Buhari Da Muslim
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi BABI NA UKU:- Yanda aka halitta taurari Kattada ya ce: Bisa faDar Allah MaDaukaki cewa: “Hakika Mun kawata saman duniya da taurari…(67:5).” Kuma dalilan halittar taurari ya kasu kashi uku: Na farko saboda kawata sama, na biyu saboda jifar sheDanun Aljnnu, na uku saboda shiryadda mutane da su. Wanda […]
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi
BABI NA UKU:-
Yanda aka halitta taurari Kattada ya ce: Bisa faDar Allah MaDaukaki cewa: “Hakika Mun kawata saman duniya da taurari…(67:5).” Kuma dalilan halittar taurari ya kasu kashi uku: Na farko saboda kawata sama, na biyu saboda jifar sheDanun Aljnnu, na uku saboda shiryadda mutane da su. Wanda ya yi fassara fiye da haka to lallai ya yi kuskure ya tozarta rabonshi, kuma ya Dora wa kanshi Abin da bai sani ba.” Saboda haka harba mutum zuwa taurari vata dukiya ne da karfi.
BABI NA HUDU:-
Siffar Rana da Wata bisa lissafi. Mujahid ya ce: Suna juyawa kamar mulmulin dunkuli. Wasu sun ce: “Suna kewaya bisa lissafi da masaukai wani bai ketaran wani. Kuma ana kiran jama’a da suna Husban: Kamar yadda ake faDar shihab da shuhban….har zuwa karshe duba littafin Tafsiri.
140. An karvo daga Muhammad DanYusuf ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga A’mash daga Ibrahim Ataimi daga babansa daga Abu Dharri (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce wa Abu Darri lokacin da rana ta vuya: Shin ko kasan inda wan nan rana take zuwa? Na ce, “Allah da ManzonSa suka fi sani ya ce: “Lallai ita tana tafiya ne zuwa karkashin Al’arshi tayi sujuda, sai ta nemi izini sai ayi mata izinin. Kuma ya yi kusa in tayi suujuda ba za’a karvan mata ba. Kuma za ta nemi izinin, ba za’a yi mata izininba. Sai a ce mata: Ki koma in da kika fito, sai ta rika vulla in da take vuya. To wan nan shine fassarar faDar Allah MaDaukaki cewa: “Rana tana gudana ce ga matabbacinta wan nan shine kaddarawa Mabuwayi Masani. (36:38).”
Sa’an nan ya yi sallama alhali rana ta yi haske. Ya yi wa mutane huduba ya ce: “Game da khusufin rana da wata cewa: Lallai su ayoyi ne biyu daga ayoyin Allah, ba su rashin haske saboda mutuwar wani ko don haihuwarshi, amma idan kungansu haka ku gaugawa zuwa ga yin sallah.”
141. An karvo daga Musaddad ya ce: “Abdul Aziz DanMukhtar ya ba mu labari ya ce, Abdullahi Danaji ya ba mu labari ya ce, “Abu Salmat DanAbdirrahman ya ba ni labari daga Abuhuraira (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce: “Rana da Wata za’a tara su ranan kiyama.”
142. An karvo daga Yahaya DanSulaiman ya ce: “DanWahab ya ba mu labari ya ce, Amru ya ba ni labari cewa: Lallai Abdurrahman DanAlkasim ya ba shi labari daga Abdullahi DanUmar (Allah Ya yarda da su),, cewa: Lallai shi ya kasance yana bayar da labari daga Annabi (SAW) ya ce: “Lallai Rana da Wata basu rashin haske saboda mutuwar wani ko saboda haihuwarshi. Amma su ayoyine (halitta) daga ayar Allah, idan kunga sun yi rashin haske to kuyi sallah.”