SAW) ya yanka masa. Ina daukawa a kaina da kamar nisar farsaki uku daga gida.” Abu Damratu ya ce daga Hisham daga Babansa cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya yanka wa Zubair wata kasa daga dukiyar Bani Nadir.”
99. An karbo daga Ahmad dan Mikidad ya ce: “Fudail dan Sulaiman ya ba mu labari ya ce, Musa dan Ukubatu ya ba mu labari ya ce, Nafi’u ya ba ni labari daga Dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Umar dan Khaddab (RA) ya kore Yahudu da Nasara daga kasar Hijaz. Saboda Manzon Allah (SAW) ya kasance lokacin da ya ci nasara a kan mutanen Khaibara ya yi nufin korar Yahudawa daga cikinta. Kuma kasar da Allah Ya rinjiyar da AnnabinSa (SAW) a kan Yahudawa sai ta kasance na Manzon Allah (SAW) da Musulmi. Daga baya Yahudawa suka roki Manzon Allah (SAW) ya bar su bisa ga su rika noma gonakin a ba su rabin kayan amfanin gonar. Manzon Allah (SAW) ya ce, “Za mu bar ku zuwa lokacin da muka so, suka zauna bisa ga haka har lokacin da Umar (RA) a halifancinsa ya kore su zuwa Taima’u da Ariha.”
Babi na Ashirin: Abin da ake samu na abinci daga kasar abokan gaba:
100. An karbo daga Abul Walid ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Humaid dan Hilal daga Abdullahi dan Mughaffal (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Mun kasance daga wadanda suke tsaro a benayen Khaibara. Sai wani mutum ya jefo wata jakar fata cikinta da wasu kitse. Na rugo domin in dauka sai na waiga (waiwaya) na ga Annabi (SAW), sai na ji kunyarsa.”
101. An karbo daga Musaddad ya ce: “Hammad dan Zaid ya ba mu labari daga Ayyuba daga Nafi’u daga Dan Umar (RA) ya ce: “Mun kasance muna samun zuma da inabi a ganimar yake-yakenmu sai mu ci ba mu ko nuna shi (tarawa).”
102. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Abdul Wahid ya ba mu labari ya ce, Shaibani ya ba mu labari ya ce, na ji Dan Abu Aufa (Allah Ya yarda da su), yana cewa: “Yunwa ta taba kama mu, a cikin wasu dararen Yakin Khaibara, a wannan Yakin Khaibara ne muka fada wa jakunan gida muka soke. Lokacin da tukwane suka tafasa, sai mai shela ya yi shela daga wajen Manzon Allah (SAW) cewa: A zubar da abin da ke cikin tukwane, kuma kada kowa ya ci wani abu daga jakunan nan. Abdullahi dan Abu Aufa ya ce: “Sai muka rika cewa: Abin da ya sanya Annabi (AS) ya hana saboda baa cire Khumusi (daya cikin biyar na ganimar yaki wato saboda ba a yi rabo ba) ba ne. Ya ce, “Wadansu suka ce, an dai haramta cikin jaki ne gaba daya.” Sai na tambayi Sa’id dan Jubair ya ce: “Annabi (AS) ya haramta jaki ne gaba daya.”
Babi na Ashirin da Daya:
Harajin da ake karba daga kafiran amana saboda tsaron jininsu. Da sanya ajalin tsayar da yaki zuwa wani lokaci. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ku yaki wadanda ba su yi imani da Allah ba kuma ba su yi imani da Ranar Lahira ba kuma ba su haramta abin da Allah da ManzonSa suka haramta kuma ba su yin addini addinin gaskiya, daga wadanda aka bai wa Littafi, har sai sun bayar da jiziya daga hannu, kuma suna kaskantattu..(9:29).” Dan Uyaiyanatu ya ce, daga Dan Najih ya ce, na ce wa Mujahid: Mene ne sha’anin mutanen Siriya da suke bayar da Dinari hudu. Mutanen Yamen su bayar da Dinari dai-dai. Sai ya ce: “Sanya haka daga wajen Yassar ne.”