BUHARI DA MUSLIM
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi Da Sunan Allah Mai rahama Mai jinkai. Littafin bayanin hadisan da suka ambaci annabawa. Babi na Farko: Bayani game da halittar Adam da zuriyarsa. Fassarar kalmomin ayoyin Alkur’ani mun kyale su saboda takaitawa ka duba littafin tafsiri: An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Abdurrazak ya ba […]
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi
Da Sunan Allah Mai rahama Mai jinkai.
Littafin bayanin hadisan da suka ambaci annabawa.
Babi na Farko: Bayani game da halittar Adam da zuriyarsa. Fassarar kalmomin ayoyin Alkur’ani mun kyale su saboda takaitawa ka duba littafin tafsiri:
- An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Abdurrazak ya ba mu labari daga Ma’amar daga Hammam daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce: “Allah Ya halicci Adam da tsawonsa kamar zira’i (kamu) sittin. Lokacin da Ya halicce shi sai Ya ce, “Ka tafi zuwa ga wadannan mala’iku ka yi musu sallama, ka saurari abin da za su amsa maka da shi, shi ne gaisuwarka kai da zuriyarka.” Sai ya ce: Assalamu alaikum, sai suka ce: “Assalamu alaika wa wahmatullahi, suka kara masa da kalmar wa rahmatullahi. Duk wanda zai shiga Aljanna zai shiga bisa surar Adam, kuma halittu suna raguwa ne daga yadda yake har zuwa yanzu.”
- An karbo daga Kutaiba dan Sa’id ya ce: “Jarir ya ba mu labari daga Umaratu daga Abu Zur’atu daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai farkon jama’ar da za su fara shiga Aljanna suransu kamar wata daren goma sha hudu. Sa’an nan wadanda suke biye musu na da haske fiye da misalin taurari masu haske cikin sama. Kuma su (gaba dayansu) ba su yin fitsari kuma ba su yin kashi kuma ba su zubar da majina. Abin tace gashin kansu na zinari ne kuma zufar jikinsu na kanshin miski. Itacen hura wutarsu na itacen Uluwatu mai kanshi. Matansu na Aljanna suna da kamar halitta mutum daya bisa surar halittar babansu Adam da tsawon kamu sittin.”
- An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya ya ba mu labari daga Hisham dan Urwat daga babansa da Zainab ’yar Abu Salmata daga Ummi Salmata cewa: Ummi Sulaimin ta ce: ‘Ya Manzon Allah! Lallai Allah ba Ya jin kunyar gaskiya shin mace tana wanka idan ta yi mafarkin da namiji? Ya ce: “Na’am, idan ta ga ruwa,” sai Umma Salmata ta yi dariya ta ce: Shin mace tana mafarki? Manzon Allah (SAW) ya ce: “Saboda me, da ke kama da uwatasa?”
- An karbo daga Muhammad dan Salam ya ce: “Alfazariyyu ya ba mu labari daga Humaid daga Anas (Allah Ya yarda da shi),, ya ce: “Labarin isowar Annabi (SAW) Madina ya isa ga Abdullahi dan Salam don ya je gare shi ya ce: “Lallai ni zan tambaye ka game da wasu abubuwa uku wadanda babu wanda ya sansu face Annabin Allah. Sai ya ce, “Mene ne alamar Sa’ar Kiyama? Kuma mene ne farkon abincin ’yan Aljanna? Kuma daga ina da ke kama da babansa ko ya yi kama da kawunansa?” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Jibrilu ya ba ni labari game da su dazu.” Sai Abdullahi ya ce: “Wannan Mala’ika shi ne makiyin Yahudawa,” sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Amma farkon alamar Tashin Kiyama, ita ce wata wuta da za ta huro tana tarawar mutane daga gabas zuwa yamma. Kuma abincin da ’yan Aljanna za su fara ci hantar kifi. Amma kamannin da da babansa ko kawunansa, saboda idan mutum ya fada wa mace yana saduwa da ita, sai ruwan maniyyinsa ya riga nata shiga cikin mahaifa, to sai ya yi kama da shi. Amma idan ruwan maniyyinta ya riga nasa, to sai ya yi kama da ita.” Sai (Abdullahi) ya ce: “Lallai ni na shaida kai Manzon Allah ne? Sa’an nan ya ce: “Ya Manzon Allah! Lallai Yahudawa makaryata ne, idan suka san musulunta ta kafin ka tambaye su za su karyata ni a wurinka.” Ana nan haka Yahudawa suka zo Abdullahi ya zo ya shiga dakin. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce musu, wane matsayi Abdullahi ke da shi cikinku? Su ka ce, “Babban malaminmu ne, wanda ya fi mu sani kuma dan malaminmu. Kuma zababbe ne cikinmu dan zababbenmu.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Shin kun ganin (ku ba ni labari) in an ce muku Abdullahi ya musulunta? Sai suka ce, “Allah Ya tsare shi daga haka, sai Abdullahi ya fito gare su ya ce: “Na shaida lallai babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma lallai Muhammad Manzon Allah.” Sai suka ce: “Sharrinmu ke nan dan sharrinmu, sai suka fada kansa da bakar magana.”