Buhari da Muslim
448. An karbo daga Muhammad dan Yusuf ya ce: “Auza’iy ya ba mu labari daga Zuhuri daga Sa’id dan Musayyab daga Urwatu dan Zubair cewa: “Lallai Hakim dan Hizam ya ce: “Na taba rokon Manzon Allah (SAW) ya ba ni. Sa’an nan na sake rokonsa ya ba ni. Sa’an nan ya ce, mini: Ya Hakim […]
448. An karbo daga Muhammad dan Yusuf ya ce: “Auza’iy ya ba mu labari daga Zuhuri daga Sa’id dan Musayyab daga Urwatu dan Zubair cewa: “Lallai Hakim dan Hizam ya ce: “Na taba rokon Manzon Allah (SAW) ya ba ni. Sa’an nan na sake rokonsa ya ba ni. Sa’an nan ya ce, mini: Ya Hakim lallai wannan dukiya kamar ’ya’yan itace ne masu zaki. Wanda ya karbe ta saboda wadatar rai (ga lalura) sai a sanya masa albarka a cikinta. Amma wanda yake karbe ta domin tarawa da daukaka rai ba a sanya masa albarka. Sai ya kasance kamar mutumin da yake cin abinci bai koshi. Kuma hannu madaukaki (mai bayarwa) ya fi alheri daga hannu makaskanci (mai karba).” Wato hannun bayarwa ya fi hannun karba. Hakim ya ce: “Na ce, “Ya Manzon Allah! Ina rantsuwa da Wanda Ya aiko ka da gaskiya ba na kara rokon wani bayanka bisa ga komai har in bar duniya.” Har Abubakar ya kasance yana kiran Hakim domin ya ba shi wata kyauta, sai ya ki karbar komai daga gare shi. Sa’an nan Umar ya kira shi domin ya ba shi kyautarsa ya ki karbarta. Sai (Umar) ya ce: “Ya ku jama’ar Musulmi! Ku shaida na ba shi hakkinsa wanda Allah Ya raba da shi daga wannan ganima amma ya ki karba. Hakim bai taba rokon wani ba daga cikin mutane bayan Annabi (SAW) har ya rasu Allah Ya ji kansa.”
449. An karbo daga Bishiru dan Muhammad Assikhtiyani ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Yunus ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce: Salim ya ba ni labari daga Dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Dukanku masu kiwo ne, kuma za a tambaye ku game da abin kiwonku. Shugaba mai kiwo ne kuma za a tambaye shi abin kiwonsa. Mutum mai kiwo ne cikin iyalansa kuma za a tambaye shi abin kiwonsa. Mace mai kiwo ne cikin dakin mijinta kuma za a tambaye ta game da abin kiwonta. Mai aikin gida mai kiwo ne cikin dukiyar shugabansa kuma za a tambaye shi game da abin kiwonsa.” Ya ce, “Ina tsammanin ya ce, “Mutum mai kiwo ne cikin dukiyar babansa.”
Babi na Goma:
Idan mutum ya bayar da sadakar wakafi ko ya yi wasiyya ga makusantansa, kuma ko su wane ne makusanta? Sabit ya ce, daga Anas cewa: Annabi (SAW) ya ce da Abu Dalhat cewa: Ka sanya sadakarka ga makusantarka, sai ya raba ta ga Hasan da Ubayyu dan Ka’ab.” Al-Ansari ya ce: “Babana ya ba ni labari daga Sumamah daga Anas misalin Hadisin Sabit ya ce: “Ka sanya ta ga makusantanka, sai ya raba ta ga Hasan da Ubayyu dan Ka’ab, domin sun kasance sun fi ni kusanci a gare shi. Saboda kusancin Hasan da Ubayyu dan Ka’ab ga Abu Dalha kusanci managarci ne domin shi (Abu Dalha) sunansa: Zaid dan Sahlu dan Aswad dan Hiram dan Amru dan Zaid Manat dan Addiyu dan Amru dan Malik dan Annajar. Da Hassan dan Sabit dan Munzir dan Hiram shi ne uba na uku. Haram dan Amru dan Zaid Manat dan Addiyu dan Amru dan Maik dan Annajar, don haka shi yake haduwa da Hasan da Abu Dalha. Ubayyu kuma da wajen uba na shida har zuwa Amru dan Malik shi ne Ka’ab dan Kais dan Ubaidullah dan Zaid dan Mu’awiyya dan Amru dan Malik danNajjar. Amru dan Malik ya hadu da Hassan da Abu Dalha da Ubayyi.” Wadansu jama’a sun ce: “Idan mutum ya yi wasiyya ga makusantansa to rabon yana ga iyayensa na cikin Musulunci.”
450. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Is’hak dan Abdullahi cewa: Lallai shi ya ji Anas (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce da Abu Dalha: “Ina ganin ya kamata ka sanya (raba gonar) a cikin makusantanka (danginka). Sai Abu Dalha ya ce: “Zan aikata haka ya Manzon Allah! Sai Abu Dalha ya raba ta cikin danginsa kabilar (’ya’yan) baffaninsa.” DanAbbas ya ce: “Lokacin da ayar nan ta sauka cewa: “Ka yi wa danginka makusanta gargadi….” (K:26:214). Sai (Annabi SAW) ya rika kira da cewa: “Ya Bani Fihri, ya Bani Addiyyi ga kabilun Kuraishawa.” Abu Huraira (RA) ya ce: “Lokacin da wannan ayar ta sauka cewa: “Ka yi wa danginka makusanta gargadi….” (K:26:214). Annabi (SAW) ya ce: “Ya ku jama’ar Kuraishawa!”