Buhari da Muslim

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi Babi na Goma Sha Shida: Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Shin kun kasance halarce ne lokacin da mutuwa ta riski Yakub…” (K:2:133). 314. An karbo daga Is’hak dan Mansur ya ce: “Abdussamad ya ba mu labari ya ce, Abdurrahman dan Abdullahi ya ba mu labari daga babansa daga […]

Buhari da Muslim
Buhari da Muslim

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Goma Sha Shida:

Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Shin kun kasance halarce ne lokacin da mutuwa ta riski Yakub…” (K:2:133).

314. An karbo daga Is’hak dan Mansur ya ce: “Abdussamad ya ba mu labari ya ce, Abdurrahman dan Abdullahi ya ba mu labari daga babansa daga Dan Umar (Allah Ya yarda da su), daga Annabi (SAW) ya ce: “Mai karimci dan mai karimci Yusuf dan Yakub dan Is’hak dan Ibrahim (AS).”

Babi na Goma Sha Bakwai:

Bisa fadar Allah cewa: “Hakika ya kasance cikin (labarin) Yusuf da ’yan uwansa akwai ayoyi ga masu tambaya…” (K:12:7).

315. An karbo daga Ubaid dan Isma’il ya ce: “Abu Usamat ya ba mu labari daga Ubaidullah ya ce: “Sa’id dan Abu Sa’id ya ba ni labari daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa: An taba tambayar Manzon Allah (SAW) cewa: Wa ya fi mutane karimci? Ya ce, “Wanda ya fi mutane karimci wanda ya fi su tsoron Allah. Su ka ce, “Ba wannan muke tambayarka ba.” Ya ce: “Wanda ya fi mutane karimci shi ne Yusuf Annabin Allah dan Annabin Allah dan Annabin Allah dan Annabin Allah dan Masoyin Allah.” suka ce, “Ba wannan muke tambayarka ba.” Ya ce: “Cikin mu nan (asalin) Larabawa kuke tambayata? Suka ce, “Na’am,” ya ce: “Mutane suna da asali daban-daban, amma zababbunsu a Jahiliyya suna zababbunsu a Musulunci idan suka yi ilimi.”

316. An karbo daga Badalu dan Muhabbar ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Sa’ad dan Ibrahim ya ce, “Na ji Urwatu dan Zubair daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: Lallai Annabi (SAW) ya ce mata: Ki fada wa Abubakar ya yi wa mutane Sallah. Sai ta ce, “Lallai shi mutum ne mai sanyin hali duk lokacin da ya tsaya a matsayinka sai ya yi ta kuka. Ya sake umartarta ta sake fada masa kamar farko har sau uku, a ta hudu sai ya ce: “Lallai ku matan nan ’yan uwan matan zamanin Yusuf ne, ki umurci Abubakar.” Wato halin mata iri daya ne idan ba su so aiwatar da wani abu yadda suka so ba.

317. An karbo daga Rabi’u dan Yahaya ya ce: “Za’idatu ya ba mu labari daga Abdulmalik dan Umair daga Abu Burdatu dan Abu Musa daga Babansa ya ce: “Annabi (SAW) ya taba rashin lafiya sai ya ce: “Ku shaida wa Abubakar ya yi wa mutane Sallah. Sai A’isha (RA) ta ce: “Lallai Abubakar mutum ne mai halin kaza- da kaza. Ya sake fadar maganar farko ta sake fadin kamar ta farko ya ce: “Ku ce wa Abubakar ya yi wa mutane Sallah, lallai ku ’yan uwan matan zamanin Yusuf ne.” Sai Abubakar ya yi wa mutane limanci a rayuwar Annabi (SAW).

318. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari ya ce, Abu Zinad ya ba mu labari daga A’araji daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya Allah! Ka tserar da Ayyash dan Abu Rabi’ah, Ka tserar da Salmatu dan Hisham, Ka tserar da Walid, Ka tserar da mumminai raunana. Allah! Ka sanya musu fari kamar yadda ka sanya wa mutanen Yusuf.”

319. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad dan Asma’u dan dan uwan Juwairiyyat ya ba mu labari ya ce: “Juwairiyyat dan Asma’u ya ba mu labari daga Malik daga Zuhuri cewa: Lallai Sa’id dan Musayyab da Abu Ubaidatu sun ba shi labari daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Allah Ya jikan Ludu, hakika ya kasance yana neman tarowa ga rukuni mai karfi (saboda fada da masu luwadi). Kuma da na zauna cikin kurkuku da kwatankwacin abin da Yusuf ya zauna. Sa’annan a ce mai kira ya zo da na amsa masa.”

 

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano

Ya kamata a kori shugaban INEC —Obasanjo