Buhari da Muslim
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai Littafin bayanin yadda aka fara halittar mutum Babi na farko: Abin da ya zo cikin fadar Allah Madaukaki cewa: “Shi ne Wanda Ya fara halitta, sa’an nan Ya mayar da ita kuma haka Shi Ya fi masa sauki…” (K:30:27): 132. An […]
Tare da Sheikh Yunus Is’hak
Almashgool, Bauchi
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai
Littafin bayanin yadda aka fara halittar mutum
Babi na farko:
Abin da ya zo cikin fadar Allah Madaukaki cewa: “Shi ne Wanda Ya fara halitta, sa’an nan Ya mayar da ita kuma haka Shi Ya fi masa sauki…” (K:30:27):
132. An karbo daga Muhammad dan Kasir ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Jami’u dan Shaddad daga Safawan dan Muhriz daga Imran dan Husain (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Wasu jama’a daga kabilar Tamin sun zo ga Annabi (SAW), sai ya ce: “Ya Bani Tamim ku yi farin ciki da wannan albishir! Sai suka ce: “Mun yi farin ciki, sai ka ba mu wani abu.” Sai fuskarsa (ransa) ya baci, ana nan haka sai mutanen Yamen suka zo ya ce: “Mutanen Yamen ku karba mini wannan bushara, idan Banu Tamim sun ki karba mini.” Sai suka ce, “Mun karba maka.” sai Annabi (SAW) ya rika bayar da labari game da yadda aka fara halitta da Al’arshi. Sai wani mutum ya zo ya ce: Ya Imrana! Taguwarka ga ta can ta gudu, na ce kaicona! Kamar kada in tashi.”
133. An karbo daga Umar dan Hafsu dan Ghiyas ya ce: “A’amashi ya ba mu labari Jami’u dan Shaddad ya ba mu labari daga Safawan dan Muhriz cewa: Lallai shi ya ba shi labari daga Imran dan Husain (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Wata rana na shiga ga Annabi (SAW) na daure taguwata. Sai wadansu mutane daga kabilar Tamim suka zo, ya ce: “Ku karba mini wata bushara ya Bani Tamim! Sai suka ce: “Hakika ka riga ka ba mu bushara, yanzu dai ka ba mu wani abu (na dukiya) sau biyu.” Sa’an nan wadansu jama’a daga mutanen Yamen suka shigo gare shi, sai ya ce: “Ku karba mini wannan bushara mutanen Yamen, idan Bani Tamim sun ki karba.” Suka ce: “Mun karba maka ya Manzon Allah! Suka ce, “Mun zo domin mu tambaye ka game da wannan al’amari.” Sai ya ce: “Allah Ya kasance lokacin da babu abin da ya kasance, Al’arshinSa na bisa ruwa. Ya rubuta dukkan komai cikin Littafi. Ya halitta sama da kasa.” Ana cikin haka sai ya yi shelar cewa: Taguwarka ta kwance ta gudu ya Imran dan Husain, sai na tafi ban ga taguwar ba saboda kawalweniyar hanya (kyallin haske mai dauke ido). Ina rantsuwa da Allah na yi gurin da in kyale ta (taguwar) saboda labarin da (Annabi SAW yake gabatarwa). Darik dan Shihab ya ce: “Na ji Umar (Allah Ya yarda shi) yana cewa: “Wata rana Annabi (SAW) ya mike cikinmu a wani matsayi ya rika ba mu labari game da farkon halitta har shigar ’yan Aljanna masaukansu da shigar ’yan wuta masaukansu. Wanda ya haddace ya haddace, wanda ya manta kuma ya manta.”
134. An karbo daga Abdullahi dan Abu Shaibah ya ce: “Daga Abu Ahmad ya karbo daga Sufiyan daga Abu Zinad daga A’araji daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Allah Madaukaki Ya ce: “Dan Adam yana zagiNa kuma bai dace ba ya rika zagiNa. Kuma yana karyata Ni kuma bai dace ba ya rika karyata Ni. Amma zaginsa gare Ni, shi ne fadarsa cewa: Ina da da. Amma karyarsa gare Ni shi ne da yake cewa: Allah ba zai komo da ni ba kamar yadda Ya kaga halittata!”
135. An karbo daga Kutaiba dan Sa’id ya ce: “Mughira dan Abdurrahman Alkurashi ya ba mu labari daga Abu Zinad daga A’araji daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lokacin da Allah Ya kare halitta, sai Ya rubuta a cikin LittafinSa da ke wurinSa bisa Al’arshinSa cewa: “Lallai rahamaTa ta rinjayi fushiNa.”