Buhari da Muslim
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi 148. An karbo daga Hudubat DanKhalid ya ce: “Hammam ya ba mu labari daga Kattada ya ce, Khalifa ya faDa mini, ya ce Yazid DanZurai’u ya ba mu labari ya ce, Sa’id da Hisham sun ba mu labari sun ce: Kattada ya ba mu labari ya ce, Anas […]
Tare da Sheikh Yunus Is’hak
Almashgool, Bauchi
148. An karbo daga Hudubat DanKhalid ya ce: “Hammam ya ba mu labari daga Kattada ya ce, Khalifa ya faDa mini, ya ce Yazid DanZurai’u ya ba mu labari ya ce, Sa’id da Hisham sun ba mu labari sun ce: Kattada ya ba mu labari ya ce, Anas DanMalik (Allah Ya yarda da shi), daga Malik DanSa’asa’ah (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce, “Wata rana ina ga Dakin tsakanin mai barci da wanda ke farke sai ya mabaci wani mutum a tsakanin mutum biyu. Sai aka zo mini da wata tasa na zinari cike da hikima da imani. Sai aka tsaga kirjina zuwa tsakar ciki. Sa’an nan aka wanke da ruwan Zamzam, sa’an nan aka cika da hikima da imani. Aka zo mini da wata dabba fara ba takai alfadari ba kuma tafi jaki. Sai na tafi tare da Jibril, lokacin da na (muka) isa sama ta Daya, sai Jibrilu ya ce wa mai tsaron sama buDe: Sai ya ce, “Wanene? Aka ce, “Jibrilu ne, aka wake tare da kai? Aka ce, “Muhammad ne, aka ce, “Shin har an aika gare shi? Ya ce, “Na’am,” sai aka maraba da shi, kuma madalla da Abin zuwan da yazo. Sai na tafi zuwa ga Adam na yi mashi sallama, sai ya ce: “Maraba da kai, Da Annabi,” sai muka tafi zuwa sama ta biyu, aka ce, “Wanene? Ya ce, “Jibrilu ne, aka ce: Wake tare da kai? Ya ce, “Muhammad AS ne, aka ce, “Shin an aika gare shi? Ya ce, “Na’am, sai aka ce: Maraba da shi, madalla da Abin zuwa da yazo. Sai na tafi ga Isah da Yahya suka ce: “Maraba da kai, Danuwa Annabi.” Sai muka tafi zuwa ga sama ta uku: Aka ce, “Wanene? Aka ce, “Jibrilu ne, aka ce: “Wake tare da kai? Ya ce, “Muhammad ne,” ya ce: “Shin an aika gare shi? Ya ce, “Na’am, sai aka ce: “Maraba da shi, kuma madalla da Abin zuwa da yazo. Sai na tafi zuwa ga Yusuf na yi mashi sallama sai ya ce: “Maraba dakai Danuwa Annabi.” Sai muka tafi sama ta huDu, aka ce: “Wanene? Ya ce: “Jibrilu ne, aka ce: “Wake tare da kai? Ya ce, “Muhammad AS ne, aka ce: “Shin an aika zuwa gare shi? Ya ce, “Na’am, aka ce: “Maraba da shi, madalla da Abin zuwa da yazo. Sai na tafi ga Idris nayi masa sallama ya ce: “Maraba da Danuwa Annabi.” Sai muka tafi sama ta biyar, aka ce: “Wanene? Aka ce, “Jibrilu ne, aka ce: “Wake tare da kai? Aka ce: “Muhammad ne,” aka ce: “Shin an aika zuwa gare shi? Ya ce: “Na’am, aka ce: “Maraba da shi, madalla da Abin zuwa da yazo. Sai muka tafi ga Haruma nayi sallama ya ce: “Maraba da Danuwa Annabi,” sai muka tafi zuwa sama ta shida. Aka ce: “Wanene? Aka ce: “Jibrilu ne, aka ce: “Wake tare da kai? Aka ce: “Muhammad AS ne, aka ce: “Shin an aika zuwa gare shi? Maraba da shi, madalla da Abin zuwa da yazo, sai na tafi zuwa ga Musa nayi mashi sallama. Sai ya ce: “Maraba da kai, Danuwa Annabi.” Lokacin da na shuDe sai ya rika kuka, aka ce, “Me ya sanya ka kuka? Ya ce: “Ya Allah wan nan saurayi wanda aka aiko a bayana, jama’arsa zasu shiga Aljanna fiye da tawa jama’ar.” Sai muka tafi zuwa sama ta bakwai, aka ce: “Wanene? Aka ce: Jibrilu ne, aka ce: “Wake tare da kai? Aka ce: “Muhammad ne, aka ce: “Shin har an aika gare shi? Marabada da shi, madalla da Abin zuwa da yazo. Sai na tafi zuwa ga Ibrahim na yi mashi sallama. Ya ce: “Maraba da kai Da Annabi,” sai aka Daukaka mini Baitul Ma’amur na tambayi Jibrilu ya ce: “Baitul Ma’amur ke nan, kowa ce rana mala’iku dubu saba’in ke sallah, idan sun fita basu komowa karshen aikinda ke kansu kenan. Sai aka nuna mini Sidratul Muntaha (itacen mgaryar tukewa da ke sama ta bakwai). Sai na iske ‘yan ‘yan ta kamar tulunan Hajar, ganyenta kamar kunnuwar giwaye, akarkashinta akwai koramai huDu: koramai biyu boyayyu, da wasu koramai biyu bayyanannu. Sai na tambayi Jibrilu ya ce: “koramai biyun nan na cikin Aljanna ne. Amma biyu da suke bayyane, Nilu da Furat ne. Sa’an nan aka farlanta salloli hamsin. Na juyo har sai da nazo ga Musa AS ya ce: “Me ka karba? Na ce, “An farlanta mini salloli hamsin.” Ya ce, “Ni nafi ka sanin mutane, na zauna da Bani Isra’il na samu wahala mai tsanani saboda su. Kuma lallai al’ummarka ba zasu iya aikata haka ba. Ka koma zuwa ga Babangijinka ka roke shi sauki. Sai na koma na roke shi, ya mayarda ita arba’in. Sa’an nan na koma (ga Musa ya faDa mini kamar haka) na koma aka rage ta zamo talatin. Sa’an nan na koma kamar haka aka rage ta zamo Ashirin. Sa’an nan na koma kamar haka aka rage ta zamo goma. Na koma ga Musa ya faDa mini kamar haka, sai aka sanya ta zamo biyar. Na tafi ga Musa ya ce: “Nawa aka rage? Na ce, “An sanya ta ta zamo biyar,” ya sake faDa mini kamar haka, sai na ce: “Na mika wuya ta ga Allah bisa ga wan nan, daga nan sai aka kira Annabi (SAW) da cewa: “Na riga na zartarda Abin da na farlanta shi kuma na saukaka ga bayina. Kuma zan saka ga kowa ce Daya mai kyau da lada goma.”