BUHARI DA MUSLIM
Babi na Arba’in da Daya: Jefa gawakin mushirikai a cikin rijiya. Kuma ba a karbar kudinsu idan iyalansu suna son daukar gawar iyayensu: An karbo daga Abdan dan Usman ya ce: “Babana ya ba ni labari daga Shu’abah daga Abu Is’hak daga Amru dan Maimun daga Abdullahi(Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Wata rana […]
Babi na Arba’in da Daya:
Jefa gawakin mushirikai a cikin rijiya. Kuma ba a karbar kudinsu idan iyalansu suna son daukar gawar iyayensu:
- An karbo daga Abdan dan Usman ya ce: “Babana ya ba ni labari daga Shu’abah daga Abu Is’hak daga Amru dan Maimun daga Abdullahi(Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Wata rana Annabi (SAW) yana cikin sujuda a gefensa da wadansu mutane daga mushirikan Kuraishawa sai Ukbat dan Abu Mu’aizin ya zo da kayan cikin wata taguwa da mahaifarta ya jefa su bisa bayan Annabi (SAW), bai iya dagowa ba, har sai da Fadima (AS) ta zo ta ture shi daga bayansa ta rika addu’a a kan wadannan mutane. Sai Annabi (SAW) ya ce: “Ya Allah! Na bar Ka da (Ka hallaka) manyan Kuraishawa. Ya Allah! Na bar Ka da Abu Jahli dan Hisham da Utbatu dan Rabi’atu da Shaibatu dan Rabi’atu da Ukbatu dan Abu Mu’aiz da Umayyatu dan Khalf, ko ya ce da Ubayyu dan Khalf. Kuma (Abdullahi) ya ce: “Hakika na gan su cikin wadanda aka kashe a Ranar Yakin Badar. Sai aka jefa su cikin rijiya sai dai ban da Umayyatu ko Ubayyu, saboda su kattan mutane ne da aka ja su sai jikinsu ya rika tsinkewa kafin a jefa cikin raijiya.”
Babi na Arba’in da Biyu:
Laifin mai yaudara ga mai da’a da fajiri:
- An karbo daga Abul Walid ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Sulaiman A’amashi daga Abu Wa’il daga Abdullahi daga Sabit daga Anas daga Annabi (SAW) ya ce: “Lallai akwai wata tuta ga dukkan mayaudari wadda ake gane shi da ita Ranar Kiyama. Wani ya ce: “Wadda za a kafa masa, wani kuma ya ce: Wadda za a nuna gare shi don a fahimce shi.”
- An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Hammad dan Zaid ya ba mu labari daga Ayyub daga Nafi’u daga Dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Na ji Annabi (SAW) yana cewa: “Ga kowane mayaudari za a kafa masa wata tuta Ranar Kiyama saboda yaudararsa.”
- An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Jarir ya ba mu labari daga Mansur daga Mujahid daga Dawus daga Dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “A ranar da aka ci Makka da yakin Musulunci. Babu wata hijira face jihadi da kyan niyya, amma idan an nemi ku fita zuwa ga yaki. To, lallai ku fita zuwa ga yakin. Kuma ya ce a ranar cin Makka: Lallai wannan gari Allah ne Ya haramta shi tun ranar halittar sammai da kasa, yana bisa haramcin, kuma a bisa haramcin Allah zuwa Ranar Kiyama. Kuma bai hallata a yi yaki a cikinsa ba gabanina, kuma ni ma an hallata mini ne na dan wani lokaci a yinin yau. Saboda haka tana nan bisa haramcinta zuwa Ranar Kiyama. Ba a cire kayarta, ba a korar farautanta, ba a daukar tsintuwarta face ga mai sanarwa. Kuma cire makiyayanta. Sai Abbas ya ce: “Ya Manzon Allah! Sai dai ban da ciyawar tsaure! Saboda makeransu kuma da rufin dakunansu, sai ya ce: “To, ban da ciyawar tsaure.”