Buhari Da Muslim
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi Babi na Ashirin da Takwas: Yadda shugaba ke aikawa ga wanda ya warware alkawari: 114. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce: “Sabit dan Yazid ya ba mu labri ya ce, Asim ya ba mu labari ya ce: “Na tambayi Anas (Allah Ya yarda da shi), game da kunuti […]
Tare da Sheikh Yunus Is’hak
Almashgool, Bauchi
Babi na Ashirin da Takwas: Yadda shugaba ke aikawa ga wanda ya warware alkawari:
114. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce: “Sabit dan Yazid ya ba mu labri ya ce, Asim ya ba mu labari ya ce: “Na tambayi Anas (Allah Ya yarda da shi), game da kunuti yaushe ake yi? Ya ce, “Kafin ruku’u ne.” Sai ya ce: “Lallai wane yana riyawa ka ce: “Bayan ruku’u ne.” Sai ya ce: “karya ya yi.” Sa’an nan ya bayar da labari daga Annabi (SAW) cewa: Lallai shi ya yi kunuti kamar wata daya bayan ruku’u yana addu’a a kan kabilun Bani Sulaim.” Ya ce, “Kuma ya taba aikawa da wadansu mutum arba’in ko ya ce, saba’in, makaranta Alkur’ani zuwa ga wadansu mutane daga mushirikai. Daga baya suka juya baya suka kashe su, saboda tsakaninsu da shi (Annabi SAW) akwai sulhu. Kuma ban taba ganin abin da ya bata wa Annabi (AS) rai ba kamar mutuwar wadannan mutane ba.”
Babi na Ashirin da Tara:
Karbar amanar da mata suka dauka da karbar makwabtakarsu:
115. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abu Nadar bawan Umar dan Ubaidullahi cewa: “Lallai Abu Murrat bawan Ummi Hani ’yar Abu Dalib ya ba shi labari cewa: Lallai shi ya ji Ummu Hani ’yar Abu Dalib tana cewa: “Na tafi zuwa ga Manzon Allah (SAW) a ranar cin Makka na same shi yana wanka Fadima ’yarsa tana masa shamaki, sai na yi masa sallama ya ce: “Wace ce? Na ce, “Ummu Hani ce ’yar Abu Dalib.” Sai ya ce: “Maraba da Ummu Hani.” Lokacin da ya kare daga wankansa sai ya mike ya yi Sallah raka’a takwas yana lullube da wani mayafi.” Sai na ce, “Ya Manzon Allah! Dan uwana ya riya cewa zai kashe wani mutumin da na karbi makwabtakarsa (tsare shi). Wane dan Hubair. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Hakika mun karba miki makwabtakar wanda kika yi makwabtakarsa ya Ummi Hani. Ta ce: “Wannan lokaci ne da hantsi.”
Babi na Talatin:
Amanar Musulmi da makwabtakarsu duk daya ce, waninsu zai iya dauke musu:
116. An karbo daga Muhammad ya ce: “Waki’u ya ba mu labari daga Ama’ashi daga Ibrahim Tamimi daga babansa ya ce: “Aliyu ya taba yin mana huduba sai ya ce: “Ba mu da wani littafi tare da mu wanda muke karanta shi face abin da ke cikin wannan takarda. Sai ya ce: “Abin da ke cikinsa hukuncin raunuka da bayanin haramcin diyyar tozon taguwa. Kuma Madina harami ce tun daga Airu zuwa wuri kaza. Wanda ya farar (kaga bidi’a) abin farawa cikinta, ko ya taimaka wa mai fara (kaga) bidi’a cikinta, to la’anar Allah da mala’iku da mutane gaba daya tana kansa. Ba a karbar (amsar) dukan aiki ko adalci (daga gare shi). Haka wanda ya shugabanci abin da ba a nada shi ba yana da misalin haka. Kuma amanar Musulmi duka daya ce, duk wanda ya saba wa Musulmi shi ma yana da misalin haka.”
Babi na Talatin da Daya:
Idan masu karbar Musulunci suka ce, “Mun juyo, saboda ba su iya fadar cewa: Mun musulunta ba.” Dan Umar ya ce: “Saboda wannan Khalid ya rika yakar wadansu mutane. Sai Annabi (SAW) ya ce: “Ya Allah! Ba hannuna cikin abin da Khalid ya aikata.” Umar ya ce: “Idan ya ce: Matarsu (wato kada ka ji tsoro) to lallai ya nuna amintar da shi. Kuma lallai Allah Ya san harsuna dukansu.” Umar ya taba cewa ga (Hurmuzi mutum Farisa): Yi magana da harshenka babu wani laifi.” (Saboda tabbatar da tsaro ta hanyar sulhu).