Buhari da Muslim
Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi 281. An karbo daga Muhammad ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari daga Ma’amar daga Zuhuri ya ce, Salim dan Abdullahi ya ba ni labari daga babansa cewa: Lallai Annabi (SAW) lokacin da ya wue ta Hijri na (Samudawa) sai ya ce: “Kada ku shiga masaukan wadanda suka […]
Tare da Sheikh Yunus Is’hak
Almashgool, Bauchi
281. An karbo daga Muhammad ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari daga Ma’amar daga Zuhuri ya ce, Salim dan Abdullahi ya ba ni labari daga babansa cewa: Lallai Annabi (SAW) lokacin da ya wue ta Hijri na (Samudawa) sai ya ce: “Kada ku shiga masaukan wadanda suka yi zalunci face sai in kun kasance masu kuka saboda tsoron kada abin ya same su ya same ku. Daga nan sai aka ga (Annabi SAW) ya rufe fuskarsa da tufafinsa alhali yana kan abin hawarsa (taguwarsa).”
282. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Wahab ya ba mu labari ya ce, babana ya ba mu labari ya ce na ji Yunus ya karba daga Zuhuri daga Salim cewa: Lallai Dan Umar ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: Kada ku shiga masaukan wadanda suka zalunci rayukansu face kun kasance masu kuka saboda tsoron kada abin da ya same su ya same ku.”
Babi na Takwas:
Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Suna tambayarka game da Zul-Karnaini….har zuwa karshen fadarsa ..Sababa.” (K:18:83-84). Fassarar kalmomi saboda takaitawa mun kyale su a duba littafi na bakwai a tafsiri.
283. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ukail daga Dan Shihab daga Urwatu dan Zubair cewa: Lallai Zainab ’yar Abu Salmatu ta ba shi labari daga Ummi Habiba ’yar Abu Sufiyan daga Zainab ’yar Jahshi (Allah Ya yarda da su), cewa: Lallai Annabi (SAW) ya taba shiga gare ta a firgice yana cewa: “Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, tsananin azaba ya tabbata ga Larabawa saboda wani sharrin da hakika ya kusanto. Yau an huda katangar Yajuja wa Majuja da kamar haka. Sai ya kulla babbar yatsarsa da wadda take biye mata (wato kamar haka).” Sai Zainab ’yar Jahshu ta ce: “Ya Manzon Allah! Yanzu za mu hallaka alhali cikinmu akwai salihai? Ya ce: “Na’am, idan masu zunubi suka yawaita.”
284. An karbo daga Muslim dan Ibrahim ya ce: “Wuhaib ya ba mu labari ya ce, Dan Dawisu ya ba mu labari daga babansa daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Allah Ya bude daga katangar Yajuj wa Majuja da misalin kamar haka, sai ya kulla yatsunsa da nunin casa’in (kamar yadda ya gabata).”
285. An karbo daga Is’hak dan Nasru ya ce: “Abu Usamatu ya ba mu labari daga A’amashi ya ce, Abu Salih daga Abu Sa’idil Khudiri (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Allah zai ce: Ya Adam! Ya ce, “Na amsa maKa arzikin duniya da Lahira gare Ka Yake, dukkan alheri na hannunKa. Sai ya ce: Ka fitar da rabon wuta, sai ya ce: Su wane ne rabon wuta? Ya ce: “Cikin dubu kafitar da dari tara da casa’in da tara, wannan lokaci ne yaro ke furfura (farin gashi). Duk mai ciki take haihuwar abin cikinta. Za ka mutane suna maye amma ba mayen giya suka sha ba, amma dai azabar Allah ce mai tsanani.” Sai (sahabbai) suka ce, “Ya Manzon Allah! Wane mutum daga cikinmu? Sai ya ce: “Ku yi farin ciki! Lallai daga cikinku mutumin yake, dubun kuma daga Yajuj wa Majuj. Sannan ya ce: Ina rantsuwa da Wanda raina ke hannunSa ina kaunar ku kasance daya cikin hudu na mutanen Aljanna. Sai muka yi kabbara. Ya ce: Ina kaunar ku kasance daya cikin uku na yawan mutanen Aljanna. Sai muka yi kabbara. Ya ce: Ina kaunar ku kasance rabin mutanen Aljanna, sai muka yi kabbara. Sai ya ce: Ba za ku kasance ba cikin al’ummar duniya face kamar (su) bakin gashi ne a cikin jikin farin bijimi (sa). Ko ya ce, kamar farin gashi a cikin jikin bakin bijimi”.